Ouummey 01 {4/28/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*? _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey Godiya Da sunan Allah me Rahma me jin kai, dukkan Godiya ta tabbata ga Allah SWT Ubangijin talikai, me kowa me komai da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi me suna a sama cikin koshin lafiya, ina addu'ar Allah ya bani ikon gama shi kamar yadda na faro ya sa mu amfana da duk wani darisin cikin sa, kuskuren cikin sa kuma Allah ya yafe min.               *Jan hankali*. This book is a total work of fiction, suna, gari kasa ko wani abu daga cikin labarin in aka yi rashin Sa'a yayi daidai da naki to fa arashi ne, ban rubuta wannan littafi dan cin mutunci ko wulakanta wani ba face dan ganin yada ce in fito da virtues din matan da rashin haihuwa yasa ake yi wa kallon kaskantattu, wulakantattu ko marasa amfani, a guji yanke wani abu ko juya min labarin ta kowace siga dan tabbatar da zaman lafiya, kamar yadda na faɗa wannan labarin ƙirƙirarre ne bisa fasaha da baiwar da Allah ya bani tare da yin duba ga rayuwar mu da abubuwan dake faruwa cikin wasu gidajen auren.                      *Dedication* *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sai dan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ______________________________________ ______________________________________                   _Free Chapter One_ Tun daga kasa har sama nake karewa kaina kallo ta cikin tafkeken madubin da ke girke a dakin baccin nawa, babu ta inda na hango wata makusa ko kasawa a tattare da ni, hakan be wadatar da ni ba sai da na sake ɗagowa na sake sako duban tun daga kan yalwataccen gashin kai na bakikirin dake kwance kan kafadu na, a hankali na sauke duba na kan matashiyar fuska ta dake cike da tashen kuruciya, ba wai na budurtaka ba a'a na shekarun tashe ga iri na da muke kan wannan mataki, zagayayyar fuskar ta ɗauke take da wadatattun idanun da Allah ya ƙawata ta dasu, farare tas masu haske da matukar daukar hankali, ban tsawaita ba na sauko kan dogon karan hanci na da ya dada wa fuskar kyau bayan idon, hanci na ba siriri bane zut ɗin nan yana da dan fadi kadan da yasa ya zauna das kan fuskar, kyakkyawan ƙaramin baki na me ɗauke da madaidaitan lips da basu cika karanta ba haka kuma ba manya bane, a hankali kuma na lumshe idona na buɗe tare da sakin kyakkyawan murmushin da ya bayyana jerarrun haƙora na da basu kasance farare ba sedai milk ne masu kyau da suke samun kula a ko yaushe. Cikin wani irin yanayi na girgiza kai na wani abu na tsirga min cikin raina na sunkuyar dashi kafin cikin karfin halin da na saba yi na bude na cigaba da surveying jikina, a kan cikakken wuya na idanuna suka sauka wanda ke dauke da wasu layi haka ko guru guru zance, cikar kirjina dake fisgar hankali na maida kaina farin ciki na ratsa ni, shafaffen ciki na da bashi da alamar ɗagawa balle in aje tumbin da wasu daga cikin sa'anni na ke korafi dashi suke kuma sha'awar lafewar cikin nawa sai dai gare ni hakan shine ciwo mafi girma ga rayuwa ta dan babban burin na a wannan duniyar be wuce in farka in ga cikina ya tasa kamar kowace mace da Allah ya albarkace ta da arzikin haihuwa ba. Da kyar na haɗiye wani mugun miyau ina janye duba na daga wajen na maida kan faffaɗa kuma cikakken kugu na wanda shine abu mafi daukar hankali a jikina gaba ɗaya, nikaina yana daya daga cikin halitta na da nake alfahari dashi dan shine kadai abu ɗaya da ya rage min da ya riƙe ni a gidan aure na ya kuma sa nake da yar ragowar kima a idanun mijina wato surar da Allah ya min, ban tsawaita ba na karasa kan kafafuna dake wadace da jan lalle wanda bana rabo shi, lallen ya zauna daras kamar a kai a aka ƙirƙire shi, yadda ya haska farar fata ta kuwa abin ba'a ce wa komai. Babbar ajiyar zuciya na sauke dana gama karewa kai na kallo kafin cikin sanyin jiki na dauki kwalbar turaren da tuntuni shi ne zan shafa amma na tsaya kallon kaina kamar bakuwar kan nawa, zazzagwa nayi a hannu na na shiga shafe lallausar fata ta dashi lungu da saƙo sannan na aje, wata na kuma ɗauka itama na murza a hannun na shige shafe wasu wurare masu mahimmanci a jikina, ina yi ina yan tunane tunanen da suka zame min jiki a duk lokuta irin wannan. Ringing din wayata dake aje kan bedside drawer yasa na dawo hankali na sosai na shiga shiri da sauri dan nasan ba kowa ke kiran ba se oga, na dade da sanin ya tsani jira musamman daga gare ni kamar yadda yake faɗa min times without number sai too ifdai nikuma ya riga ya zame min jiki musamman a kwana kin nan. Kayan bacci na ciro masu kyau, laushi hadi da daukar hankali na zura ina tattare gashi na waje ɗaya na kama shi cikin ribbon, duk da na shafa wasu turaren kafin sa kaya ba hakan ya hanani sake fesa wasu ba wanda suka sa take dakin ya cika da sassanyan kanshi na me ratsa zuciya wanda nake amfani dashi kadai lokacin da zan je ga oga. Waya ta na ɗauka na kashe batare da duba komai ba dan bani da lokacin hakan me ni na can na jira na kuma san tuni ya cika yayi fam se nayi rarrashi. Seda na sawa kofa ta key dan gudun matsala da jan magana sannan na wuce upstairs inda nan ne turakar me gidan take, seda nayi Knocking tare da dan dakatawa sannan na tura ƙofar a hankali ina me yin sallama cikin daga murya dan ankarar da na cikin dakin cewa gani nan fa tafe. Nasan zaku yi mamakin wai na tsaya knocking ni da dakin mijina da addini ya bawa damar shiga wajen sa duk sanda naso haka kuma ganin sa cikin kowane yanayi halak ne gare ni, to ba komai yasa nayi hakan ba face gujewa haduwa da ɓacin rai, a irin wannan yanayin na kan ci karo da mabanbanta takaicin da kan hanani bacci wasu lokutan yayinda wasu lokutan kuwa nake hana zuciya ta damuwa ko da kuwa taso yin hakan. Ajiyar zuciya nayi hango shi zaune ken bed Yana danna waya, cikin tafiya ta me daukar hankali da kuma karin wasu salo dan sace zuciyar oga na kai gefen mirror ɗin sa na aje yar jakar kayan hannu na sannan na karasa gare sa wanda tun shigowa ta da yayi min kallo ɗaya be sake yi ba. Cikin jikin sa na shige ina manne masa kamar wata cingum na sanyaya murya dan nasan nayi laifi haka kuma na shagwaɓe fuska cikin fatan samun lagon sa "Am sorry zuma naaa, na tsaya shirya maka kaina ne ta yadda zaka mori daren ka cike da annashuwa da farin ciki, ayi min afuwar dadewar da nayi plsss". Na karasa ina kai hannuna cikin ƙirjin sa ina masa waiwayi cikin salon da nasan baze iya jurewa ba, kamar yadda na sani kuwa lumshe idon sa yayi tare da rike hannun da ke yawo jikin nasa kana ya bude su ya zuba kan fuska ta "Kullum se kince ayi miki hakuri kuma ba haka ze Hana gobe ma ki sake ba, na kasa gane meye matsalar ki Khadijah, ke ba da ba ba jikan da zaki fake da kula da shi ba amma ko mariya dake goyo ba zata faɗa miki kawo uzuri ba, Allah ya sani kin fara kaini bango dan na fara gajiya da uzurorin ki marasa kan gado da bakya rasa na bayar wa kullum". Daga jikin nasa da nake kwance na lumshe ido zuciya ta na motsawa, ba se Salees ya tuna min da cewa ban taɓa haihuwa ba, ba se Salees ya tunatar da ni bani da tsuntsu bani ga tarko ba dan hakan abu ne da bana taɓa mantawa ko da kuwa acikin mafarki ne. Sanin shiru na wata matsalar ze jawo yasa na daure rashin daɗi na na bar shi iya cikin raina yayinda a zahiri na ɗago na sumbaci bakin sa ina tabbatar masa insha Allah ba zan kara ba wanda hakan yayi tasiri gare shi dama kuma be fiya riko ba, cikin zakuwa da natsuwa ya shiga birkita nutsuwa ta da salon sa masu tafiya da ruhi na suke kuma karamin kaunar sa a ko da yaushe inda nima tuni na biye masa muka fada cikin wata duniya me wuyar bayyanuwa, seda duk muka sami nutsuwar da ta dace kafin muka shiga wanka dan yin shirin kwanciya. Ko a cikin toilet din ma be bar ni haka ba dan se da yayi neman maganar sa san rai kafin muka wanko jiki muka fito, cikin sanyin jikin gajiyar da ya tara min na maida kayana tare da hayewa kan gado na lafe ina sauke numfashi yayin da gefe ɗaya nake mamakin rashin faruwar lamarin da ya zame mana jiki cikin watanni ɗaya zuwa biyu da suka wuce. Ban kai ƙarshen mamakin ba sautin kukan yaro ya fara ratsa kunne na, tun ina jiyo wa kasa kasa har ya fara ƙarfi alamun ana nufo dakin ne, cike da takaici na tsurawa kofar dakin ido cikin jiran faruwar sabon mu, dukan kofar aka shiga yi kamar a filin yaki wai kuma hakan da sunan knocking ne fa ake yi, daga kwancen da nake ban motsa ba naga tashin sa daga kokarin kwanciyar da yake yi kusa da ni ya bude dakin yana ɗan haɗe rai. "Ka gan shi nan yaki yin shiru, nayi nayi wallahi se kuka yake har na rasa yadda zan masa, ni yadda yake yi ne ma yafi bani tsoro kalli kaga se wani miƙewa yake kamar ze shide". Ai oga se ya nemi haɗe ran da ya ɗan yi ya rasa ya kai hannu cike da hanzari ya karbi dan ya shiga riritawa, kamar abin shiri yaro maimakon yayi bacci ko yayi shiru ba se ma karawa kukan sa karfi da yayi hakan kuma ya sake dugunzuma hankalin uban duk yabi ya tashi dan Allah ya zuba mishi so da kawa zucin yaya, ko dan ya dade kafin ya same su ne?. Iya shaka na shaka domin dai a yau na gaza yiwa mariya da Salees uzuri, ba dan komai ba sedan saboda ba yau hakan ya fara faruwa ba, abin kamar ya zame mata sabon da take jin dadin sa ni kuma ya zama sabon da ke taɓa zuciya ta da sani cikin ɓacin rai. "Amma dai kasan wannan shiga hakki ne ko, yaya muna kwance kawai zaka bude wa wata daki hakan kuma duk be yi ba se an hana ni bacci, shin shima hutun nawa ya zama abin bakin ciki da hassada ne ko kuwa me?. Wani kallon Salees ya shiga yi min me kama da na mamaki ko kuwa na zallar takaici ne, kafin kuma yayi magana tayi caraf ta riga shi "Kiyi haƙuri Khadijah, Amir ne ban san me ke damun sa ba kwana biyu, ko kuwa har ya gane uban sa ne oho, kinga har mun kwanta amma yaron yace be san zance ba kuka har na rasa yadda zanyi dashi shi yasa na kawo masa ko ze yi shiru dan mama tace yawan barin yaro yana kuka ba lallashi na jawo masa matsalar ƙwaƙwalwa da kuma ciwon zuciya". "Kinga dan Allah dakata ba dake nayi magana ba ki bari shi da nake dashi ya amsa min, zuma naaa da kai fa nake magana". A irin fusacen da Salees ya kalle ni abin seda ya girgiza ni dan kallo ne me shaida Allah ya soki bana kusa da ke "A sani na dai ke ba kurma bace kin ji me tace ko?". A yadda nakai geji nima hakuri na ya kare dan haka na bashi tawa amsar da fusatacciyar murya kamar yadda ya min "Shine nace ina buƙatar sanin me kake nufi da ni ne dan wallahi sedai ko ta fita da yaron daga dakin nan ko ni na fita dan ba za'a dinga hanani bacci ana samun ciwo a banza ba". "Aikuwa sedai ke ki fita dan da dai dakin uban sa ne cikin gidan uban sa, kinga kuwa maganar a fitar dashi ma ai bata taso ba". Kuriii na masa da ido ina kallon sa yadda ya fadi abinda ya faɗa hankali kwance, ban san me yasa murmushi ya zabi wanzuwa a fuska ta ba a lokacin duk kuwa da tsananin ɓacin da rai na yayi "Amma dai kasan nima ina da gidan uba ba daga sama na fado ba ko Salees, so ba daga daki ba ko gidan kace in fice ma yanzu se in tafi ai". "Mtsww, Ni dai ban ce ki fita daga gida ba sedai in Kuma ke kika so, daki dai nace ki fita dan yaro na ba inda zeje, ke ban da ma rashin imani kina kallon irin kukan da yaron yake yi ko tausayin sa ba kiji ba balle mahaifiyar sa da duk hankalin ta ke tashe se wani soki burutsu kike yi, ko da yake ai baki san ya rainon da yake ba tun da baki taɓa yi ba dole ki ga kamar karya ne". A wannan gaɓar kam tuni idanu na suka tara ruwan bakin ciki, ɓacin rai da kuma wani irin rauni dake tasowa tun daga can karkashin zuciya ta, ban kuma cewa komai ba na sauko daga gadon tare da ƙarasawa inda na aje jakata na ɗauka ina nufar hanyar fita daga dakin dauke da alwashi me girma cikin raina. Kan bed na faɗa ina sakin kukan da nayi dauriyar riƙewa, wani irin kuka me fitar da sauti sosai jikina na rawa, kallo ɗaya me imani da tausayi ze min yaji zuciyar sa ta motsa, Allah ya sani na dade da gajiya da zaman auren Salees, ba dan na daina son sa saba, ba dan bana son cigaba da rayuwa dashi ba, sai dan in aka cigaba da tafiya a haka lallai zuciya ta na gab da bugawa, in Kuma haka be faru ba na tabbata jinina se yayi yawan da saukowar sa se Allah, yanzu haka ina mamakin yadda ko yaushe nayi gwajin bp nake samun negative result dan a irin damuwar da nake ciki hawan jini shine cuta mafi kankanta da ɓacin ran gidan Salees ka iya haifar min...................!. _*Ba zan gaji da fada muku ba haka ba zan gaji da tabbatar muku da ba gazawa ce ta sa Allah ya kaddare ku da rashin haihuwa ba face jarraba irin tasa da yake yi dan gwada karfin imanin duk wanda yace yayi imani, da zafi, da ciwo, da damuwa, da rauni amma in akaa daure tabbas rabon me girma ne kamar yadda Allah da kan sa yace yana kunyar matan da basu taɓa haihuwa ba, Allah ya bada masu albarka inda rabo, in Kuma babu Allah ya azurta ku da dauriya da karfin iya jure wannan ƙaddara*_. Comment, share and follow. Ouummey 📚✍🏻. Ouummey 02 {4/28/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________                  _Free Chapter two_ Haka na kwana cike da kunci da ɓacin rai, kwata kwata dama ban sa ran Salees ya biyo ni wani rarrashi ba dan nasan ba yi zeyi ba, so da yawa na kan yi mamaki yadda tashi ɗaya rayuwar aure na ta juye daga happy married life cike da so da kauna zuwa wani yanayi da ba zan iya faɗa ba. Sai dai ba abin mamaki bane in akayi duba da irin nakasun da mutane ke gani tattare da ni, ba wai tawayar halitta ba, bana hali ba face na wani arziki da Allah ke bawa bayin sa da yaso ba dan kuma dan ya tsane mu mu da be bawa ba, a'a sai dai dan ya jarraba karfin imanin mu, wanda in ba ya shiga cikin lamarin ire ire na ba cin wannan jarrabawar tana yin wuya domin abun ba sauki, lamarin babu dadi sam haka yanayin me matukar taɓa zuciya ne. Da safe ko da na tashi ban fasa yin abin kari ba sanin nike da girki, sharp sharp na hada breakfast tare da zubewa kan table kana na ɗora na Ilham da zata tafi dashi school sannan na koma ɗaki dan shirya wa zuwa wajen aiki, a hanzarce nake komai dan na makara saboda rashin samun bacci da wuri sanadin ɓacin ran Salees da mariya. Sai da na tabbatar da zaman gyalen jiki na sannan na fesa turare kasa ƙasa wanda ba'a jin ƙamshin sa se an matse min waje sosai sannan na fito, kan table na tadda su zaune cikin farin ciki suna hira abin su, da ka gan su kaga wasu ma'aurata da rayuwa kewa dadi sabanin ni da rayuwar aure na ke cike da bakin ciki, ɓacin rai tare da takaicin da namiji iri iri. Kau da damuwa ta nayi na shanye ta cikin ciki na na karasa tare da jan kujera na zauna "Good morning zuma na, fatan ka tashi cikin koshin lafiya". Na faɗa ina kissing lips din sa kana goshin sa sannan na juya ga mariya "Barka da safiya maman Ilham, fatan kun tashi lafiya". Duk da naga sanda yanayin ta ya canja lokacin da na sumbaci Salees amma tuni ta ture tare da maye gurbin matsewar fuskar ta da wadataccen murmushi tana amsa min har da yar dariyar ta "Lafiya lau Auntyn yara, fatan kema haka". "Alhamdulillah kam". "Ehm nace dan Allah kiyi haƙuri da abinda ya faru jiya, sha'ani na yara ne me sa mutum ya rude amma ba da wata manufa nake kawo Amir ba, kin san al'amarin raino in ba wanda ya taɓa yi ko yake cikin yi wani abin ba yarda zaka yi in an fada ba, ni kaina da Umma ke faɗa min akwai yara masu kukan dare ban yarda ba seda na haihu, amma karki damu kema soon zaki fahimta in Kika haifa". Duk wannan surutun da take yi ni tuni nayi nisa da zuba abincin da zan karya dan Ina zama na zubawa Salees, ban ɗago ba duk da naji me tace ban kuma yi mamakin maganar da ta fa min a wayance ba dan indai ita ce nasan zata yi fiye da haka dan tuni na dade da gane da kuma fahimtar inda ta dosa. Wahalallen murmushi na kakaro na ɗorawa fuska ta na ɗago ina duban ta "Haba ai ba wani abu bane maman Ilham karki damu". Haka muka fara cin abinci tana ta zungurin Salees da hirar Amir da ta Ilham shi kuma ya biye mata dan a bayyane yake yana mugun son ƴaƴan sa tare da kulawa da duk abinda ya shafe su, gane hakan ne kuma yasa mariya ta samu damar kuntata min kamar yadda ta dauri niyyar yi tun haihuwar Ilham zuwa yanzu kan Amir. Tissue nasa na goge baki na ina miƙewa daidai fitowar Ilham daga dakin mamanta goye da skul bag ɗin ta na tafiya makaranta, tun da yarinyar ta fito na kalle ta na kau da kai batare da na sake duban ta ba duk kuwa da yadda nake son yin hakan. Allah ya sani ina matuƙar kaunar Ilham saboda yadda ta dauko kamaninn Salees kamar yayi kaki, yanayin ta na surutu da sakewa yasa take da farin jinin jama'a ciki kuwa har da ni sedai dole nake koyar dannewa tun wani incident da ya taɓa faruwa. "Good morning Daddy, good morning Mommy". Ilham ta gaida iyayen ta batare da ni ta kalle ni ba, ban damu da hakan ba na sake daidaita zaman mayafi na tare da ɗaukan handbag dina na kalli Salees "Ni na tafi se na dawo". "No ki tsaya ki sauke baby a school yau ba zan fita da wuri ba". Ya katse ni da sauri daga nufar falo da nayi, dole na ja na tsaya cike da damuwa dan na makara na kuma san se na kara wata a kan wadda nayi saboda sanin halin Ilham wanda uwar ta ta gama poisoning mind din ta a Kai na "Yi sauri kiyi breakfast ku tafi baby, yau Aunty ce zata kaiki". "To Daddy". Tace tare da zama ta shiga tsakuran abincin gaban ta kamar ba zata ci ba, ni kam daga tsayen da nake mamakin Salees ne ya cika min rai ganin yadda be damu da rashin gaishe ni da Ilham tayi ba, na jijjiga kai kawai tare da kallon wristwatch dina me tsada dake daure kan tsintsiyar hannu na kana na maida kan Ilham da se lokacin take yin spoon na uku a abincin. "Eat fast pls Baby, am already late". Ba wanda ya tanka min cikin su ukun haka kuma ba ta fasa cin abincin yadda ta ga dama ba, nikam tuni raina ya ɓaci dan nasan da hujja take yi dan ta bata min lokaci saboda i overheard them once tana fada wa uwar bata san tafiya dani saboda ni nake kai ta wataran kamar dai irin yau in baze fita da wuri ba, budar bakin uwar ta bata shawarar dinga bata lokaci in tare zamu tafi, a cewar ta har na gaji na tafiya ta kafin ta gama shininnikin ta. "Ina ganin zan wuce fa Abban Ilham dan na makara tuni gashi kuma naga ita bata gama ba". Ban jira amincewar sa ba bare umarnin tafiya na shiga takawa zuwa waje dan da kyar ma na lallashi kaina na yi maganar dan kar yaga laifi na sedai ashe ban tsira ba "Wai meke damun ki ne a kwanakin nan Khadijah, ina fa lure dake duk sanda nace ki sauke baby a school se kin kawo uzuri, makara, ba zaki fita da wuri ba and many more, me kike nufi ne?". Seda na lumshe ido jin wata sabuwar fitinar kuma da sanyin safiya kafin silently na juyo Ina tausar Kai na "Babu abinda nake nufi fa Abban Amir, kalli agogo it's already past eight kasan Kuma ka'idan aikina thirty minutes past seven ne na makara". "Ba matsala, zaki iya tafiya zan kai ta da kaina Allah yasa uban ta na da motar". Ɗan jim nayi kamar na tafi sai dai zuciyar neman zaman lafiya ta rinjayi me tunzura ni se kawai na koma cikin falon na zauna tare da rufe ido, daga haka nake jiyo maganar Mariya murya kwance cike da tsantsar kissa da yaudara "Haba baban yara, me ye na fusata haka, ai kaga tana da uzuri me ƙarfi, ko rannan ma ta tafi ta bar baby ne saboda tana da meeting, se kana mata hakuri fa, kasan bata saba da hidimar yara ba". Abin dariya wai Salees se ya dubi mariya "Abin da Khadijah ke min a gidan nan ya fara isa ta, amma ba komai ta cigaba". Se kawai fuuu yayi sama, "Dan Allah Auntyn yara ki dinga kiyaye abinda ze sa Abban Amir ya dinga miki faɗa haka, wallahi bana jin dadi". Ban iya cewa komai ba saboda kullutun da ya tare min makogaro, da na buɗe baki nasan ba me daɗi zan fadawa Mariya ba wanda da nayi hakan nasan wani tashin hankalin ze Kuma zama so se kawai na zabi yin shiru, ina jin ta tashi ta bi mijin ta sama ta bar ni nan zaune na kasa motsi cike da ɓacin ran da ta jagoranci zama silar sa, seda siririyar muryar Ilham yet cike da rashin kunya ta ratsa kunne na "Ni kin ga Malama in baki shirya tafiya ba ki bari in faɗawa uba na ya kai ni, atoh tun da ina da iyayen da suka haife ni su ba juya bane". Wal haka na ware idanuna na sauke kan fuskar yarinyar me cike da kuruciya hadi da yarin ta da a lokacin take shekara na sha uku, fuskar nan irin ta mahaifin ta a yamutse ta turo baki gaba cike da tsiwa yayinda madaidaitan idanun ta ke wulkitawa da hararar da take min. Cike da wani kudiri a raina na mike tare da fita daga falon ina dan karkada mukullin mota na har na karasa tare da budewa, farar mota ce me kyau tasha wanki tana ta ƙyalli, da addu'a na bude mazauni na na shiga tare da rufewa kana nayi unlocking sabida ta shiga dan ina hango ta biye da bayana, murmushi nayi jin shigar ta bayan motar wato ta mai da ni driver Kamar yadda ta saba in tafiya ta haɗa mu tun da ta fara wayo. Sai da muka hau titi sosai bayan na bawa me gadi ihsanin da na saba na cigaba da tuki na cike da nutsuwa, ba wata tafiye me nisa muka yi ba dan bamu gama fita daga unguwar ba na tsayar da mota tare da bude murfin na fita, door ɗin da Ilham ke zaune na bude tare da finciko ta a fusace har seda ta tsorata, na bude gaba na sakata bayan na watsa mata wani shegen kallo me cike da gargadi hakan yasa bata yi yunkurin komawa bayan ba har na shiga mazauni na. Kyakkyawan mari me kyau nayi wa bakin ta da ya gama zuba min rashin kunya ta yadda seda ta sa ihu tana rike bakin ga ba halin guduwa na rufe motar, kunnen ta na kama na riƙe da kyau ta yadda na san gargadi na ze shige ta na fiddo kyawawan ido na waje na haske ta dasu ina zare su "Duk sanda kika kuma yi min rashin kunya, kallon banza ko harara se na ci uban ki tun da baki da kirki, kina zuwa school kina haduwa da marasa tarbiyyan yara kina koya ko?". Da sauri ta girgiza kai jikin ta na rawa dan yadda na mata ba ƙaramin tsorata tayi ba ga bakin ta dake zafi dan har lips din sun fashe "Ni ba sa'ar ki bace balle ki kawo min iskanci, duk rashin mutuncin da ke kan ki se na sauke miki shi dan duk kika kuma min ɗaya daga abin da na faɗa se na kulle ki a daki na zane ki ciki da bai ko kuwa in wullo ki daga sama ki fado ki mutu kowa ya huta, zaki kara?". Yanzu ma da sauri ta girgiza kai na kuwa sake haɗe rai tare da zare mata ido "Baki da bakin magana ne kike min knodding?". Yadda nayi maganan a tsawace yasa bakin ta na rawa ta furta "A'a...a'a...ba zan kuma ba...". A firgice, haka na mata warning me kyau kafin na sake ta bayan nasa ta gyara kan ta na tashi mota muka cigaba da tafiya ina bin karatun Alkur'ani da nasa suratul Noor cikin raina kuwa cike fal da tunanin yadda zamu kaya da boss dina wajen aiki saboda nayi makara fiye da ka'ida a tsukin. Har cikin school premises din na kai ta tare da kara mata kudin break ta karba tare da barin wajen da sauri, na bi bayan ta da kallo ina tariyo tsoro na da na hango cikin idan ta sannan na fita, se kuma tunanin yadda zamu kwashe da Salees in ta faɗa masa ya fado min, dogon tsaki na ja ina jin na shiryawa duk ma me ze faru, abu ɗaya na sani ba zan dau raini daga uwar ya in Kuma na dau yarinyar ba, yar da da na sami haihuwa da tuni ina da sama da ita sosai, kai baze sabu ba wannan karon nima na shiryawa duk abinda Salees ya taka. Da wannan tunanin na karasa wajen aiki na inda nake aiki da ma'aikatar haraji wato revenue nake kuma da office na bakwai mafi girma a wajen, sai da na kai uzurin rashin lafiya wa me gidana kan na koma office ɗina Ina istigfar na karyar da Salees yasa nayi. Aikina nayi cikin nutsuwa duk da sa'i da lokaci wasu abubuwan na daga rayuwa ta kan fado min cikin rai sai dai bana bari ya zauna balle ya hana ni aiki na ke ture shi gefe. Waya ta ce ta dauki soft ringtone me daɗi wanda na sawa duk family na, ina dubawa na ga Ummi na ce, take naji wani sanyi ya shiga sauka cikin raina na dau call din cike da farin cikin jin muryar mahaifiya ta "Ummii naa" "Dijeehh naaah". Itama ta amsa min cike da so da kauna ta wanda suka fallasa kan su sanadin rashin haihuwa da Allah ya jarrabe ni dashi "I miss You Ummi naa, hope kina lafiya ba abinda ke damar min mamana". Sai da tayi yar dariya sannan ta amsa min "Ina lafiya Khadijah, ina fatan kema haka kuma babu wani matsala ko?". "Alhamdulillah, Allah ya kara muku lafiya ke da Abba na, matsala kam babu Ummi sai dai duk da haka muna bukatar addu'ar ku". "Wannan kam a kullum ba'a fashi Khadijah, kullum addu'a ta da fatana shine Allah ya azurta ki da rabo me albarka, Allah ya kare min ku ya tsare ku daga dukkan wani sharri ya albarkace ku ya kuma hada min kan ku". "Amin Ummi na, Allah ya saka da alkhairi ya kara girma tare da nisan kwana me albarka". "Amin, ki kwantar da hankalin ki ki cigaba da rayuwar ki cike da tawakkali tare da godiya ga Allah, har kullum ina faɗa miki be manta dake ba ba kuma baya son ki bane ya jarrabe ki, ki rike addu'a ki tsarkake zuciyar ki ki kuma zauna da abokiyar zaman ki Lafiya, dan Allah Khadijah kar ki bari sheɗan ya zuga ki a kan ƴaƴan ta ko ita, in da kara da mutuntaka ya'yan mijin ki naki ne, ki gyara musu ina suka kuskure amma ban da cutar wa dan Allah". Wani irin rauni ne ya lulluɓe ni kamar yadda ya kasance yana faruwa duk Ummi take min nasiha "Insha da Ummi na, ina iya kokari na ki cigaba da taya ni da addu'a, ina autan ki ne ban ji shi ba kwana biyu?". "Allah ya shige mana gaba, auta yana can ya fita neman maganar da ya saba, ai ni dai wannan da se Allah ya shirya min amma jin magana kam ba'a cewa komai". Da haka muka bar waccan maganar muka koma hirar mu har lokacin da muka yi sallama na aje wayar ina sauke numfashi.......................! Ouummey 📚✍🏻. Ouummey 03 {4/29/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey Ouummey 003 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________                _Free Chapter Three_ Hankali a kwance na tashi aiki tare da tattaro kaya na na fito, tsayawa nayi ina gaisawa da abokiyar aiki na me suna A'isha "Yau ba zaki jira oga ba kenan?". "Ai bana tunanin oga ya shigo yau dan a gida na bar shi". Na bata amsa, akan Salees take magana dan wajen aikin mu daya da shi sai dai ya fi ni matsayi da office uku, mataki na uku yake a ma'aikatar ni ina na bakwai "Eh na manta fa, kin san zasu je meeting a main branch so yau zasu tafi". Da yake na amsa mata dan na manta da batun haka kuma da zan fito be min sallama ze tafi ba, da haka muka rabu na wuce wajen mota na na shiga tare da barin ma'aikatar. Sannu a hankali nake driving zuciya ta cike da tunanika barkatai, wato dai yanzu ban da sauran matsayi a wajen Salees, da ni da banza kwance kusan ɗaya muke, to in ba haka ba ai ya cancanta ya min sallamar ze tafi ko. Wai a duk cikin yanayin da nake sai da wani bangare na zuciya ta ya dinga tursasani yiwa Salees uzuri, ban ja ba na yi masa ta hanyar yin tunanin maybe dan yasan na san zancen ne tun a office. Seda na tsaya a mall nayi siyayyan kaya shafa na da suka yi kasa tare kuma da undies dina da naga kaman sun ɗan yi sanyi, ban fito ba se da na siyowa baby wato Ilham wata gown me kyau da ta burge ni Amir kuma wani takalmi me kyau, wannan sabo na ne bana yin siyayya ban musu tsaraba ba har Salees, Mariya ce dai ban taɓa ɗorawa kaina yin wannan karyar ba dan ba zan iya ba, shima Salees ɗin daga baya aje wa nayi ganin ba sannu bare na gode. Sai da na adana motar inda ya kamata sannan na kwashi ledoji na zuwa main falon mu, da sallama a baki na na shiga , yuuuu haka Mariya da ƙawayen ta suka zuba min ido kamar sun ga wata sabuwar halitta lamarin da yasa naji na tsargu dan kafin na shigo kaya kaya haka nake jin surutun su. Kadaran kadahan na musu sannu da gida na wuce daki na ina tafe ina jin kaifin idanun su da suka min rakiya da shi, zube ledojin nayi kan bed tare da zama ina aje numfashi, seda na huta sannan na cire kaya tare da shiga toilet na yi wanka. Jakar shopping ɗin su Amir na ɗauka na fita bayan na shirya cikin atamfa ta purple color ɗinkin riga da skirt da suka zauna a jikina suka kuma kama ni wanda yawancin dinkuna na duka haka suke, duk tsadar kaya bana bakin cikin kacaccala shi wajen yin dinkin da nasan zasu zauna a jikina in birge me gida. "Sannun ku fa, maman Ilham ga wannan nasu Amir ne". Na faɗa ina aje mata ledar a gaban ta kana na juya zuwa kitchen dan yin girki "Oh mace har mace amma bata da wani amfani, to meye amfanin juya da bata haihuwa?". Kalaman daya daga cikin su da na jiyo dan dama a yadda ta daga sauti take magana ta faɗa ne dan naji "Haba ke kuwa Asmah, bana san neman magana, ya muna zaune ƙalau da yar uwa ta kina min irin wannan kalaman?, Gaskiya bana so". Mariya ta fada da murya me kaman tana dariya ne ko kuwa, nidai ban tsaya ba na shige kitchen din na Kai jingine jikin Island da sauri ina sauke numfashi a jere a jere kamar wadda tayi tseren gudu, makogaro na ya bushe kamar wadda ta shekara bata sha ruwa ba, da kyar na iya lakato wani yawu me daci na haɗiye ina lumshe ido, a kuma lokacin ruwan hawaye ya fara zarya kan kunci na, halin da na shiga a lokacin ba me bayyanuwa bane. Sanin suna falon yasa na daure zuciya ta na lallashi kaina na hada fruit salad maimakon noodles da na shigo da niyyar yi, juice na ɗauka me sanyi tare da bowl dina na fita cike da fatan kar wata ta kwata faɗa min irin maganganun nan dan a yadda nake ji zan iya biye musu muyi duk wadda ta kama. "Auntyn yara angode fa". Yatsu biyu na daga mata batare da nace komai ba na shige ɗaki, da kyar da sidin goshi na sha salad din nan dan wani daci naji yana min a baki. Kuskure baki nayi bayan na gama na ture plates din gefe tare da ɗaukan waya ta ina dubawa wai ko zanga missed call din Salees, sedai ga mamaki na ko text babu balle kira, murmushin takaici nayi tare da kiran shi ni, ta dade tana ringing be dauka ba har ta katse na sake kira shima be ɗauka ba, seda na masa miss call biyar sannan ya turo min short text "Busy". That's all he said, Ina gani na aje wayar jiki a sanyaye, saboda gudun tunanin da ka iya rufe ni na janyo tablet dina na hada mata keyboard na shiga ayyuka a ciki, duk wanda ya ganni kallo ɗaya ze min yasan ina aikin ne kawai amma ba dan jin dadi ba. Dake Allah Alhakeem ne se gashi tashi ɗaya ya aiko min da sanadin farin ciki madaukaki, ba komai bane face karin matsayi da ake shirin yi a ma'aikatar mu, cikin rahamar Ubangiji kuma har da suna na cikin wanda za'a yi reviewing Wanda muna sa rai in mun tsallake review shikenan promotion ya tabbata. Ban yi farin cikin ni kaɗai ba na kira Ummi na na faɗa mata tare da fatan a taya mu da addu'a ta amsa, yayata Salima na kira itama na sanar da ita, ba tun yau ba na fahimci kunya da nauyi na ta take ji ba sedai ni a raina wani irin girman ta nake gani domin tai min abinda ba kowa ze iya ko kwatanta wa ba. Ta taya ni murna tare da fatan dacewa, tana neman kashe wayar na tare ta da sauri "Ina yaro na?, Shiru baya neman mommy?". "Ba haka bane ba maman Haidar, kin san baban makarantar wuni ya kai shi saboda yaki maida hankali a waccan". "Ayya, dan Allah yaya a kula min da shi sosai, kar a bar min shi da yunwa da damuwa". Daga cikin wayar na jiyo faffaɗan murmushin da tayi tare da amsa min mukai sallama na kashe wayar sabon zafi na sake hudowa daga kirji na sedai tuni na dakatar dashi saboda bana san abinda ze dinga tuno min da baya, duk da present din ma ba dadi ne dashi ba amma bayan nan akwai ciwo me matukar raɗaɗi. Seda na tabbatar ƙawayen Mariya sun tafi dan gidan yayi shiru ba hayaniyar su kana na dau bowl din da nayi amfani dashi na fita zuwa kitchen. Zama nayi a kujera tare da kunna Tv na shiga kallon wata drama da ake yi a mbc Bollywood, cike da zallar nishadi na kalli abina har aka gama na tashi zuwa daki dan It's evening, akwai bukatar in kwance kai na dan sati na biyu yake ciki. Seda nayi Asr sannan na fara tsifar a falo ina yi ina sauraren wani hirar classmates dina a group da sukai ta hanyar voicenote, a lokacin ne kuma baby ta shigo dan se five ake tashin su, da karfin gwiwar ta ta shigo murya a sama tana ihun kiran sunan uwar ta ita kuma tana saukowa daga sama tana amsawa sedai tashi ɗaya taji dif yarinyar tayi shiru. Wai ashe ni da ta tarar cikin falon ne yasa ta ɗauke wuta jikin ta ya shiga rawa, sam ban ma lura ba ni hankali na na kan abinda nake ji seda naji babar na tambayar ta "Me haka, lafiya na ga jikin ki na rawa?, Me ya faru?". Da mamaki na daga kai ina kallon su, yarinyar ta maza ta faɗa jikin mamanta tana zare ido, ko da na gane abinda ke faruwa se kawai na dauke kai na cigaba da abinda nake yi ita kuma taja ta daki tana tambayar ta. Ban san me ta fada wa uwar ba se ganin Mariya nayi a gabana a tsaye kamar wata bishiya "Wane irin rashin imani ne yasa kika yi wa Ilham wannan marin, kin kuwa ga yadda bakin ta ya kumbura?". Kamar kar in tanka se kuma na tanƙwasa kai na sanin shi bayani yana da dadi kuma rigima sam ba abar so bace musamman gare ni da ba hali na bace, zama da Mariya ne yasa har ban san yaushe na canja ba. "Ilham rashin kunya take koyowa Mariya, wai kamar ni zata kalla ta zaga, imagine fa". "Ban gane zagi ba, kin ga tun kafin raina ya ida ɓaci ki min bayani yadda zan fahimta, Ilham ta zage ki tace miki me ?". "Kin san dai ko ke baki isa in miki karya ba balle ƙaramar yarinya kamar ta, ce min tayi wai Allah yasa tana da iyayen da suka haife ta tun da ba juya bane su". Ƙanƙance ido tayi cikin rashin mamaki balle damuwa "To ai ba karya tayi ba tana da iyaye, shima juyan ai ba sharri tayi ba tunda da juya ne su da basu haife ta ba, shine kawai dan wannan yar maganar zaki nemi lahantata, to wallahi bari uban ta ya dawo dan ba zan yarda ba". Iya maƙura raina ya kai wajen ɓaci dan haka na mike tsaye nima kamar yada take "In Kika yarda ma ba sunan ki Mariya ba, haka kuma in Kika fasa fadawa Salees ba ki haifu ba, maza faɗa masa yazo yayi wa khadeeja tuf ta mutu kin ji, shashasha mara tunani, a faɗa miki yarki tayi wannan rashin mutuncin amma ki goyi bayan ta saboda rashin sanin ciwon kai, to ai karki fasa, dan yau dai ba ayi masa haka in zaki gyara ki gyara". "Naki na gyara, nace naki na gyara ɗin, yar ki ko yawa, aikin banza da zaki zo kina wani kinibibi ai se ki bari se kin haifa se karki goyi bayan naki, ko da yake macen da ta shekara sha shida da aure bata taɓa ko bari ba ta ina zata haihu, wai wanda be san ciwon da bane zece ga yadda za'a masa tarbiyya, mtsww juya kawai mara amfani". Wannan kalma ta juya itace kalma mafi ciwo a duk cikin kalaman Mariya, sanin babban weakness dina gorin rashin haihuwa ne yasa Mariya daura damarar cewa se ta ga karshe na, gashi ni kuma bana iya daurewa wannan gorin, ko nayi kokarin haka se fuska ta ta bayyana halin da nake ciki, idanuna da suka yi jajir na kalli mariya dasu se kuma na juya na shige ɗaki da sauri ita kuma ta raka bayan da harara. Cikin son karfafawa kaina gwiwa na dinga tausar kai na dan na gaji da kukan da nake yiwa mariya, na gaji da bata hawayena kan ta, na gaji da komai ma na ta. Haka na wuni a daki saboda bana san fita balle shaidan ya raya min wani abu na biye mata balle kuma azo ace laifi na ne kamar yadda ake ɗora alhakin komai dake faruwa a kaina, saboda ita ɗin kirsasshiyar mace ce da gane halinta na gaskiya se wanda Allah ya ciyar kamar dai iri na da zama ya haɗa ni kishi da ita na zama victim. Washegari ban taya jiran wata Ilham ba na tafiya ta aiki, ko da na gama na dawo a nan na tadda me gidan ya dawo dan ina shiga falon idanun mu suka sarƙe cikin na juna, wani kallo me zafi na watsa masa cike da jin haushin sa, tun da mutumin nan ya tafi be kira ni ba balle text, ni nakira shi ya turo min kalmar "busy", daga ita kuma be kuma cewa komai ba haka kuma be neme ni ba, wanda in rayuwa da adalci kamata yayi ko da ace busy din ne in yayi free ya Kira ni yaji ya nake, ya bani haƙurin tafiya batare da ya sanar dani ba tun da ina da hakki amma duk be yi haka ba se dawo wa nayi na tadda shi a dararraje cikin iyalin sa suna hira cikin farin ciki da alamar rayuwa ta gama yi musu daɗi. Ko da nayi sallama ban lura da sun amsa ko ba su amsa ba nasa kai ciki, kamar in wuce batare da na kula shi ba se kuma zuciya ta tuna min da zaman kishiya a tsakanin mu wato Mariya, haka na daure cikin son nuna babu wata matsala tsakanin mu na tafi gare shi da niyyar yi masa side hug amma se ya goce yana watsa min zazzafar harara lamarin da yasa na ɗan yi turus cike da kunyar yarfa nin da yayi a gaban kishiya "Daga ina kike?". "Wajen aiki". Na bashi amsa a sanyaye idanuna na cika da hawaye "Me ya hana ki kai baby school?". Ɗan jim nayi kafin na buɗe baki "Bata shirya ba ni kuma zan makara". "A'a Khadijah kiji tsoron Allah gwara ki faɗa masa gaskiya kawai, wallahi dear tun seven na safe baby take a shirye, dalilin ta na kin kai baby kawai dan tayi abu ba daidai ba na yi magana ne. Wai baby ce tayi mata rashin kunya shine ta mari bakin ta da kuncin ta tare da murde mata kunne, to ganin yadda ta dawo da zazzaɓi a jikin ta fuska a kumbure yasa na yi mata magana, daga cewa ta dinga sassauta hukunci shikenan take fushi da mu a gidan nan, ko magana bata kuma yi min ba tun jiya har yau da ta fita shine kuma dalilin barin Ilham, dan Allah ka bata hakuri, Khadijah kiyi haƙuri ni ba da wani abu na faɗa ba". Irin yadda take tsara labarin abin da be faru ba tare da cakudawa da burbushin gaskiya yasa kawai na zuba mata ido na ma kasa magana, shi kuwa Salees batare da binciken gaskiya ne ko karya bane ya hau kai ya zauna ya dinga surfan bala'i, yi yake kamar bazai daina ba, nikam da na gaji kawai na wuce su na shige ɗaki na kama kuka dan na kasa daurewa. Wai ashe laifi nayi da na tafi na bar shi a wajen, bawan Allahn nan be yi duba ga halin da nake ciki ba, be min adalcin jin ta baki na ba, be tausaya wa ƙaddara ta ba ya kira Hajiya Iya ya shiga faɗa mata karya da gaskiya. Kiran wayar Hajiya Iyan ne ya katse min kuka na inda tace tana jira na gobe a gida, da toh kawai na amsa na kashe wayar raina a bace, zuciya ta cike da kunci dan nasan a can ɗin ma ba za'a saurare ni ba, ba za'a bani dama ba, za'a yanke min hukuncin da aka so ne kawai bisa doron son zuciya, nikam ina ganin ƙaddarar rayuwa.............!. Ouummey 📚✍🏻 Ouummey 04 {4/30/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey Ouummey 004 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________                _Free Chapter Four_ Ragowar ranar nayi ta ne cikin damuwa da tunani, kwata kwata na rasa meke min dadi a duniya, irin yadda kaddara ke kwallo da rayuwa ta abin ba'a cewa komai. Ko da dare yayi kasa barci nayi, so nake na samu wani mu zanta ko naji sanyi cikin rai na sai dai na rasa wa ya kamata na yi maganar da shi, Ummi na kullum cikin son ganin ta kwantar min da hankali take inda ni kuma nake tabbatar mata lafiya nake a kullum ko da ba hakan bane saboda gudun shigar ta damuwa, yaya ta daya mace wato Salima sai dai bana jin zan iya maganar nan da ita saboda gudun sa ta jin kunya, ragowar yayye na biyu maza ne, duk da suna tausaya min suna kuma so na sai dai bana jin zasu gane halin da nake ciki. Ban san yadda aka yi hannu na ya danna number Abban mu ba kamar yadda muke kiran mahaifin mu se jin muryar sa nayi yana min sallama, a lokacin dukkan wani rauni da nake ta boye wa da dannewa ya bayyana kan sa ta yadda ban san ya akayi ba se ji nayi na fashe da matsanancin kuka me tada hankalin duk me saurare, shiru Abba yayi be kuma cewa komai ba tun bayan amsa min sallama da yayi, haka ya bar ni nayi kuka na har na gaji murya ta ta dusashe kafin can kasa yayi gyaran muryar da ya shaida min yana bukatar in saurare shi, ban musa ba na katse ragowar kuka na se yar sheshsheka da ajiyar zuciya. "Uwatah". Yadda ya kira sunan cike da kwantaccen lafazi da sanyin murya yasa naji sabon kuka na neman kufce min, na amsa masa da murya me rawa "Na'am Abban mu". "Bani hankalin ki nan ki saurare ni sosai". A wannan karon itama sheshshekaar dakatar da ita nayi tare da sake shigewa cikin katifar gado na me aminci "Rayuwar duniya gaba ki dayan ta jarrabawa ce, ita kuwa rayuwar aure yar hakuri ce, uzuri a gurin da babu muhallin sa, kau da kai a abinda yake zahiri ko da an cuta maka, danne bukatar kai saboda ta abokin rayuwar ka, ji ka nuna baka ji ba, ka gani ka nuna baka gani ba haka kuma a taba ka ka nuna baka san an yi ba ta hanyar yafiya. Base kin ce min komai ba ba kuma se kin fada min halin da kike ciki ba, kukan ki ya bayyana min komai, sai dai ina so in tuna miki da abin d kika manta, ni baban ki ne, dan Adam kuma ajizi, da ni dake Allah muke bautawa gaba ki daya haka kuma wajen sa muke neman taimako, kama ta yayi da damuwa tayi miki yawa ki tashi ki dauro alwala ki fuskanci qibla ki kai kukan ki wajen me duka cikin kaskan da kai, yi masa kirari da kuma tsarkake shi, ina me tabbatar miki da wallahi in kika yi hakan zaki sami saukin kome ke damun ki, damuwar ki zata yaye, ruhin ke ze aminta haka kuma zaki sami nutsuwar zuciya. Ba kamar ni ba da in kika fada min sai dai in miki kalamai wanda bayan haka ba abinda zan miki in Kuma ba so kike in zama uban kawai me shiga sha'anin rayuwar auren yar sa ba. Yanzu maza ki tashi kiyi kamar yadda na fada miki kinji, insha Allah nima zan taya ki, a kullum cikin addu'a ta kike uwatah ke da sauran yan uwan ki amma zan kara da izinin Ubangijin mu, ina fatan Allah ya yaye miki kome ke damun ki, ya aminta da ruhin ki ya kawo miki sauki da salama a rayuwar ki, zan kira ki da safe, Allah ya bamu alkhairi". Kit Abba ya kashe wayar sa da ya gama min wannan bayanin, be saurare ni ba, bance masa komai ba game da halin da nake ciki amma ga mamaki na wallahi se na ji kaso fiye da hamsin cikin kuncin da nake ci ya kau, lallai na gaida iyayen mu,  ya Allah  kasa iyayen mu su cika da imani ka saka musu da mafificiyar aljanna, Amin. Batun yanzu ba ina sha'awar rayuwar Abban mu da Ummin mu, so da yawa ina fadar in da ace kowane miji kamar Abban mu yake da ba'a samu gurbacewar rayuwar aure ba, da ba'a sami yawaitar matsalolin aure ba, da ba'a samu yawaitar zawarawa ba haka da mata basu ji tsoron aure ba, in Kuma na dube shi ta fuskar uba se in ga lallai babu ya'yan da suka kai mu yin dacen uba nagari, se in dun ga tausayin wanda Abba be kasance mahaifi gare su ba har in dinga ganin lallai sun yi rashi babba. Alwala nayi na shimfida tsaftatacciyar pray mat dina dake nan kamar sabuwa saboda samun gyara na sa wadataccen hijab dina na kabbarta sallah, a cikin kowace sujjada kuka nake yi gaban Ubangiji ina rokon sa sauƙin rayuwa, farin cikin rayuwa, haka kuma yayewar bakin ciki tare da cikawa da imani, irin kukan da nayi ba zan ce ga sanda nayi shi ba dan tun da na dora goshi na a kasa naji bani da wani sauran karfi ko kwarin zuciya. Cikin ikon Allah na yi raka'a goma wato sallama biyar sannan na daga hannu na cigaba da addu'a, ina shafawa na dau Kur'anin da na aje gaban sallaya ta na budo Suratul mu'umin na soma karatu cikin kyautatacciyar kira'a murya can kasa dan gudun takurawa abokan rayuwa ta a gidan, sai da nayi surori uku bayan ta sannan na rufe tare da sake wasu addu'o'in na kuma shafawa, abin babu karya ba kuma yaudara tun kafin na kai ga idar da sallar naji zuciya ta wasai tamkar ban taba sanin wani abu wai shi damuwa ba, farin ciki da walwala suka cika rai na tamkar wadda akayi wa bushara da kujerar hajji. Agogo na kalla wanda ya nuna karfe biyu da rabi na dare na tashi na cire hijab din da na sa na rataye shi tare da maida daurin dan kwali na na nufi gado na na kwanta hannu na rike da calbi ina ja cikin kirari wa madaukakin sarki, cikin rahmar Allah se gashi na samu salamammen bacci me cike da jin dadi kamar kar na farka dan se da nayi da gaske na iya tashi asuba ba kamar ragowar ranaku da ake kiran farko a kunne na ba saboda damuwar da kan hanani bacci, lallai Allah buwayi ne garara misali haka kuma duk wanda ya bar Allah tabbas yayi hannun riga da nutsuwar fili har ma da ta boye. Ba fa wai na manta da abinda Salees ya min bane, ba kuma na manta da kara ta da ya kai wadda zamu je yau bane kawai dai damuwar hakan Allah ya cire min daga rai na. Ban yi gigin yin breakfast ba dan ban manta layin d ya shata min ba na cewar in har ban kwana dakin sa ba to bani da girki gaba daya, ma'ana har dafa abinci, a can baya da yasa dokar na damu amma a yau se naji ni hakan ma yayi min dan gashi na samu damar bajewa a gado ina baccin safe kasancewar asabar babu aiki. Se after 10 na tashi nayi wanka da shower gels dina da ragowar turarukan wanka masu kamshi da gyaran fata wanda a kullum yanayin yadda nake kula da jikina yake bawa wanda suka san ainihin shekaru na mamaki, dan da yawa mutane basa yarda na kai shekaru na, so da yawa se kiga ana bani shekara Ashirin da biyar da shida koma da hudu, nidai in irin haka ta faru sai dai nayi dariya kawai, amma fa bana mamaki dan ko ke kika kalle ni ba zaki ce nayi talatin har da biyu ba wanda sune shekaru na na gaskiya da gaskiya . Doguwar riga na sa kirar Morocco, kafin kace me na zama wata bakar balarabiya saboda yadda rigar ta min ainihin kyau ta bi dirarren jiki na ta zauna Kamar yar asalin ƙasar, kai har ma nafi dan su ba su da cikakken diri irin nawa. Karamin fridge dina na bude tare da zubawa kayan snacks din ciki ido sannan a hankali na debi samosa uku tare da drink na maida murfin na rufe, a tsanake naci abina na kora lemo na kara da ruwa me dan sanyi, take naji ciki na y dauka masha Allah na koma  tare da zama kan doguwar cushion din dakin ina bibiyar chats din kawaye na cikin group din mu me suna *UWAR GIDA*. Knocking din da aka min yasa na dan saurara daga karanta wani post da nake yi kana na tashi na tafi na bude bayan na kuma jin wani, Sahal ne me bin Ilham, tsakanin su shekara daya ne dan yanzu sha biyu yake yayinda ita take sha uku "Daddy yace ki fito". Yace tare da barin wajen da sauri, jinjina kai nayi tare da komawa daki ina fadin "Wata matsalar ta dawo" a raina dan zan iya cewa Sahal har yafi Ilham dan shi kan kamar uwar sa ta bashi zuciyar ta ne, bakin hali a cikin yaron abin se addu'a shiyasa tun farko ban sake masa ba bare ya raina ni ko da dai b wai girmama ni yake ba duk tsare gida na, tun hutu ya tafi gidan iyayen Mariya kuma ko da aka koma makaranta be dawo ba ta can yake tafiya se yau da aka dawo dashi. Sai da na koma gaban madubi na sake gyara zaman mayafi na na kara turare kadan me sanyin kanshin da baya tashi sannan na dau waya ta da karamar purse dina na fita, basa falon hakan yasa na fita compound bayan na rufe kofar falon. A tsaye na hango Salees jikin motar sa wadda ina fitowa ya bude ya shiga, takawa na shiga yi zuwa wajen su sedai kafin na karasa ya ja motar sa yana yi wa maigadi horn ya bude gate tsayawa nayi kallon ikon Allah se kuma na bar shi as tun d ta kusa dani zai wuce maybe ze tsaya in shiga, "Motar ya cika, ki biyo bayan mu a naki tun da kina dashi". Sakatoto nayi ina bin shi da kallo kafin kuma na kau da mamaki da sauri dan wannan kadan ne daga halin shi, shi in har kuna fada to fa ba zaki kuma jin dadin sa ba, duk yadda ze bata wa mace rai to se yayi so tuna haka se kawai na saki murmushi me kyau na gyada kai na alamun toh na juya zuwa wajen mota ta. Farin ciki na daya , kamar yadda yace ina da motar, mota kuma ba karama ba domin suna gogayya da tasa a wajen kudi, bangaren tashe kuwa har ma tawa ta zarta tasa, ina tsananin so da kaunar motar domin kuwa Abban mu da hannun sa ya bani kyautar motar lokacin da Mariya ta haifi Amir wata shida da suka wuce. Cikin tuki na na natsuwa na fitar da motar daga gidan tare da hawa titi na nufi babban gida kamar yadda suke kiran family house din su inda nan ne iyayen Salees suke. Gefe da tasa motar na aje parka tawa sai dai ban fito ba sai da na gama addu'o'i na na samun rinjaye kan makiyi dan kusan zance makiyan nawa ne mutanen da zan hadu dasu. Bakin babban falon Hajiya Iya nayi sallama tare da daga labulen na shiga bayan na sabule takalman kafa ta, a duk cikin mutane takwas dake zaune a falon ba'a sami ko daya da ya iya amsa min sallamar da nayi ba wanda hakan ba bakon abu bane a waje na, gefen one sitter na samu na zauna kana na shiga gaida Hajiya da ta nuna kamar bata san da shigowa ta ba tana yi wa Amir dake hannun ta wasa, seda na maimaita gaisuwar sannan ta amsa min a watse. Daga Lafiya lau din bata kuma cemin komai ba nima kuma naja baki na nayi shiru, sai da ta gama da shalelen ta sannan ta mikawa Hannatu kanwar Salees dake zaune a wajen Amir kana ta fuskanto mu gaba daya. "Uhm, kace mene?". Dan muskutawa Salees yayi ya fara rattabo zance kamar me karanta labari "Hajiya karar khadeejah na kawo miki, ban san meke yawo a ranta ba, ban san wake zuga ta amma gaba daya ta birkice, gaba daya ta canja halaye da dabi'un ta ta kwaso mugayen akidu da ra'ayi ta ɗorawa kan ta. Babu damar naman Amir tayi wani abu yanzun nan se ta hayyako ta fara fadin maganganu marasa kan gado, kwata kwata bata neman zaman lafiya kamar yadda ita Mariya ke son su rayu cikin salama, a kullum burin ta ta kuntata min ta bata min rai. Duk ma kuma ba wannan ne babbar damuwar ba, kin ga yaran nan wallahi khadeejah yadda ta tsane su bana jin ko makiyin ta ta tsana haka, daga ni uban su har ita mahaifiyar su bamu san me mukai mata ba da take neman saukewa kan su. Shekaranjiya iIlham d zazzaɓi ta kwana me zafi saboda yadda ta fasa mata baki ga kuma kunnen ta da ta murde saboda wai tayi mata rashin kunya wanda zan iya rantsewa baby ba zata yi haka ba sedai yarinta, wai kuma daga uwar ta ce ta dinga sassauta hukunci shikenan ta dau fushi da ita da yaran har tana tafiya wajen aiki ta bar baby bata je makaranta ba saboda tana tutiya da tinkahon baban ta ne ya sai mata mota, Hajiya Iya fa abubuwan da zan iya fada miki kenan kuma akwai wasu bayan su sai dai in zan zauna lissafa miki wallahi zamu wuni ba mu gama ba, shiyasa na kawo ta gaban ki ta fadi meye matsalar ta da ni, Mariya ko yayana".............. Ouummey 📚✍️. Ouummey 05 {4/30/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________                            _Free Chapter Five_ Har ya gama zuba surutun sa ina zaune kamar yadda nake tun farko sedai tsoron Allah ya dade da cika zuciya ta jin wai yau a kaina ne Salees yake rattabo wadannan Laifuka da matsaloli, lallai rayuwa juyi juyi ce wai kwado ya fada ruwan zafi. "Uhmmm yanzu duk wannan abubuwan ita hamshakiyar ke yi amma ka zauna kana kunsar bakin ciki, lallai sannu khadeejah autar mata". Sake kasa da kai nayi ina jin tune din da Hajiya Iya ke magana dashi kafin ta ja dogon tsaki "Ke dago nan ki kalle ni bana son munafurci, ana magana kina sunkuyar da kai kamar wata mumina bayan kasurgumar muguwa ce ke, dago nace ki kalle ni". A sanyaye na dago na zuba ido na cikin na Hajiya Iya "Yanzu ke dan kin kasance butulu wadda bata san alkhairi ba har ya'yan Salees abin ki ne a wajen ki bayan dimbin halaccin da yayi miki a rayuwa?, Da zaki fidda hannu ki daki yarinya karama irin haka saboda baki san zafi da ciwon haihuwa ba, anyi magana ke ga Sarkin an iya bakin rai kin dauki fushi da su". Se kuma ta juya kan Salees "Ai duk kai ne shashasha shi yasa har mace ta raina ka, ban da raini kana kallon ta tana iskanci ka zuba ido baka yi maganin ta ba, ko da yake ai ta gama da kai yanzu ma da sauki tun da kana iya ganin laifin ta". "Saurare ni nan kiji, in kin gama da Salisu to ni na fi karfin ki, shima kuma gashi nan Allah ya fara karya alkadarin ki ta hanyar matar kwarai da ya samu, na san ba komai ke damun ki ba face bakin ciki da hasssada tare da asararren kishi, ke a rashin tunanin ki se mu bar Salisu ya zauna da ke kadai bayan ba haihuwa kike ba, kullum yayi ta cika miki ciki da abinci kina juye wa a masai babu fus balle as, to ta Allah ba ta ki ba, jinin Salisu ne gasu nan kina gani, karewar bakin ciki ki hadiyi zuciya ki mutu ni da wallahi farin ciki zan yi dan zaman ki gidan dana dan kawai babu yadda zan yi ne amma ba so nake ba. Batun yara kuma daga yau na shata layi tsakanin ku, ko da wasa kika Kuma kai hannun ki kan jikoki na wallahi a bakin auren ki dan se Salisu ya sake ki ko na tsine masa albarka, uwar su kuma in dan kin ga me hakuri ce kike cuta mata to Allah yana kallon ki kuma baze bar ki ba". "Kai kuma in zaka dauki mataki akan juyar matar ka ka dauka in kuma zaka cigaba da zama tana raina ka kai ka sani". Hakuri Salees ya shiga bawa Hajiya Iya ganin har dashi cikin fadan sedai ni tun daga gaishe ta ko tari ban yi ba balle wani ban hakuri, na bata hakuri akan me, me nayi mata, bayan duk cin zarafin da aka min kuma na bada hakuri, tabdi. Aikuwa rashin bada hakuri na ya sake tunzura Hajiya ta cigaba da bala'i da fade faden maganganu na cin mutunci d zarafi a kaina har muka mike zamu tafi "Allah ya bamu alkhairi Hajiya". Na mata sallama batare da na bada hakurin ba, Hannatu tayi tsagal ta zage ni yarinyar da yanzu take shekara sha takwas, fadin shekarun da na bata ma bata baki ne "Juyar banza da wofi mara amfani kawai, ciki ba komai se kashi, mtsww Allah dai ya raba yayan mu da kayan bakin ciki". Na jita sarai kuma zagin ya ci min rai dan na tsani raini a rayuwa ta shiyasa duk runtsi bana yarda na wulakanta ko cin mutuncin na gaba da ni. Ashe shima Salees zagin ya masa zafi dan har na dan yi gaba se ji nayi ya fisgo ni baya kofar dakin hajiyar ya hade rai tamau yana yiwa Hannatu mugun kallo "Dan ubanki matata sa'ar ki ce?". Ya tambaye ta a kausashe lamarin da ya matukar daurewa Hajiya Iya kai dan su a ganin su ai yanzu Salees ya daina so na dama suna cewa soyayyar sihiri ce, to tun d yanzu ya karye ai zasu taka ni yadda suke so "Kar ka kuma zagar min ya in ba haka ba ranka ya ɓaci". "Amma Hajiya kin san dai hakan ba daidai bane, ban da iskanci karamar yarinya kamar Hannatu ta kalli khadeejah ta zage ta, Hannatu da bata fi kanwa ta kusan shida ba wajen khadeejah, to wallahi tun wuri ki shiga hankalin ki in ba haka ba se na kusa karya ki, mahaukaciya mara hankali kawai". Ya fada yana karasa directing maganar kan Hannatu, nidai ina samu na zame hannu na daga cikin nasa se kawai na yi gaba abina na fice dan wallahi ko kadan shigan min da yayi be burge ni ba. Na riga su isa gida dan haka na shige daki na kulle tare da yin lamo kan gado na, in ka ganni zaka yi zaton wata marainiya ce d babu uwa kuma babu uba haka babu sauran gata, kulle ido na nayi ina sauke numfashi ina fadawa kai na rayuwa ce haka kuma Allah yaso gani na, jarrabawa tace da ban isa na tsallake ba har na samu na ji sanyi a raina kafin na shiga toilet dan yin wanka. ★★★★★ "Yanzu haka zaki zauna kullum kina kuka akan matsala daya, na baki shawara tuntun tuni Falmata amma kin share, kin gwammace ki yi ta asarar hawayen ki a banza ko, to ai shikenan". Babbar mace da a kalla zata kai shekaru hamsin da biyu zuwa da biyar ta fada tana kallon kawar ta dake zaune ta zuba tagumi hawaye na bin fuskar ta kamar an bude famfo. Ganin bata ce komai ba yasa matar jan tsaki tana duban Falmata "Bata akan ki kadai abin ya tsaya ba, yanzu haka ina fada miki da zan shigo na hadu da wancan fitsararren dan Adam, wallahi yaron nan akan ido na yayi min tsaki har da tsartar da yau sannan ya shige bangaren su, shin haka zaki zauna ke a raine wanda ya alakantu dake ma ana masa kallon banza shara wofi mara amfani Falmata, shin ba zaki yi komai domin kwato abin da ya kasance naki ba tun farko? Ko kuwa zuba ido zakiyi har se rayuwa a gidan nan ta gagare ki, ki dubi karamin yaro Haisam irin motar da yake hawa ki kuma dubi taki wadda kike jin jiki da ita tuntuni, ya kamata ki farka daga barci da kike yi ki amso what is rightly yours, Ina baki shawara ne matsayin yar uwa aminiya wadda bata san ganin ki cikin komai face farin ciki".   "Ban damu da nawa ze kashewa yayansa ba Farida, ban kuma damu da kyautatawar sa gare su ba, damuwa ta yadda kome na bukaci Alh yayi min se ya kawo uzuri, ba kuma ze yi abin nan ba ko da zuwa da shekaru nawa ne, a cewar sa kullum nauyi kara karuwa yake a kan sa saidai yana mantawa cikin nauyin nasa akwai ni, ina da hakki a kan sa wanda a yanzu ya sauke wa kan sa, da ni da babu duk daya ne a wajen sa, se ya shigo ya ishe ni da dadin baki, kin san matsalar da nake fama dashi na ciwon ciki, naje naga likita akan shi sedai ya bukaci naje babban asibiti, to ko da naje sun ce se an min aiki, yanzu halin da ake na fadawa Alh dan ya shirya min tafiya zuwa India ayi min aikin a can amma yace be da kudi se gashi dazun nan a gabana yayi wa yar lelen sa alkawarin sabuwar mota zuwa gobe, ban face ya bini ba, ban kuma ce ya biya min tare da wani da zai kula da ni ba, iya ni kadai nace amma yace babu se gashi be rasa na canja wa yar sa motar hawa ba, innalillahi wa inna ilaihi rajiun". Hajiya Falmata ta fada tana sake rushewa da kuka, hatta da Hajiya Farida hawaye take yi na tausayin kawar ta, aminiyar ta kuma yar uwar ta "Mata sune matsalar mata yan uwan su Falmata, na rantse miki da girman Allah duk abinda Alh yake miki da sanin Hauwa kuma tsarin ta ne, tun asali matar nan bata son ki kin sani ta ya zata so miki kwanciyar hankali, kai hasbunallahu wa niimal wakeel". "Farida ina ganin zan hakura da auren Alh kawai dan be da wani amfani a waje na, gara kawai in san single nake da ciwon zuciyar da Alh ke kokarin ganin ya kakaba min karfi da yaji". "Ba zaki bar mata gidan ki ba, ba zaki bar mata mijin ki ba, wallahi ba zaki je ko ina ba, kenan ma kin yi biyu babu, baki ga tsuntsu baki ga tarko inaaa, sam wallahi". "Gwara in tafi da in zauna Ina kun sar bakin ciki". "Kece kin cika sanyin rai, tuntuni na kawo miki shawarar yadda zamu yi maganin ta amma kin xayan wasu tunane tunane, ke yar uwa ta ce kuma kawata, wallahi ba zan taba yin abinda zan cutar dake d sani na ba, ki bani dama mu nuna wa Hauwa ita karamar kwaruwa ce, ita yanzu ta soma bariki lokacin da mu kuma muka riga muka maida ita gida". Shiru Falmata tayi kafin ta saki ajiyar zuciya a hankali "Ba tsoron Hauwa nake ba Farida, saidai ina tsoron Ubangiji na, ban haifa ba, ban ji dadi ba a gidan aure na sannan kuma na lalata kiyama ta Falmata?, Anya in nayi hakan ban cuci kaina ba?". Da sauri Farida ta shiga girgiza kai, "Ba zaki lalata kiyamar ki ba, ramuwar gayya zaki yi wadda tafi gayya zafi, daga lokacin da kika rama zaki ji sanyi a ranki daga nan kuma se mu tuba, amma ai kafin nan itama taji ko da rabin yadda kika ji ne". "Bazan iya ba Farida, ba zan iya lalata dan kowa ba, ba zan iya sanya mahaifiya kuka ba, ba zan iya fuskantar Ubangiji da laifin shirka ba, na hakura Farida, na barwa Allah shine ze min sakayya kan Alh da Hauwa amma ba zan iya kauce hanya saboda ita ba". "Banza tursasaki ba Falmata, ban kawo wannan shawarar dan batar dake ba sai dan sama miki salama amma tun da baki yarda ba ba za'a yi komai ba, sai dai kiyi hakuri domin zan janye jiki daga gidan ki dan ba zan iya zuwa ina ganin ki kullum kina ramewa da karewa a tsaye saboda bakin cikin wasu ba bayan kina da yadda zakiyi, zuciya ta ba zata iya hakurin ganin ki cikin matsala ba alhalin kece yar uwa mafi kusanci da ni, kiyi hakuri ba wai na janye gaba daya bane sai dai yawan zuwa zan rage, sai an jima zan kira ki in na koma gida". Da haka Hajiya Farida ta dauki jakar ta bayan ta yafa gyalen ta ta fara daga falon, babban compound ne da ya lashe motoci kusan sha biyar wanda daga nan zaka san gidan ba karamin girma gare shi ba, gate ta nufa tana tafe kama zatai bindiga saboda haushi da takaicin yar uwar ta, sanyin ta yayi wa, zuciyar ta ta fiye kyau da yawa haka hakurin ta ya wuce ka'ida. Ta dade da sanin da ita ke rayuwa a gidan matsayin kishiyar Hauwa to wallahi da tuni labari ya dade da suyawa dan ba zata dauki ko rabin rabin abinda yar uwar ta ta dauka ba, da ita ce da tuni ta takawa Hauwa birki dan ai rashin Haihuwa ai ba hauka bane da zata dinga wani iskanci, kai da ita ce da ta nunawa Hauwa itama Shegiya ce dan wallahi yadda take mata iskanci kan haihuwa ita kuma se ta lalata rayuwar yaran ta ga karshen tutiya da tinkaho, abinda take so Falmata ta goya mata baya suyi kenan amma tsarkin zuciyar ta ya hana ta hango me ita take ganowa. Tana zuwa gidan ta tayi parking tare da shiga falon ta me bala'in kyau, abu na farko da ta fara yi bayan zama shine kiran Falmata taji yaya take, Allah shaida ne tana matukar san Falmata, ta dauke ta yar uwar da suka fito kamar ciki daya ne shiyasa duk abinda ke faruwa a rayuwar falmatan yake matukar damun ta. Hankalin ta be kwanta ba se da taji lafiyar ta kalau kafin tayi shiru cikin zurfin tunani se kuma ta gyada kai cikin yarda da shawarar da ta yanke. Tana nan zaune yan matan yaranta biyu suka shigo daga islamiyya, hassana d hussaina. Har kasa suka gaishe ta tare da mata sannu da zuwa ta amsa kana suka wuce dakin su suka canjo kaya "Yaya jikin momyn?" Hassana ta tanbaya a kagauce, sanin yadda hassana ke bala'in son Falmata yasa Farida boye mata halin da take ciki "Ta sami sauki sai dai zamuje India a sake duba ta, yanzu dai kuje ku dora girki sannan ki kira yayanku kice ina neman sa". "Da toh". Husaina ta amsa kana suka shiga kitchen yin girki. D daddare kuwa se ga dan ta Safwan kamar yazo kamar yadda Hussaina ta fada masa tana kiran sa, bayan sun gama gaisawa da tambayar yaran sa da matar sa ta kawo masa batun da yasa ta kira shi. Albarka tayi ta sa masa bayan ya amsa wa kudirin ta kana ta sallame shi ya tafi bayan ta bashi tsarabar yaran tace ya kai musu.............. Ouummey 📚✍️. Ouummey 06 {5/3/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey Ouummey 06 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Six _ Tun da akayi wannan case din na janye jiki na daga mutan gidan gaba daya, ba shi Salees din ba ba ya'yan sa ba balle matar sa d dama kissar ta ke kawo ta gare ni, gaba daya na dauke musu wuta, tsakani na dashi gaisuwa, daga ita kuma se maganar d ta zama dole. Abin dariya wai kuma se hakan ya dame shi, ko da yake amfanin kan sa ne yasa ya damu dan har kwana na daina zuwa dakin sa, wannan kuma ba karar da ya kai ni bace, kudiri na ne hakan tun ranar da yace Amir baze bar daki ba saboda gidan uban sa ne yasa na sawa raina to kuwa ba zan kuma bin shi dakin sa ba, in ya matsu da son kasamcewa dani se ya biyo ni daki na. Sati biyu muna cikin wannan halin dashi, wata magana kwakkwara bata hada mu in ba wajen aiki ba dan a yadda nake hade rai duk na gan shi yasa yake shakkar yi min magana. Yau mun tashi daga aiki d wuri saboda matar ogan mu da ta haihu yasa cikin farin ciki ya sallame mu tun kan lokaci yayi, tun da na fito daga ma'aikatar nake tunanin zuwa gida wajen Ummi na sai dai ba ze yiwu in je din ba dan ban tambaye shi ba, haka nake kallon hanyar har na wuce. Ina yin parking na tattara kaya na na fito tare da rufe motar na shiga falon da sallama, Mariya da kanwar ta na zaune suna hira duk suka juyo gare ni, daga sallamar nan ban kara komai ba na wucewa ta kofa ta ina kokarin ciro mulki dan bude dakin se dai ganin kofar a bude yasa na tsaya cike da mamaki. Daga ni se Salees ne masu key din kofar, to waye ya bude min dakin?. Da dan sauri na matsa jikin window tare da daga labulen ina surveying compound din, se kuwa naga motar shi ajiye alamun ya dawo nice ban kula ba da na shigo. A hankali na saki labulen na karasa dakin na shiga da sallama ina tunanin me ke dalilin da ze kawo Salees daki na balle ma ya bude min kofa bayan bana nan, kan bed na same shi kwance yana pressing phone ya bararraje kamar gadon sa, na dan yi turus ina kallon sa wanda hakan yasa ya dago tare da aje wayar shima ya shiga bina da ido. Ganin kallon nasa ba na kare bane yasa na wuce shi cikin son basar dashi na aje kayan hannu na na rage mayafin jiki na kana na nemi cushion na zauna Ina bude fridge din gefe na na ciro bottle water me sanyi na bude da bismilla na sha, ina sauke ajiyar zuciya na aje ragowar na sake kishingida ina lumshe ido cike da gajiya, seda na dan huta kafin na tashi na shige toilet na maida kofa na rufe sannan an shiga rage kayan jiki na dan yin wanka. ★★SALEES★★ Tun da ta shigo yake bin ta da kallo cikin son ganin gudun ruwan ta, ya gaji da wannan zaman da ta tsiro tsakanin su, ya gaji da shariyar da take masa, ya gaji da ko in kula din da tayi dashi, ya gaji da komai ma dan yana bukatar kasancewa da ita, yana bukatar jin dumin jikin ya sai dai ya lura in ya biye mata to fa haka zasu cigaba da kasancewa har zuwa lokacin da shi kan sa be hango zuwan sa ba. Baki bude ya ke kallon ta ganin yadda ta shigewar ta toilet ta rufe kamar bata lura da zaman sa cikin dakin ba alhalin so biyu suna haɗa ido dashi. 'me Khadijah ke nufi dani' ya ayyana cikin ransa, koma me take nufi yana nan yana jiran ta har ta gama ko me take cikin toilet din dan ba ze dau raini da wulakanci ba, yana zaune ta wuce shi wato ga shara banza mata amfani ko, shiyasa Hajiya Iya ke cewa ta raina shi, a da be yadda ba amma a yanzu tabbas yana hango burbushin hakan. Ya dade zaune kafin ta fito daure da guntun towel din ta da be gama sauka kan kosassun cinyoyin ta ba, jikin ta dauke da abin ruwa shaidar wanka tayi, haka kuma kan ta da ta wanke shima kulle cikin wani karamin pink towel. ★★★ Tun da na fito nake jin tasirin idanun sa a jikina alamun kallo na yake sedai ban nuna na fahimta ba na wuce na zauna kan stool din mirror, a hankali na warware towel din kaina hakan yasa jikakken gashi na ya kwanta kan kafada ta, hand dryer na jona na shiga busar da kan a nutse har na gama kana na shiga shafa mayukan da nake amfani dasu wa gashin, take ya shiga kyalli haka kuma ya sake kwanciya sosai a kafaduna bayan na taje, ribbon me dan tudu kadan na sa na kama shi sannan na kitse jelar na sake ta ta na reto a keyana. Mai na dauko tare da murzawa a hannu na na shiga bin cinyoyi na dashi bayan na sassauta zaman towel di na, a nutse nake komai kai baka ce na san da zaman wani dan Adam a dakin ba, wani na kuma murzawa na shiga bin kafaduna, kirji zuwa ciki na a tausashe cikin raina ina yabawa taushi da santsin fata ta ko da dai ba banza ba dan kudin da nake kashe wa iya mayuka da shower gel ba kadan bane. Dagowar da zan yi ba kalli mirror se kawai na ci karo da jajayen idanun Salees a kai na, da mamaki nake kallon yadda ya tsaya bayana daf yana sauke ajiyar zuciya da nishi kamar wanda yayi tsere, dauke kai nayi na fara kokarin mikewa sai dai yadda ya sake matse min waje tare da zuba hannayen sa kan kafada na yasa dole na cigaba da zama. Lotion dina ya zuba cikin hannun sa da ya dauke kan jikina bayan ya matse min waje ta yadda ba zan motsa ba, bin shi na dinga yi da kallo cikin mamakin me ze yi da man da yake murzawa a tafin hannun sa, na dan fito da ido waje jin ya sauke hannuwan kan bayana ya shiga shafa min cikin wani irin salo da yanayi me tafiyar da mutuwa, ban san sanda na lumshe ido ba sedai ban fasa dakatar dashi ba ta hanyar rike hannun sa kana na bude ido na zube su kan fuskar sa dashi ma ni yake kallo "Na shafa ai". Na fada ina kubcewa da sauri na nufi wardrobe di na cikin kokarin dauko kaya, hannuwan sa yasa a kugu na ya zagaye ni dashi tare da hade ni da jikin sa yana magana kasa kasa "Aje dauko kayan nan kizo muyi magana". "Magana? Ai yanzu ma ita muke yi". "Maganar na da matukar muhimmancin da nake bukatar nutsuwar ki, muje ki zauna ki saurare ni". "Ba zan iya zama tsirara ba, ka jira na saka kaya tukuna". Da alama ya fuskanci yadda nake kokarin hade rai shiyasa ya sake ni ya dan koma gefe, doguwar riga na dauko ta wani yadi me kyau da sulbi na zura, ba kadan ba rigar tayi min kyau haka naji dadin saukewa cikin ta dan bubu ce, hulan da ya hau da rigar na dauko tare da sawa a kaina na kara sa gaban mirror ina sake daidaita mata zama kana na shafa turaren kaya haka na kara da na feshi bayan wanda na shafa wa jikina tun farko. Waya ta na dauka tare da zama kan cushion na shiga kokarin kunna data sedai ban kai ga haka ba na ji an zare ta, nasan ba kowa bane se Salees, ya zauna kasan ƙafafuwa na tare da zuba hannayen sa kan cinyoyi na "Dago ki kalle ni Khadijah". Ban ki ba na dago kaina a hankali tare da sauke duba na kan fuskar sa, ya langwabe kai tare da karyar dashi gefe kamar wani Maraya, idanun sa sun yi jajir, in ba gizo idanu na ke min ba se n aga har ya dan fada dan kwarmin idanun sa sun nuna rama, take naji zuciya ta ta karye, tausayi hade da son miji na suka rufe ni "Khadijah bani da Lafiya". Ya fada yana kama hannu na ya kai wuyan sa, tabbas bashi da lafiya dan zazzaɓi ne ma a jikin sa "Ban san me nayi miki ba kike fushi dani Deejah bayan kin dade da sanin fushin ki ba karamin illa yake yiwa zuciya ta da jiki na ba, kin saka zuciya ta cikin rudu da halin ko in kulan da kike min". Yayi shiru tare da kallo na, nima kallon sa kawai nake ba ni da alamun yin magana sedai zantukan sa na shiga ta yadda ya kamata dan wani irin sanyi na ji jiki na yayi wanda na san hakan Salees ya karanta yasa ya matso sosai tare da shige min "A da ba zan iya kwatanta girman soyayya da kaunar da Khadijah ke yi wa Salees ba, soyayyar da tasa take hakuri da duk wanda ke tare dashi dan kawai tayi rayuwa dashi, soyayyar da ta kasa boyuwa har a gaban iyaye da jama'ar da ke kewaye dasu, haka shima Salees yake mutuwar san Khadijah, yake yin komai dan farin cikin ta har wasu ke ganin an mallake shi ne bayan tsantsan kauna ce kawai ke aiki, shin Salees yayi wa khadeejah laifi ne da yasa ta daina ko take kokarin daina son sa alhalin shi a yanzu ne yake kan ganiyar so da kaunar ta?". Wani irin laushi da rauni zuciya ta tayi a lokacin, kai wallahi maza sun iya dadin baki ta yadda zaki yi abu se bayan kin aikata ki dinga tunanin taya ya kika yi, me ya kai ki, wanda ko gobe se kin kuma yi in baki jajirce kin kai zuciyar ki nesa ba. Idanunsa da suka cika da hawaye na dago na kalli Salees, soyayyar sa ta cika min rai, na far kokarin bude baki na dan shaida masa ban dena son sa ba, ban bar kaunar sa ba haka kuma zan cigaba da hakuri dan kawai in yi rayuwa dashi, sedai kamar wadda aka dannawa pause haka na tsaya ina kallon sa na kasa fada, ba komai yasa hakan ba face abubuwan da ya dinga aika ta min a kwanakin baya, irin bakin ciki da bacin ran da ya kun sa min, wai har a gabana yake fadawa kishiya y fara gajiya da hali na, meaning ya fara gajiya dani, wanda a da be san da halin nawa bane ya so ni da a yanzu ze ce wai hali na, kawai nice ya gaji dani yake neman wulkantawa shine kuma yanzu ze dauko wasu shanyayyun kadafun sa ya zo yana karanta min karya. Eh karya mana a yanzu, na san a da Salees ya so ni Kamar yadda ya fada, nima kuma nayi haukan son sa, sedai ko rantsewa nayi ba zan kaffara ba a yanzu baya min ko da rabin rabin son da yayi min a da, akwai dai abinda yake bukata daga gare ni, akwai abinda yake so nayi masa ko yake nema a waje na shine bari ya yaudare ni da kalmar soyayya. Murmushi na saki bayan na gama kallon idon sa, se yanzu na gane me ya kawo shi daki na, se yanzu na fahimci soyayyar d yake fada yana min, ni dama nayi mamakin wai Salees ke fada min kalaman soyayya haka abinda in ban mance ba rabon da in ji irin wannan kalaman a bakin shi tun bayan haihuwar Sahal shekara goma sha biyu kenan yanzu. Be yi tsammani ba be yi tunani be se ji yayi nq ture shi daga gare ni na dauki waya ta nayi waje a hanzarce dan bani da lokacin zama magana dashi, ban shirya hakan ba tukuna dan wallahi alkawari nayi se na rama ko da kashi daya ne cikin kashi darin bacin ran da yasa ni. ★★SALEES★★ Ido ya zuba mata yana sake kankance ido cikin son tabbatar mata eh da gaske yake yanzu ya fara son ta ma, ganin yadda itama take kallon sa yasa zuciyar sa ta shiga tsalle a kirjin sa yana addu'ar Allah yasa ta yadda da abin da ya fada mata dan ya kai makura wajen san kasancewa da ita. Ba karya ya fada ba har yanzu yana son ta yana kaunar ta, sedai wasu halaye da ta ara ta yafa wanda be san ta dasu ba yasa yake yi mata abinda ya ga dama don ba zata bata masa rai a banza ita tayi farin ciki ba, be san wake koya mata bakin hali ba da yasa har take tsanar masa yaya da kuma neman ta ringa tsallake umarnin sa wanda shi kuma baze dauki haka ba. Be aje ya'yan sa a kusa ba a ran sa, sune abu mafi soyuwa gare shi so baze lamunci yaji ko ya ga tana musu wani abu na rashin kyautawa ya kau da kai ba, haka Mariya, tana iya kokarinta wajen ganin sun zauna lafiya amma Khadijah taki bada dama bayan da farko ita ta nuna ba abinda take nema daga Mariyar face zaman lafiya se gashi ta tankwabe rokon ta da kan ta, amma ban da wannan abubuwan yana son matar sa, Khadijah ce macen da ya fara so haka kuma macen da ya fara kasancewa da ya ke kuma samun gamsuwa wajen ta fiye da kowa, ta ya ya baze so ta ba?. Yana cikin tunanin yaji ta ingiza shi gefe tare da ficewa daga dakin da sauri, a rikice ya mike ze bi bayan ta se kuma ya tuna da Mariya da kanwar ta dake zaune a falon, dole ya tsaya ya koma dakin ya shiga kai da kawo ransa yayi mummunan ɓaci da abin da tayi masa...................... Not edited ❎ Ouummey 📚✍️. Ouummey 07 {5/5/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________                 _Free Chapter Seven_ Ban tsaya a falo ba na wuce garden din mu dake can bayan gidan, ba wani babban waje bane sedai gwargwado yayi kyau, kan elephant grass din wajen na kwanta abina ina sauri numfashi, kalaman Salees na sake dawo min cikin rai na, lallai Salees ma, yanzu shi after all that happened har yana da karfin halin nufin na da bukatar da, ko da yake ba abin mamaki bane. Amma fa ba karamin juriya da karfin hali nayi ba wajen ture kalaman sa daga raina haka kuma ba karamin kokari nayi ba wajen ganin be yi galaba a kai na ba, dan da gaske zuciya ta ta raunana, so da kaunar sa sun rufe ni. Ko yanzu ma da nake kwance tunanin rayuwar mu ta baya nake yi, haduwar mu, soyayyar da muka zuba zuwa rayuwar auren mu me cike da farin ciki kafin Mariya ta shigo cikin mu kuma komai ya canja. Ajiyar zuciya na sauke jin mutum a jiki na da na tabbatar Salees ne, nima dama ban yi zaton ya bar ni haka da wuri ba dan yana cikin maza masu naci kan abinda yake so, sedai na kudire ko yafi antaru taurin kai da naci wallahi baze sami komai daga gare ni ba. Da sauri na mirgina jin hannun sa ta cikin riga ta, tunkurkur na zauna tare da zuba masa idanu na da mayen son sa suka sa yayi ja lokaci guda ina bata rai matuka, cike da basarwa irin tasa ya nuna kamar be gani ba ya matso tare da son sake shige min sedai tuni nayi baya da sauri Ina turo baki "Bana son irin abinda kake min wallahi, baka na dawo nan bane, ya kamata ka gane hutawa nake son yi". Dan tsai yayi yana duba na da mamaki dan zan iya cewa ban taba yi masa gardama ga bukatar sa ba cikin rayuwar da muka yi ya tsawon shekaru goma sha shida, na san dole abin ya dake shi gashi kuma nayi fuska abina tare da komawa na kwanta na bashi baya. Sosai jikin Salees yayi sanyi sedai he's the type that doesn't give up easily so se ya Kuma matsowa tare da sa hannu ya juyo dani ta karfi, be kuma jira komai ba ya danne ni cikin son se ya hade bakin mu guri daya, aikuwa kamar me haka na shiga fighting din shi na kuma ki bashi duk damar da yake so, ya zata abin wasa ne ya shiga kokarin kashe min jiki sedai ya ga ko kadan ban da niyyar saduda asali ma na kara kai mi ne wajen kokawa dashi dole ya hakura ya daga ni tare da tsura min jajayen idanun sa da ke cike da neman magana ga kuma bacin ran da na tusa masa, yana daga ni na tashi ina gyara riga ta na mike tsaye tare da kakkabe jikina nayi hanyar barin garden din ina karkada masa jiki, ko banza na san shima na bata masa kamar yadda yake bata min. ★★SALEES★★ Duk yadda yake tunanin iskancin khadeejah ya wuce wajen, kalli yanzu abin da tayi masa kamar wani kwarto alhalin yana matsayin mijin ta shugaban ta, a yanzu kam dari bisa dari ya yarda raini ne tsagwaron sa tsakanin sa da Khadijah, ta raina shi ne take masa haka, ai da datake ganin girma da kimar sa musu wannan ze iya kirga so nawa ta masa, lallai se ya dau kwakkwaran mataki kan ta, ba dai jikin ta bane take masa wulakanci dan ya bukata?, To ta rike abin ta ta jika tasha dan alkawari ne baze kuma neman ta ba, in kuwa ta kawo kan ta lokacin zata san ita bata iya wulakanci ba dan se ya nuna mata shima tantiri ne kamar ta, yana ji da fiye da duk abinda take ji. Ya dade zaune a wajen kafin ya iya mikewa ya koma gida, fita ya so yi ko yaji sauƙin bacin ran sa sedai baze iya ba, a yadda marar sa ke damun sa cikin ma da kyar yake taka kafa. Ganin yadda ya wuce su rai bace fuska hade yasa Mariya tashi ta bi bayan sa da sauri, sedai ko kafin ta kai gare shi tuni ya shige tare da datse kofar, turus ta tsaya tana kallon kofar dan this is unlike him, bugawa ta shiga yi hankali tashe sedai duk iya bugun ta yayi mata banza ko uhm bece ba haka ne bude kofar ba har ta gaji ta juya jiki a mace ta sauka kasa. Shi kam Salees duk bugun da take yi yana ji kuma yana sane yayi mata banza, abinda bata sani ba dan ita ya rufe kofar dan ya san se ta zo takura masa shi kuma baya bukatar takurar ta dan ba abinda zata iya yi masa, khadeejah ce kawai maganin sa ita kuma ya fahimci hayaki kan ta keyi amma yayi alƙawarin sauke mata duk ma uban dake kan. Haka ya cigaba da juyi dafe da marar sa se uban gumi yake haɗawa kafin wani wahalallen bacci yayi gaba dashi me cike da mafarkin Khadijah kala kala. Be tashi ba se after Six, a gurguje yayi wanka ya fita Masallaci jikin sa duk ba kwari, sallar ma ranar cikin wasi wasi yayi ta dan gaba daya hankalin sa na kan Khadijah, tunane tunane kawai yake yi a kan ya, wata zuciyar na fada masa ya sake gwada ta ko zai dace wata kuwa na bashi shawarar fita harkar ta har ta gane kuren ta, be bar masallacin ba se da yayi isha kana ya nufo gidan cike da karbar shawarar zuciyar shi ta sake bata dama. ★★★★ Fadawa nayi kan bed fuska ta cike da murmushi me fadi wanda na manta rabo na da irin shi, wato yau da naga Salees cikin irin yanayin da na kan shiga a dalilin da se naji raina yayi sanyi, sanyi fa sosai dan ba karya naji dadi wallahi. Juyi nayi tayi ni kadai ina sake shirya yadda zan cigaba da zama da kowa na gidan da halin sa, na daina daukar cin kashin kowa tun da ina hakuri amma ba'a san ina yi ba, da ace duk abinda ke faruwa Salees na bin bayana in Ina da gaskiya da maybe ban sare ba haka, amma babu ruwan sa dani, babu ruwan sa da zan damu ko zuba cutu, shi dai duk abinda aka tsara masa shi yake hawa, duk abinda aka fada masa a kaina se ya yadda, nayi ban yi ba duk ba ze bin cika ba, kamar ba shine a baya yake fada min ba wanda ya kai shi sani na ba, ba wanda ya kai shi sanin hali na, ba wanda ya kai shi sanin abin da zan aikata ko ba zan aikata ba, duk ya manta wannan, duk ya zubar da komai ya watsar da komai, baya kallo na a komai face Khadijah, matar da yake aure wadda bata haihu ba, ba'a ma maganar soyayya, dan yanzu ina tantama in akwai so na a ran sa, dan abinda yake min masoyin gaskiya baze yi shi ba. Kiran sallah ya sa na mike tare da shiga toilet na dauro alwala na tada sallah, ina idar wa na yi azkhars dina kana na cire hijab din na fita zuwa kitchen dan yunwa nake ji, noodles na dafa na zauna na ci acan kana na wanke plate din na aje na koma daki, system na jawo na shiga aiki na dan yanzu na sake maida hankali dan bana san abin d zesa suna na ya fita daga cikin masu samun promotion din nan, na saka rai sosai ina kuma fatan Allah ya sa na dace. Karfe tara na tattara komai na aje na shiga wanka, sleeping dress na saka kana na feshe jiki na da turarukana masu sanyin dadi wanda ko ba zan je dakin Salees ba bana fashin sa su, se da nayi addu'a sannan na kwanta bayan na kulle kofa ta. Har bacci ya fara dauka ta na ji kamar an bude dakin an shigo, a tsorace na mika hannu na kunna wuta dan switch din na daga saman kai na ne, a boye na sauke ajiyar zuciya ganin Salees sedai a fili se na bata fuska in bin shi da kallon mamaki da kuma gajiya da ganin sa, maida kofan yayi ya rufe tare da takowa ya zauna bakin gado yana kallo na nikuwa na kau da kai gefe ina bata rai. "Tashi zaune muyi magana". Kamar ba zan tashi ba se kuma na fara tashin a hankali kamar me ciwon laka wanda ina sane nayi dan na bata masa dan tuni na dade da sanin baya san jira a rayuwar sa, kusan minti biyu kafin na zauna sosai sannan na kai kai gefe. "Bana san tashin hankali Khadijah, ki fuskance ni mu sami fahimtar juna". Juyo da kaina nayi na zuba masa ido kamar yadda ya bukata, seda ya dan yi shiru alamun yana tunanin ta ina ze fara kafin ya riko hannaye na, na kalli hannun sannan na maida duba na kan sa "Bana san irin wannan zaman da muke yi Khadijah, ban taba tsara hakan tsakani na dake ba, in laifi nayi miki ki fada min na baki hakuri a wuce wajen amma bana san gaba da fushi". Shiru nayi kawai, lallai namiji bai da kunya, wai ni Salees ke tambaya in laifi yayi min saboda yanzu tashi ta kawo shi, duk abinda ke faruwa be ga ni ba, duk abinda yake min ba laifi bane, aikuwa ze ga rainin hankali in dai nice dan nq shirya masa "Kiyi magana, ki fada min laifi na and we'll sort things out komai ya wuce". "Baka yi min komai ba zuma na". Zuba min ido yayi na tsayin mintina kafin ya sake matsowa kusa na har nunfashin sa na sauka kan fuska ta "No nayi miki, Ina ji a jikina nayi miki laifi, in haka ne meyasa da baki min haka ba se yanzu?, pls ki fada min me nayi miki dan iya tunani na na kasa ganowa". Murmushi nayi jin wai ya kasa gano laifin sa "Ka kwantar da hankalin ka pls, baka min komai ba ni hutu kawai nake bukata, pls ko zaka iya komawa wajen Mariya har zuwa wani dan lokaci?". Izuwa yanzu ina iya hango bacin ran d Salees ke ta kokarin boyewa sedai ko gezau ban ji komai ba a raina akasin da da ban so ko kadan in ga fushi ko damuwa tattare dashi "To kuwa baze yiwu ba, na biki na lallaba ki, na kwantar da kai na sanyayar da murya duk dan mu zauna lafiya amma kin ki bani hadin kai, zama da nine kika gaji ko kuwa wani salon wulakanci ne?". Zare hannyeye na nayi daga nasa na koma na kwanta ina bashi amsa "Babu ko daya cikin biyu kawai dai kamar yadda na fada maka ne ina bukatar hutu, Allah ya bamu alkhairi, pls in zaka fita ka kashe min wutar ka kuma rufe min dakin". Daga haka na ja bargo na lullube ƙafafuwa na tare da kulle ido na, tabdi bala'i ni kaina na san na tsokana masifa sedai sanin na shirya mata yasa nayi banza da duk bala'in da Salees ke yi "Kar ki maida ni wani shashasha mana, bar ganin ina bin ki ina lallaba ki amfada miki tsoranki nake ji, ko kuwa kin fi karfi na ne, to wallahi kyale ki nake yi kawai darajar su Abba, amma ban da haka ke in ance kiyiwa Salees iskanci ba zaki fara ba, wacece ke da za'a dinga bin ki kina wani daukan kai, ban da ma kin kasance butulu duk rufin asirin da nayi kiki baki gani ba, duk suturar da nayi miki amma nine zan zama abin wulakancin ki, to bar ganin ana wani cewa kin raina ni kin mallake ni, wannan duk karya ne dan ba macen da ta isa ta raina ni, ba'a haife ta ba wallahi dan kuwa se ta koma gidan gyatumi tun da babu abinda ya zama dole, kuma wallahi tun muna shaida juna maza ki koma hayyacin ki kafin mu kai ga yin batacciya dan akan haka wallahi komai ze iya faruwa, in nace komai ina nufin komai". Ya sa kai ya fice tare da banging min door din, duk da cikin fadan nasa akwai kalaman da suka zafafa min amma se ban bari sun yi tasiri a raina ba, mafi aala shine na bata masa rai wanda shine aiming dina kuma na ci riba dan haka se na tashi na maida kofa ta na rufe tare da kashe wuta na koma na kwanta tare da rufe ido bayan nayi addu'a, aikuwa ba jimawa bacci yayi awon gaba dani. Washegari tun bakwai saura na fice dan bani ce da girki ba bana kuma bukatar abin karin su, a office na hada tea da heater na dan ina da komai na bukata, na karya a nutse hankali kwance sannan na shiga aiki na raina fes. Karfe tara daidai na kwaso takardu zuwa cikin hall din da zamu yi meeting din ma'aikata gaba daya, a nan naga Salees sedai kallo daya yamin ya dauke kai ni ma kuma ban kuma kallon sa ba muka shiga abin da ya kawo mu, muna gamawa na koma office dina, karfe biyu nayi na tashi aiki, yau kam ban iya dauke ido daga hanyar gidan mu ba duk da zuciya ta na fada min kar nayi amma wata bangaren na tunzura ni kan naje dan ko na tambayi Salees baze bari ni ba, tun bayan auren Mariya ya dauki wata banzar akidar kulle ya ɗorawa kan sa, har gwara ma ni ina zuwa aiki ita Mariya ba inda take zuwa se ta rufe watanni shida bata fita a gida ba, sauƙin ta yana kai wa iyayen ta ya'yan ita ce dai se sanda ya so sannan ze kai ta da dare, nima haka se dare yake bari na zuwa gida ko ya kai ni, daga baya ne nake takura masa in wuce daga wajen aiki shima ba ko yaushe yake yadda ba. Ajiyar zuciya na sauke bayan na gama daidaita parking a compound din gidan mu kana cike da matsanancin kewa nake bin ko ina da ido ganin an sake gyara shi yayi kyau fiye da da, gwanin sha'awa ko ina ya sha sabon paint ga kuma shuke shuke masu daukan hankali, ba karamin kokari su yayan mu ke yi ba akan gidan mu shiyasa kullum cikin sa albarkar Abba da Ummi suke, gidan mu babban gida ne tun a da dan Abban mu na cikin masu kudin unguwar mu, compound din gidan mu babbane dan yana daukar motoci sama da biyar, a takaice dai ze dauki mota bakwai ko takwas batare da takura ba, sassa uku ne a gidan mu, bangaren samari wanda yanzu duk sun yi aure, bangaren Abban mu se part din Ummin mu inda a nan muka rayu ni da yayata salima. A hankali na bude kofa na fito me gadi ya washe baki yana min sannu da zuwa haka ma sauran ma'aikatan mu, na amsa a mutumce muka gaisa kana na nufi main falo din mu....................... Ouummey 📚✍️ Ouummey 08 {5/6/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey Ouummey 08 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Eight _ A hankali na tura kofar na shiga baki na dauke da sallama, Muryar Ummi da ta amsa min yasa na san tana zaune a falon so ina cire takalmi na na shige gaba daya na cike da dokin ganin ta, aikuwa da gudu na karasa na fada kan ta ina dariya "Kai kai kai, kayar dani kike son yi Khadijah, irin wannan fadowa ai se ki karya ni, wai ke bama ki san kin girma bane?" Ummi ta fada cikin dariya itama tana rike ni a jikin ta, gyarawa nayi na zauna kusa da ita kamar zan koma cikin ta na kwantar da kaina kan kafadar ta ina fadin "Nayi kewar ki ne sosai Ummi na, wata uku fa rabon da nazo naga Ummi na ai nayi kokari". "Ba wani kokari, mu da ada mace se tayi shekara bata je gida ba in ba wani abun ne ya faru ba". Zaro ido nayi, shekara, lallai "Tab wallahi ba zan iya shekara banzo gida ba, waiiii". Hararata Ummi tayi "To in ba'a barki ba ya zaki yi ai dole ki zauna". "Ai ko daga wajen aiki ne se na biyo, yanzu haka fa Salees be san zan zo nan ba, kawai na kasa daurewa ne na biyo". Ban san abinda ya kaini da shegen surutu na na fadi haka gaban Ummi ba bayan na san halin ta, aikuwa ture kai na tayi da sauri daga jikin ta lamarin da yasa gaba na ya fadi ga kuma amon muryar ta cikin ban umarnin in juyo gare ta cikin tune me shaida sam babu wasa a tattare da ita. Matsawa nayi daga kusa da ita da dan sauri kadan dan Ummin mu na da saurin hannu wataran duk da bata fiye yi min ba amma ina shakkar bacin ran ta "Kika ce ba da sanin mijin ki kika zo nan ba?". Yadda nake raba ido a wajen zaka dauka kisan kai nayi dan Ummin mu bata wasa da yaro akan gaskiya, duk shirin da kuke da son da take nuna maka baze hana ta rikide ba a take. "Uhm ko na tambaye shi baze bar ni bane Ummi". "Okay se hakan ya zama excuse din da zakiyi satar fita?, Saboda kina takamar kina aiki ko?, Ita yar uwar ki ba haka take zaune ba, ko kuwa kin fita iya son gida da iyaye ne?". Da sauri na girgiza kai alamun a'a kana murya na rawa na shiga bata hakuri, aikuwa na sha fada kafin ta hakuran sannan ta ɗora da nasiha kan biyayya da hakuri cikin zamantakewar aure. "Ummi wallahi na gaji da zaman gidan nan, jiya zuwa yau ne fa kawai nayi farin ciki amma kusan kullum cikin damuwa da bacin rai nake". Shiru Ummi tayi bata ce komai ba se tsura min ido da tayi, ban so na fada mata ba dan nasan zata damu amma waye nake dashi bayan ita, uwa tafi kowa fahimta da kuma sauraren ya'yan ta haka kuma cikin hikima da basira zata kwantar musu da hankali, duk da mun yi magana da Abba har naji sauki sedai ba kamar Ummi ba dan Abba da yace ze kira ni da safe be kira ba, nasan kuma ba komai yake gudu ba face ji na cikin tashin hankali, sedai nasan da Ummi ce wallahi se ta kira ni, ba kira ba kiraye kiraye ma dan uwa daban ce, ina son iyaye na duka amma matsalar mace a gidan aure yar uwar ta mace ce kawai zata fahimta. "Akwai abinda ke faruwa wanda ya kamata na sani ne Dijeh?" Seda na sauke ajiyar zuciya kafin na shiga bayyana mata halin da nake ciki, sedai dole na boye wasu abubuwan dan nasan ze sa Ummi taji haushin Salees sosai wanda maybe har mu shirya ita tana kallon shi da abin, ba kuma wai Ummi bace kadai haka duka iyaye suke so pls yan uwa mu dinga sanin iya abinda zamu fada a gidan iyayen mu. "Ki kara hakuri khadeejah, ina da tabbacin Allah baze bar rayuwar ki haka ba insha Allah, ki cigaba da kau da kai akan shi da matar shi da ƴaƴan shi, ban da daukar hudubar banza duk da nasan ba kawaye ke gare ki ba, amma zuciya ma na iya kai mutum ta baro, ki rike addu'a da karatun Kur'ani, komai yayi zafi maganin sa Allah, nima ina ta taya ki kullum, insha Allah Allah zai dube ki da duk ma masu iri matsalar ki". "Ameen Ummi na Nagode sosai". "Se kuma batun gudun mijin ki, kar in kuma jin wannan shashancin a wajen ki, ban sani ba ko sakarcin autanci ke damun ki, wataran in kika yi wani abin kamar in zane ki, nasan kin sani amma bari na tuna miki duk randa kika bijirewa bukatar mijin ki zaki kwana ne Mala'iku na tsine miki in har baki roki gafarar sa ba, dan haka umarni ne na baki in kin koma kije ki bashi hakuri kuma ban yarda ki bar shi ba har se kin tabbatar ya hakura, ban da wautar ki khadeejah ai ita mace zata iya kwatowa kan ta daraja cikin ruwan sanyi batare da tashin hankali ta hanyar irin haukan da kika yi ba, ga kuma kishiya a kusa dake da take jiran kowace dama dan sake karbe miki miji amma baki lura ba". Haka Ummi tayi ta min nasiha tare da karin tips din kula da miji iri iri, kar kuyi mamaki dan dama ni bani da kawaye, Ummi ce kawata ita da salima haka kuma itace uwata, wajen shawara ta bani wajen gyara tayi min wajen fada ma duka haka. Kayan gyara masu kyau da inganci ta hado min na karba cike da godiya dan Ummi tsohuwar likita ce, komai zata yi tana yin wanda tasan baze zama illa ga lafiya ba, shiyasa tun muna gida ta ɗora mu kan akidar fruit dan tace babu abinda ya kai shi amfani jikin ya mace shiyasa har yanzu ya bi jikina kullum se na sha shi kafin na kwanta. A sanyaye na ke tuki dan fa Ummi bata bar ni na wani zauna ba, kwata kwata ko minti talatin ban rufa ba ta kore ni da tsattsauran gargadi, kalaman ta nake tariyowa lokacin da ta rako ni compound "Ita mace nasarar rayuwar ta shine gidan miji Khadijah, nasan bakya jin dadin zaman sedai hakuri zaki yi dan bake kadai ke irin wannan situation din ba, bar ganin taki Kaddarar wallahi da za kiji ta wata se kin ji taki shafar mai ne, se kin ji ke taki ba komai bane compared to ta wata, so ki godewa Allah da niimar da yayi miki ki rike ta hannu bibbiyu ki cigaba da hakuri, masu irin Kaddarar ki da yawan su wasu na gidan iyayen su, ba dan komai ba se dan sun kasa hakuri, ko kuwa an kasa hakuri dasu, ke kuwa kin yi hakuri wanda shine ya zaunar dake har yanzu, haka shima Salees ya yi hakurin da ba kowane namiji ze iya ba saboda abin yayi masa yawa, ga iyayen sa da yan uwan sa basa son ki, ga Kaddarar ki sannan kuma kema se ki basu gudunmawa wajen kai shi bango har se an zo an yi batacciya Khadijah?, Ko kuwa kin daina san Salisun kin ne?". Nayi dariya tuno yadda ta karasa cikin zolaya, na sauke numfashi ina yin alkawarin cigaba da hakuri da kau da kai insha Allah ko dan Ummi na, na lura bata san duk abinda ze raba ni da aurena, a ganin ta maybe ba wanda ze yarda ya aure ni bayan yasan bana haihuwa shiyasa take ta kara min kwarin gwiwa da tausa ta dan na rayu gidan Salees. Da wannan tunanin na karasa gida na kashe motar tare da fita zuwa gida, a falo na same su gaba daya Salees har ya dawo, cikin murmushi na masa barka da gida na wuce ban kalli Mariya ba. Ina shiga shima ya shiga dakin, ban kalle shi ba na shiga cire kayan jiki na har na gama na daura towel, ta bayan sa na zagaya na rufe kofar da ya bar mana a buɗe sannan na karasa gaban sa na zuba masa narkakkun idona wanda na shanye shi ina langwabar da kai gefe, lamarin da yasa Salees kasa cewa komai ya shiga kallo na kawai "Wanka zumaaa naaaa". Na fada a narke cikin wani salon murya, ban yi wata wata ba na ja hannun sa zuwa bathroom dina, tare mukai wankan ina bada hakuri a aikace, ko da muka fito tuni na ruda Salees ta yarda ya kasa jurewa bare daure alkawarin sa ya shiga min wani salo ne rikita ƙwaƙwalwa nima kuma ban yi kasa a gwiwa ba na taya shi yadda yake so har ma fiye, bayan mun sake wanka kan gado na fada dan na gaji matuka gaya, shima bed din ya biyo ni tare da daga ni gaba daya ya dora kan chest din shi ya na shafa gashi na dana busar, duk shiru muka yi se sautin bugun zuciyar juna da muke ji kafin a hankali na ji muryar Salees di na "Nagode sosai khadeejah, Nagode matata, Allah yayi miki albarka". Murya ta na rawa na amsa da Ameen dan ba abinda ya fado min rai se shekarun baya da muka wanzar da tsantsan so da kauna a zaman mu, haka Salees ke min wannan godiyar duk lokacin da ya samu nutsuwa dani. "Na san ni me laifi ne, na san ina bata miki sedai wallahi kin ji na rantse khadeejah ban san me nake yi da yake bata ran ki ba, jiki na ne kawai yake fada min nayi laifi, dan Allah ki fada min kuskure na I promise to repent insha Allah". Shiru nayi cikin harhado laifukan Salees gare ni na shiga analysing wanne zan fada wanne zan bari dan wallahi ba zasu fadi duka ba saboda yawan su. Jin yadda yake hura min iska a kunne yasa a hankali na bude baki na "A kullum fatana da buri na be wuce karasa rayuwa ta da kai ba Salees, ban taba hasko rayuwa da wani da namijin ba bayan kai, kai na fara so kuma har yanzu kai nake so sedai abubuwa da yawa na dakatar dani a kan ka. Allah be bani haihuwa ba Salees, da siyar wa ake yi wallahi bana jin da ko shekara zan kai a gidan ka batare da da ba, da kwatowa ake yi shima ko da zan rasa raina zan fita nayi gwagwarmaya na kwato, haka kuma da soyayya ke bada haihuwa nasan da tun farkon auren mu ka bani, sedai Allah ne me badawa ga wanda yaso ya zaba ba kuma dan mu da ya hana baya san mu ba amma mutane basa fahimtar hakan, ba damuwa nayi da wasu se sun fahimta ba in har Kai da nake tare da kai ka fahimta, sedai abin da ke tayar min da hankali kai ma din kallon mara amfani kake min, kai ma din ka gaza fahimtar ba kasawa ta bace, so da yawa se in ga kamar jira na kake abu ya hada mu kayi min gorin rashin haihuwa, wannan shine babbar matsala ta a gidan nan se kuma na matar ka ya biyo baya, amma a kan ta ba zan ce maka komai ba dan duk abinda take yi Allah yana kallon ta kuma i do believe yasan yadda ze yi da ita". Shiru dakin ya dada yi na tsawon lokaci kafin Salees yayi breaking silence din "Am sorry for all my mistakes, am sorry na saki bacin ran da nayi times without number, am sorry for everything khadeejah, dan Allah kiyi hakuri and am ready to change, for good and for you khadeejah, ki fada min me kike so nayi wallahi i promise you zan yi". Abin mamaki kawai yake ban dan rabon da mu sami mutual agreement kamar haka wallahi ba zan ce ga yawan shekarun ba, abin da na rike kawai its too long, an dade sosai. "Ka ringa bincike kafin yanke hukunci, ka dinga sauraren both side kafin zaban me gaskiya, ba abinda nake bukata a wajen ka face adalci, kulawa da kuma tausaya wa, this is all I need from you Salees, dan Allah". Na hade hannaye na alamun roko hawaye na zuba a ido na, da sauri ya dora nasa kan nawa ya jimke kana cikin taushin murya ya amsa min "I promise you love, care and justice daga yanzu har zuwa ranar da numfashi ze bar gangar jiki na, insha Allah ba zan kuma yanke hukunci batare da bincike ba, insha Allah zan zama me adalci gare ku baki daya, ke kuma abu biyu nake so wajen ki dan Allah, uzuri da soyayyar ki, ina barar wannan abubuwna khadeejah". "And i promise you also". Ba muyi bacci ba seda muka cimma matsaya wa rayuwar mu, wannan daren ya shiga cikin tarihin rayuwa ta domin dai tun da muka shiga daki da shi tun dawowa ta karfe hudu da rabi Salees be sake fita ba se washegari dan hatta sallah tare muka dinga gabatarwa a daki. Tun daga wannan lokacin zance alhamdillah domin kuwa Salees ya tabbatar da alkawarin sa ko ince yana kan tabbatar wa dan haka har wata kiba nayi ta kwanciyar hankali da samun nutsuwar zuciya. ★★★FALMATA★★★ Yau ma zaune take a falon ta, sedai tun da gari ya waye take jin ta ba daidai ba, cikin ta wani irin ciwo yake mata da ya hanata zama guri daya, tun tana daurewa a daki har ta kasa ta janyo wayar ta ta shiga kiran me gidan, wayar na ringing amma ba'a dauka ba, azaba ta sa itama ta kasa daina kiran wanda a kalla ta masa miscall kusan ashirin amma no answer. Azabar ciwo da radadi yasa ta wurgar da wayar ta shiga malelekuwa kan carpet din kasan gadon, gaba daya ta fita hayyacin ta , a haka Allah ya jefo daya daga cikin masu aikin ta, cikin tashin hankali ta fice a guje dan zuwa sanar da mutan gidan halin da uwardakin ta ke ciki, sedai bata sami Alhaji ba dan baya gida, ita kuwa Hauwa da ta fada mata Allah ya sawwaka kawai tace ta dauke kai. Dole harira me aiki ta kuma kwasowa a guje ta dawo, ita ta zauna da ita sedai ta rasa me zata mata, cikin ikon Allah ta hango wayar Hajiya Falmata ta dauka hannun ta na rawa, dake tayi makaranta har zuwa secondary se ta lalubo number Hajiya Farida ta kira, shine fa ta zo, ashe maganin ta ne ya kare ga ba kudi hannun ta, dole Hajiya Farida ta tafi siyowa ita kuma harira ta taimaka wa uwardakin nata zuwa falo kafin Hajiya Faridan ta dawo.......................... Ouummey 📚✍️. Ouummey 09 {5/7/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Nine_ Babu dadewa Hajiya Farida ta dawo rike da maganin, kusa da yar uwar ta ta zauna tana mata sannu ganin yadda ta damke cikin tana runtse idanu, da sauri ta balla maganin harira ta miko bottle water ta haɗa ta kamo falmatan ta sa mata maganin a baki kana ruwan, da sauri ta hadiye tana dan jujjuya kai na ciwo. Babu dadewa ciwon ya lafa dan maganin babban magani ne haka kuma fast action shiyasa yake da tsada sosai, seda ta dawo hayyacin ta harira ta zuba mata abinci bisa umarnin Hajiya Farida ta karba ta dan ci ta aje ragowa. Ganin yadda hankalin ta ya dawo sosai yasa Farida kasa iya cigaba da rike abinda ke cikin ta "Wai haka zaki yi ta zama da ciwo a ciki sai dai ki sha magani ki kwantar dashi?, Wait taya ma aka yi yau maganin ya yanke miji?". Dan murmushin takaici Falmata tayi "To y azan yi Farida, tun da kaddara ta kenan?, D ana sake wa Alhaji magana yace wai in jira next month yanzu kam dai babu kudi wajen sa, magani kuma yace na bawa Adam kwalin ya siyo, to tun da na bashi ban ma kuma ganin sa ba". Kankance ido Farida tayi cike da mugun mamaki "In ji shi Alhajin yace ki cigaba da zama da ciwo har zuwa karshen wata?, Lallai mutumin nan ya wuce duk yadda nake zato, ke dama kin sa ran ya kawo muku maganin, wannan tambadadden dan da uwar sa ta riga ta gama poisoning mind finishing, ai na fada miki kin ki yadda, wallahi hau da za'a ce kin mutu dukkan su murna zasu yi domin dadadden burin su ne ya cika". "Kuma fa cewa nayi ko a asibitin nan ne ya biya ayi min aikin duk da akwai risk me girma amma na gaji da wahalar da nake sha Farida, wataran har na kan gwammace mutuwa saboda radadi da azabar da ni kadai na san me nake going through, ki dena ce musu tambadaddu, Allah ya shirye su su gane gaskiya ". "Uhm". Kawai Hajiya Farida tace cikin takaicin yar uwar Tata, kalli dai wahala ta gama sha ta sanadin Alhaji da ƴaƴan sa amma wai a daina ce musu tambadaddu, ita ta rasa wace irin zuciya Allah yayi wa Falmata amma komai ya kusa zuwa karshe dan ita ba zata zuba ido ba, dole ta dauki mataki ko dq da ba da sanin Falmata bane. Yin wannan tunanin yasa ta saki ranta ta shiga kwantar wa da yar uwar ta hankali kana ta tashi ta gyaggyara mata daku na inda masu aiki basa shiga mata, se daf da magriba ta yi shirin tafiya bayan ta jaddada wa Falmata cewan ko yaya taji wani ciwo ta kira ta haka kuma ta tambayi Alhaji suje su ga yan uwan su. Da toh Hajiya Falmata ta amsa mata kana suka yi sallama Farida ta wuce. Bedroom din ta ta koma ta yi wanka ta fito ta tsaya gaban mirror dan yin shirin ta sedai se ta bige da kallon kanta cikin madubin. Gaba daya tayi baki ta rame kamar ba ita ba, farar fatar ta me sheki duk ta yi duhu, kyakkyawar fuskar nan duk ta mokade saboda rama, baka ganin komai a fuskar se dogo siririn yancin ta da ya kara tsayi se kuma kodaddun idanun ta da kallo daya zaka musu ka hango rashin lafiya, damuwa, rashin nutsuwa da rashin kwanciyar hankali cikin su. Hannu tasa ta shafo wuyan ta inda kasusuwa suka bayyana kan su a wajen, ta dade ta na shafa wajen cikin tunanin tana hawaye batare da ta san tana yi ba, tsayin lokaci kafin ta farga ta share fuskan ta kana ta karasa gaban bed da ta aje kayan da zata sa ta dauka ta maida wardrobe, a yadda tayi wannan ramar sam ba zata sa kayan mu na al'ada ba dan ba kadan ba zasu bayyana ramar ta kasancewar duk an dinka su ne lokacin da take falmatan ta ba yanzu da se sunan kawai ba. Doguwar riga ta sa kirar Oman kana ta aje dankwalin a gefe ta shiga gyara kan ta wanda shima se d aya samu tangarda saboda halin da take ciki, seda ta tufke jelan sannan ta daura dankwalin kan ta, ba karamin kyau tayi ba duk da kuwa fuskar ta babu komai face kwalli da ta sawa idan ta dan ya rage kodewar da yayi. Kai daga yadda ta daura dankwalin abayar zaka san lallai a da an zuba gayu an kuma kafa dauruka ba kadan ba, ita kan ta murmushi tayi da ta kalli kanta sannan ta kwashi wayoyin ta ta fita falo. Tare da harira suka zauna dan duk cikin masu aikin ta tan matukar kaunar harira haka kuma ba matsayin me aiki take kallon ta ba, kallon yar uwa kuma karamar kanwa take mata dan ta girmewa hariran nesa ba kusa ba, hirar su suke yi suna kallo sama sama abinda yasa zuciyar Falmata dan samun nutsuwa daga tunane tunane. Yadda hankalin su ya dauku yasa har basu ji sallaman Alhajin ba balle shigowar sa seda yayi gyaran murya, da sauri harira ta tashi tayi waje ta kofar baya bayan ta gaida shi, kusa da Hajiya Falmata ya karasa ya zauna inda ita kuma ta tashi zuwa kitchen domin kawo masa ruwa. Kan karamin tray ta dauro bottle water da juice na kwali me dan sanyi kana ta hado da glass cups ta kawo gaban sa ta aje kana ta zuba ruwan ta mika masa ya karba ta kuma shiga zuba juice din. Seda ya karewa juice din kallo kafin yayi bismilla da karfi sannan yasha, ita dai tana kule dashi sedai bata bashi wani muhimmanci ba har ya shanye lemon ya aje. "Wanka zaka fara yi ko abinci zan kawo?". Da sauri kamar wanda tace zata kawowa mugun abu ya shiga kada kai "A'a, a'a ai ba zan ci abincin nan ba, na riga naci abinci a waje cikina a cike yake". Dan tsai tayi tana kare masa kallo kafin kuma ta girgiza kai tana dan murmushin da kan kallo zaka san ba na jin dadi bane "To shikenan, wankan fa?". "Yanzu zan je can part di na nayi, dama dai nace ba wata damuwa ko?" Seda ta dan hadiye miyau kan ta bashi amsa "Maganin da na bawa Adam ne dai har yanzu be kawo ba". "Se fa kina yi wa yaran nan uzuri, yana da harkoki da yawa ne, yanzu haka ya ma tafi can kudu kan kayayyakin mu da ze shigo dasu, amma kiyi min texting sunan maganin se na taho dashi". "Ko kawai ka bawa Bala ya siyo min?". Ta fada sanin in dai shi ze siyo maganin to kuwa har ta mutu be kawo ba. "Shikenan zan bashi kudin ya siyo kawai, shikenan ko?". "Maganar aikin nan alha......". Tun kafin ta karasa ya katse ta yana mikewa tsaye daga zaman da yayi "Ai tuni muka gama magana akan wannan, na fada Miki babu kudi a hannu na yanzu amma watan gaba insha Allah se ayi aikin ko a nan asibitin Shehu ne dan gaskiya fita wata ƙasa ze ci miliyoyin kudade kuma kin ga yadda yanzu harkokin suke se a hankali". Tun d aya fara maganar take kallon shi har ya kai karshe "Allah ya kara budi, gobe ina so inje gida". "Gida kuma, wane gidan kenan?". Ya fada yana bata rai kamar wadda tace masa zata je gidan karuwai ". "Gidan marayu mana, muna da wani gidan da yafi nan ne?". "Ba zaki je ba". Ya fada yana kade babbar rigar sa ya nufi fita waje "A'a Usman ka bar ni kawai dan wallahi goben nan se naje". Ta fada da rawar murya, shima Alhaji tsayawa yayi kana ya juyo cike da mamakin yau Falmata ke ja da hukuncin sa, anya be fara kure hakurin baiwar Allahn nan ba kuwa. "Shikenan kije Allah ya tsare, ki gaida su". Bata amsa masa ba ta zauna tana kallon tv sedai hawaye ke zuba a idanun ta, yana fita itama ta tashi zuwa daki da sauri, kan gadon ta ta fada tana kuka me shiga jiki, wani kuka me tafe da sheshshekar dake fitowa daga can karkashin zuciya, a hankali nunfashin ta ya fara seizing kadan kadan kafin kuma tari ya turnike ta , da sauri ta tashi daga kwancen da take tare d da finciko tissue dake aje kan mirror din ta tasa a bakin ta zuwa hancin ta dan ta ana abinda ze faru gaba. Seda tarin ya tsaya mata da kyar sannan ta zare tissuen dake kan hancin ta ta aje haka ma na bakin ta, gaba dayan su sun ɓaci da jini, wani irin bakin jini me kauri, ganin bata firgita ba yasa nasan ta dade yana ganin hakan kenan. Wata tissuen ta sa ta goge bakin ta sosai kana sa ruwa ta kuskure bakin, ta dauko wani ma ta goge hancin, take fuskan ta yayi tas kamar ba ita ta shiga yanayin ba. Kora tissues din tayi cikin closet ta karawa toilet din spray sannan ga fito, bedside drawer ta bude ta ciro wani tablet guda biyu manya ta sa a baki tare da korawa da ruwa, Wani ta dauko different from the first shima ta sha biyu sannan ta cire doguwar rigan jikin ta tasa na bacci yayi light off tare da kwanciya bayan tayi addu'a. Kashegari da wuri ta shirya, tayi matukar kyau cikin Abayan da tasa kirar Dubai, sosai ramar ta ta buya se wadda ba'a rasa gani ba, sallama tayi da su harira sannan ta fita cikin motar ta wadda bata wata me kyau bace can amma kuma ba wai ba ta da kyau bane. A compound din gidan Hajiya Farida tayi parking ta fito tana sakin murmushi, Farida ce kawai kawar ta ita ce kuma kadai yar uwar ta haka kuma aminiyar ta, gurbin da Farida ta cike mata ba kadan bane haka kuma halaccin ta gare ta me yawa ne duk da dai ita ce ta fara yiwa Faridan amma ba kowa ke iya rama alkhairi ba. Da sallama ya shiga falon, ihu Hassana ta saki tare da tashi ta nufo ta a guje, duk kai kai kai din da Hajiya Farida keyi be sa ta fasa ba se da ta fada jikin falmatan har da wani dan tsalle kafin ta kankame ta, ita ma sa hannu tayi ta sake riƙe ta a jikin ta suna dariya Farida kuwa ta soma fada "Ke dai wallahi ban san yaushe zaki yi hankali ba Hassana, ban da rashin mutunci kayar min da ita zaki yi da zaki dane min ita haka bayan kin san ba wani lafiya ne ya ishe ta ba salan ki cuce ni, to Allah ki ka kuma se ran ki ya baci, bana son shashanci, yarinya ga uwar nauyi kaman buhun shinkafa kawai ki nemi illata min yar uwa". Bata fuska Falmata tayi ganin yadda Hassana tayi rau rau da idanu, "Gaskiya ni dai Farida kina min abinda bana so, kawai shikenan se ba zata zo ga uwar ta ba saboda bani da lafiya, ko kuwa ke kadai ce me yar uwa da zaki ce haka, dan ma kin samu ana yin yar uwar ta ki, to ni dai kiji ma ya'ya na are above anyone, maza matso ki sake yi min oyoyo sweetheart ". Ta fada tana sake buɗe mata hannu bayan ta matsa nesa da ita daidai lokacin da Hussaina ta fito daga bedroom suka kuwa kwaso da gudu su duka biyun suka fada kan ta gaba daya suka zube kan kujera suna dariya, ita kam Farida bata kuma bi takan su ba ta cigaba da abinda take yi a kitchen jin yadda Falmata ta gwale ta sedai tana jiyo kyakyacin dariyar su daga nan wadda ta manta rabon da taji dariyar Falmata har haka. Wani irin tausayin ta ne ya sake kama Farida tuno yadda Falmata ke masifar son yara tun suna kanana se gashi Allah ya jarraba ta da rashin haihuwan kuma ta bata mamaki dan bata taɓa zaton Falmata zata iya karbar wannan kaddarar ba. Seda ta gama aikin ta sannan ta fito ya same su kamar wasu kawaye "Oya aje a fito da komai a shirya kan dining bari nayi wanka nima". Da haka suka tashi zuwa aikin da aka sa su ita kuma ta wuce wanka aikuwa itama Hajiya Falmata ta tashi ta shiga taya su jera abincin, tare suka yi gaba daya sannan suka wuce wanka suma ita kuma ta zauna kallon wata hira da ake yi da wani mawaki a TV. A shirye suka fito dan tare zasu tafi dukan su zuwa gidan marayu wanda nan ne gidan su Farida da Falmata kasancewar marayun da suka tashi suka budi ido a gidan batare da sanin su waye iyayen su ba, hakan yasa suka riki gidan marayun gida duk kuma wanda ke cikin gidan suka dauke su yan uwa kuma dangi, Hajiya Farida bata taɓa kunyar nuna wa ya'yan ta gidan matsayin nasu gidan iyayen ba, a kullum tana alfahari da gidan dan acewar ta ba'a yi musu rikon wulakanci ba. Seda suka karya gaba daya har Falmata sannan suka dungu ma zuwa compound suka shiga motar Hajiya Farida leaving behind motar Falmata a gidan. A motar na hirar su suke yi ita da Farida dake tuki yayinda Hassana da Hussaina ke baya suma suna tasu har suka kai gidan, kayayyakin alkhairin da suka saba bayarwa na kayan abinci duk suka dire haka kuma suka dinga zagaye gidan bangare bangare suna gaisawa da jama'a, da suka tashi tafiya wannan karon Hajiya Farida ce kawai ta bada kudi kamar yadda suka saba dan ita Falmata babu kudi hannun ta. Haka suka yi sallama da jama'a suka koma gidan Farida suka sauke yan biyu su kuma suka sake fita domin tafiya meeting din kungiyar su wadda Farida ta shiga ne kawai saboda Falmata dan kungiyar purpose din ta babu irin su Farida ciki. *NATIONAL ASSOCIATION OF INFERTILE WOMENS* Babbar kungiya ce da ta cika ta tunbatsa da Manyan mata iri iri, kungiya ce da aka kafa ta solely dan matan da basa haihuwa, zaka yi mamaki in ka ga dimbin mutanen dake ƙarƙashin kungiyar domin ta haɗa mata kala kala, manyan masu kudi masu rufin asiri kai har ma d talakawa. An kafa wannan babbar ne domin kwantar wa d matan da basa haihuwa hankali, samar musu da aikin yi da kuma kwatar musu yancin su a inda ya dace, haka kuma domin taimaka su a gurin da suke buƙatar taimako. Suna yin meeting din wannan ƙungiya ne annually ma'ana duk shekara, a nan za'a zauna a ji koken juna, me bukatar taimako ayi mata, sababbin members kuma ayi masu rigister tare da councelling kan abubuwan dake jawo rashin haihuwa, in abin me magantuwa ne suna tsayawa kai da fata har se sun ga an ci nasara da izinin Ubangiji batare da duba da ko nawa za'a kashe ba while the treatment........... Ouummey 📚✍️. Ouummey 10 {5/9/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey                        Ouummey 10 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________                   _Free Chapter Ten_ Hajiya Falmata da Hajiya Farida sanannu ne a kungiyar saboda irin gudunmawar da suke badawa, ba wai sun fi kowa taimako d kudi bane, a'a irin matsalar da Falmata ke ciki da yadda take da jarumta da juriyar mai da komai ba komai ba yasa ka bata mukami dan na kasa suyi duba izuwa ga rayuwar ta su kuma yi koyi da tawakkali hadi da karfin zuciya irin nata. Kamar ko da yaushe yau ma cikin nasara aka gama gabatar da meeting din, inda yau taimakon nasu ya karkata ne kan wata mata da ke da matsalar karin mahaifa da ya hana ta haihuwa gashi kuma mijin da iyayen ta ba masu karfi bane hakan yasa jin labarin kungiyar da irin taimakon da ake yi a cikin ta yasa ta kawo kanta haka kuma aka saurare ta duk da bata kasance wata hamshakiyar me kudi ba, ba kuma wata celebrity ba haka kuma ba wata kusar gwamnati ba, motto din kungiyar shine mu'amala da kowa with equality, babu ruwan su da mai kudi ko talaka, abinda suka sani shine they all are one family and have almost similar problem so they'll come together in finding a solution. Miliyan uku da rabi ake bukata domin aikin dan abin yayi worsting ta yarda har ya fara neman lalata mahaifar hakan yasa ake bukatar aikin urgently, wani abin burgewa shine a wannan zaman da suka yi da kowa be san za'a iya kawo matsala ba se gashi tashi daya har an hada miliyan biyu da rabi, inda wasu suka karbi bank account na kungiya domin sending kudaden wasu kuma suka tura, abinda be isa ba za'a cika a asusun kungiya. Compound din building din tuni ya cika da kayayyaki, kayan masarufi, kayan amfanin mata kama daga kan sabulai da turarukan wanka, kayan sawa, mayukan gyaran fata da gyaran gashi, takalma, kai abubuwa dai da yawa da mace zata bukata na gyara daga wajen mijin ya, ba mutum daya ne ya kawo ba, kowannen su kan zo da abinda Allah ya hore mishi ne in aka hada se a raba, suna yin hakan ne dan ragewa mata takaicin namiji da wani baze iya bada kudin gyaran jiki ko wani gyaran gashi ba, musamman ma masu irin matsalar su da mata ke kallon basu kudin gyara ko wani abu as a waste of resource. Kowanne ka kalla fuska cike da farin ciki ana wasa ana dariya suka rabu, Falmata cikin ranta bata ji dadin yadda abun ya zo mata cikin rashin kuɗi ba sai dai taji dadin yadda yar uwar ta kuma aminiyar ta Farida ta rufa mata asiri domin kuwa ashe kayan masarufi ne cike damkan a bayan motar ta bayar da sunan Falmata. Gida ta mai da ta bayan sun zagaya gari duk saboda tayi lightening mood din Falmata wadda duk abinda Farida ke yi ta na ankare haka kuma zuciyar ta cike take da matukar godiya ga Allah bisa kyautar wannan rai mafi tsananin so, kulawa hadi da tausayi gare ta, bata san me yasa ba se take jin wani matsananciyar kewar Faridan tare da ita duk da gata a gefen ta suna tare. Har bedroom Farida ta rakata, duk yadda take fada mata ita fa lafiyar ta lau bata bar ta ba se da tayi wanka ta canja kaya gaban ta ta ci abinci sannan ta kwanta kana hankalin Farida ya kwanta har ta iya ta mata sallama ta tafi nata gidan. Kallon Hassana tayi dake zazzage karamar akwatin yan kunnen ta, wani babban saiti ta dauka me hade da awarwaro, zobe, sarkar kafa da kuma zobe, jujjuya su tayi kana ta dauka ta sa a handbag din ta dake gefen ta kana ta umarce ta ta maida ragowar, cike da dimbin mamaki Hussaina ke kallon ta wanda duk Farida na hankalce amma se ta nuna kamar bata gani ba ta mike tare da nufar bedroom din ta tana umartar Hussaina da ta bi bayan yar uwar ta su kwanta se kuma gobe, haka dole ba dan taso ba Hussaina ta yi dakin su ranta cike fa mamakin me maman ta zata yi da babbar sarkar auren ta, sarkar da iya rayuwar ta zata iya fadar so nawa ta sa ta saboda son da take mata. Washegari tana tashi Falmata ta fara kira, jin ta garau yasa hankalin Farida kwanciya sannan ta gabatar da ibada ta koma baccin da bata samu yi da wuri ba saboda tunani. ★★★ A hankali na kashe datan waya ta fuska ta dauke da madaukakin farin ciki, a duk lokacin d nake kallon mutanen nan ta cikin waya ji nake kamar na budi ido na ganni cikin su, wata irin kaunar su nake ji kamar irin yan uwa na ne na kusa kusa, na san ba komai ke sa min wannan feeling din ba se dan ya kasance matsalar mu iri daya ce dasu, damuwar mu iri daya ce sedai wata tana fin wata samun kwanciyar hankali. A duk sanda nake kallon su wani irin kwanciyar hankali nake samu da nutsuwa sanin ba ni kadai Allah ya jarraba da wannan ƙaddarar ba muna da yawa haka kuma ina karuwa da shawarwari da nasihar da ake yi a karshen meeting din. A kalla shekara goma sha daya kenan da nayi joining kungiyar NATIONAL ASSOCIATION OF INFERTILE WOMENS, yaya Salima ce ta ga sunan kungiyar a facebook lokacin bata bunkasa haka ba se kuwa ta fada min tana yabon yadda suke gudanar da tsare tsaren su, aikuwa ban yi sanya ba bayan tafiyar ta nayi searching sunan kungiyar na kuma gan ta, ban gushe ba se da nayi wa daya daga cikin admins din magana privately ita ce ta fada min dukkan procedure din da zan bi wajen yin register haka kuma nayi. Takaici na daya da ya zama kungiyar tana garin Bakwarni ne ni kuma ina garin Darma ne so ba ta yadda zan dinga attending meetings din su, lokacin da aka kawo shawarar yin live vedio yayin meeting din ba karami dadi naji ba, tun daga lokacin kuma ban taba missing ko daya daga cikin meetings din ba, haka kuma sanadiyar watsapp group da kungiyar ke da mata da yawa sun kulla zumunta tsakanin su, nima akwai wata Zuhra da muke so close da ita saboda yanayin yadda naji Kaddarar ta kamar tawa har kuwa irin dangin miji da surukar da Allah ya bamu. Numfashi na sauke tare da tashi zuwa kitchen bayan nayi offing data na, yau girki na ne gashi kuma me gidan yayi tafiya se yau ze dawo shiyasa zan shiga kitchen da wuri dan sama masa abin tarba. Kusan wuni nayi cikin wajen ina aiki, dishes kala kala na hada wanda nasan miji na na so kuma ze yi farin ciki in ya gani, seda na jera komai a dining tare da yin decorating sannan na tafi daki dan yin wanka. Staright gown na saka na wani dark purple material da ya sha wani azababben dinki, ko ta ina jikin rigar stones ne sune shining suna daukan ido, yadda rigar ta kamani kam yasa na tabbatar eh nayi kiba fa dan last sawar da nayi mata bata kama ni haka ba. Light purple head nayi anfani dashi na kafa a kai na ta yadda ya zauna sosai kai kace a haka yake tun ainahi, turare kuwa kamar wadda nayi wanka dan bana iya kirga adadin turaren da nayi wa kaina feshin, kawai duk wanda naji kanshin sa ya min dadi ɗorawa nake kan na baya. Falo na dawo na zauna ina dan girgiza kafa ta tare da taunan cingum a hankali, duk wannan kwalliyan fa ba komai a face na ban da powder da kohl se mascara kawai, ba dadewa kuwa naji shigowar motar da driver ya je dauko shi, cike da madaukakin farin cikin da na kasa boyewa na tashi zuwa bakin kofa na tsaya dan na kasa tsayawa jiran sa, kwana ukun da yayi baya gida se naji tamkar mun shekara uku ne bamu ga juna ba, ni kai na wannan zumudin nawa akan Salees na bani mamaki, sedai na fi dangan ta hakan da yadda muke zaune lafiya kalau cikin kwanciyar hankali tun bayan alkawarin da yayi min wanda kusan two month kenan yanzu baya, daga Salees dai ban kuma ganin wani abin bacin rai na azo a gani ba se wanda ba'a rasa ba na yau da gobe wanda shima mostly akan ya'yan sa ne dan Allah ya jarraba Salees da mugun so da gudun zuciyar ya'ya wanda nake jiye masa wataranan da idanun su shida mahaifiyar yaran ya rufe basa hango ta. Daga wajen Hajiya Iya da yan uwan sa ne kan nake Fuskantar Matsala dan sun matsa min a kwanan nan, har gidan nan suke zuwa su ci min mutunci yadda suka so, ba yadda zan yi haka nake shanye wa nake kuma hana kai na damuwa tun da dai muna zaune lafiya dashi. Maybe ku ga rashin zuciya ta akan nacewa zaman gidan Salees sedai ba naci bane, sanin ciwon kai ne da kuma biyayyar iyaye domin a kullum Ummi na na fada min babu suturar da ta kai ta aure wajen ya mace, gidan miji shine bigire mafi daraja a wajen mace haka kuma shi mijin shine rai mafi girman biyayya, taya kuke tunanin zan biye wa zafin zuciya da bacin rai wajen yin fatali da nasihar uwar da na tabbatar tafi kowa so min kwanciyar hankali da zaman lafiya.....?. Rundunar da Salees yayi min ce ta dawo dani hayyaci na, ban yi wata wata ba nima na bude hannaye na na zagaye shi dasu cike da tsananin farin ciki da jin dadi, se kuma nayi saurin yin baya jin sautin yaran na fadin "Oyoyo Daddy, oyoyo". Se lokacin na kula tare suke da maman su, yo Ina na kula, ganin miji na ya mantar da ni kowa, daya bayan daya ya daga ya'yan suna dariya yana amsa musu sannun da suke mishi, daga karshe ya karbi Amir a hannun Mariya muka taka cikin falon gaba daya muka yi masauki kan kujerun wajen. Sannu da zuwa muka shiga sake yi masa yana amsa wa cike da walwala haka kuma muka dora da hira gaba daya wadda sa'i da lokaci Mariya ke kokarin zare ni cikin su sedai yaki bayar da kofar hakan, ko akan yan uwan ta tayi magana se ya sako ni nima kuma bana gwale shi zagawa nake na amsa shi, na kula hakan ba karamin batawa Mariya yayi ba, wanda dama tun da taga yadda muka dinke da Salees yake gudun bacin rai na kamar farkon shigowar ta cikin mu shikenan ta rasa walwala. Yanzu ma tashi tayi ta tafi daki ta kwanta wai bata jin dadi kan ta na ciwo haka kuma tana ganin jiri, sannu duk muka yi mata yaran suka bi bayan ta nikuma na wuce dakin Salees ya biyo ni dan yin wanka da kuma samun hutu. Duk yadda nake son kwalliya ta seda Salees ya bata min dan dagewa yayi tare zamu yi wanka, haka ba yadda na iya na biye masa, muna fitowa na wuce dining na kwaso abinci na kawo masa saboda yadda yake ta kiran yunwa yake ji, ashe fitowar da nayi Mariya ta gan ni, zuciyar ta ta kuma cunkushewa da bacin rai na gani na da towel kai na a jike, ita a tunanin ta wani abu ne na daban niku wa ba da gangan nayi ba kaya na ne ya jika min wajen wanka gashi kuma ya ruda ni da kiran yunwa shiyasa ba shiri na dauro towel na fito. Cikin annashuwa nake kallon sa yana cin abinci a nutse, irin yadda nake farin cikin zaman lafiyar mu wallahi ba zan iya kwatanta wa ba, ganin yadda na tsare shi da ido yasa ya dago kai ya kalle ni tare da dage min gira daya "Ya dai yan mata, irin wannan kallon haka kamar za'a cinye ni?". Murmushi nayi me fadi da yasa haƙora na bayyana "Kawai inq tunani ne". "Tunanin me kunq bayan gani a gaban ki". "Tunanin rayuwa zuma na, irin yadda muka samu kwanciyar hankali se nake jin ba abinda ya kai hakan dadi". Seda yayi dariya kafin ya kashe min ido cikin tsokana "Ke dai fadi gaskiya, kina tunanin rayuwa babu ni ne, uhm fada min". Nima dariyar nayi "To meze raba mu balle har in yi tunanin rayuwa ba kai?". "In ba rabuwa fa akwai mutuwa Khadijah, kin san wannan?". "Na sani sosai Salees sedai ina fatan Allah ya dauke ni kafin kai dan i can't imagine a life without you, beside haka kana da wasu rayukan da kai ne jigon su ba kamar ni ba da ban aje komai ba, rabuwa kuma, hmm bana zaton akwai wannan kaddarar a tsakanin mu". Aje spoon din hannun sa yayi ya zuba min ido har na gama magana kafin cikin serious tone yace "Rabuwa tsakanin mu itace zata zama mafi munin kaddara da bana fatan kasancewar ta a gaske, dan Allah kar ki kuma kawo wannan maganar a ran ki ko da kuwa a mafarki ne". Kallon sa kawai nake zuciya ta na bugawa saboda tuno wani incident da ya faru shekaru tara da suka wuce, wani irin faduwa gaba na yayi kamar a lokacin abin ya faru, irin yadda na runtse ido tare da dafe kirji yasa Salees saurin riko hannu na a rikice "Lafiya kuwa Deejah, me ya same ki?". Seda nayi dan sakwanni kafin na bude ido na kalli Salees murya ta na rawa "Shekaru tara da suka wuce, salees anya......". Da sauri ya rufe min baki yana girgiza kai kamar shima ya rude "Kar ki karasa, a wancan lokacin na sharrin zuciya ne da kuma zuga, bayin kai na bane ba Deejah, dan Allah ki daina tuna min da mafi girman kuskure na". A hankali na cire hannun sa daga baki na ina gyada masa kai alamar toh. Gaba dayan mu jikin mu yayi sanyi amma muna kokarin ganin mun danne komai mun nuna ya wuce sedai har lokacin bugun zuciya ta ya kasa sasssaitawa balle ya daidaita. ★★★ *BURAIMA QUARTERS, BAKWARNI STATE* Plate din da ta gama cin abinci dashi ta dauko zata kai kitchen, tsaya wa tayi ganin yadda yake sanda zai fice kamar wani barawo, takawa ta shiga yi har ta kai bayan sa daf sannan ta tsaya kana ta ambaci sunan sa cike da mamaki "Dada". A firgice ya juyo yana kallon ta ido waje se kuma ya sauke ajiyar zuciya tare da sa hannu a bakin sa ya mata alamar tayi shiru, seda ya kalli babban falon ya ga babu kowa sannan yaja hannun ta da sauri suka shige kitchen din ya bude kofar suka fita compound ta cikin kitchen din. Ajiyar zuciya ya sauke kana ya sake mata kyakkyawan murmushin da bacin ya'yan sa da iyayen sa ba wanda yake samun alfarmar ganin sa balle ace shi a ka yi wa. "Dada lafiya kuwa?". "Where's pretty". Ya fada da dakakkiyar muryar sa yet kuma me taushi "Tana shirya wa ne Dada, wani abu ya faru ne?". "Wa ita nake wannan sandan, bana so ta ganni dan kin san rigimar kanwar ki, da kyar tayi bacci da dare wai ita a kai ta Maamah". Ya karasa sunan in a bitter tone haka itama matashiyar take yanayin fuskar ta ya canja daga mamaki zuwa alhini da damuwa...................... Ouummey 📚✍️. Ouummey 11 { 5/10/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Eleven_ "Kaje Dada zan kula da ita, insha Allah ba zata yi rigima ba". Gyada mata kai yayi tare da pecking goshin ta ya juya ze cigaba da tafiya "Dada". Ta tsaida shi, da sauri ta karasa gare shi tare da shan gaban sa ta shiga bin shi da kallo "Baka yi bacci ba jiya ko?". Kau da kan sa yayi daga kan ta yana hadiye wani daci a ran sa jin yadda tayi magana da wani sassanyan sauti me cike da tausayawa "Dan Allah kar ka fita Dada, kaje ka sami bacci, i promise to look after Meerah and Meemah". Wani murmushin ya sake yi mata kana ya riko hannayen ta yana mata magana a hankali ransa cike da so da kaunar wannan yarinyar tasa me matukar nutsuwa, wayo, hankali da kuma fahimta "Bana tare da bacci Haanah, idanu na ne na tashi suna ciwo, take a look here". Ya fada yana zira hannu cikin aljihu ya fiddo da maganin ciwon ido, a hankali ta sauke ajiyar zuciya kana ta sake masa kyakkyawan murmushin da ya haska matashiyar fuskar ta me cike da kuruciya "Oh Dada, har hankali na ya tashi fa na zata bacci ne baka samu ba, shikenan a dawo lafiya Dada na". "Allah yasa Haanahn Dada, pls do take care of your little ones, I won't take long insha Allah ". Gyada masa kai tayi har lokacin murmushin ta na nan, da sauri yayi gaba jin wayar sa na daukan ringing, da kallo ta bi bayan baban nata me cike da tsananin tausayi hadi da kauna me yawa kafin ta juya zuwa cikin falo ta same hanyar da suka fito. A falo ta tadda Meemah da Meerah both decently dressed cikin islamiyya uniform din su, dage musu gira tayi while tana sake musu tattausan murmushi kana ta bude hannayen ta, da gudu suka karaso suka bata a huge sisterly hug ta sa hannu ta sake kai su jikin ta sosai, kusan minti biyu kafin ta sake su tana bin su da kallo inda tayi branching kan fuskar Meemah dake yatsuna fuska tana wani tura baki. Tun kafin ta kai ga tambayar ta meye Meemah ta fara magana cikin zazzakar muryar ta me cike da tsiwa "Kai gaskiya kadai ya Meerah baki iya hug ba, jibi yanda kika matse ni kamar zaki da kayan ciki na su fito ta baki na, da kyar fa nake numfashi, tabdi". Meerah da abinda Meemah ta fada ya kular tayi kan ta zata kai mata duka hakan yasa Haanah yin intervening da sauri "Me ye haka kuke yi?". "Jibi yadda take min rashin kunya Adda bayan ke da Dada kun hana ta". Wani kallo Haanah tayi wa Meemah da yasa ba shiri ta kalli Meerah "Koyi hakuri Adda Meerah ba zan sake ba amma kema ki daina matse ni gaskiya". Meerah zata sake magana Haanah ta daga mata hannu kana ta tashi tana pointing musu hanya "Oya let's have our breakfast, we're almost late". Ba musu suka yi gaba ta bi bayan su har kan dining din su dake shaƙe da kayan kari wanda a kalla mutum goma zasu ci a wadace, babban plate Haanah ta dauka ta zuba musu gaba daya chips din wajen ta aje musu gaban su ita da Meerah sannan ta haɗawa kowa tea a cup, ita kuwa Meemah farfesun hanta ta sa mata a karamin bowl ta bata bread da Egg. A nutse suka karya cikin nutsuwa babu me yin magana har suka gama kowa ya zari tissue ya goge bakin sa da hannu kana suka wanke a wash hand basin dake dining area din. "Ku dauko jakan ku muje na san Lawan na can na jira". Da toh suka amsa mata suka yi yadda tace, a tare suka fita daga falon tayi locking din sa suka wuce parking space inda suka tadda Lawan na jiran su kamar yadda tayi zato, Meerah da Haanah suka shiga baya Meerah kuma gaba, har ya tada motar zasu fita ta wani zaro ido tana fadin "Lalalala, tabdi malam Lawan tsaya tsaya". Tsayar da motar yayi yana kallon ta haka ma su Adda Haanah jira suke suji tace tayi mantuwa se suka ji tana fadi "Ban yi wa Dada sallama ba Adda, bari in maza in je". Da sauri Haanah ta dakatar da ita da fadin "Ba kya ganin mun yi late ne, ki bari mu dawo dan Dadan ma baya nan, Malam Lawan muje ko". Turo baki tayi gaba ta gyara zaman ta dan dole dan yadda taga Addan ta hade rai ta san ba ta isa ta kawo wargi ba. Har bakin kofar class ya kai su Meemah da Meerah inda Haanah ta sauka a ajin su Meemah kasancewar ta malamar su shi kuma ya juya ya tafi. Karfe biyu suka tashi daga makarantar, Meerah tazo ajin su Meemah dan a nan suke haduwa su tafi bakin makarantar inda Lawan ke tsayawa, sedai ga mamakin su yau Lawan yayi late xan kuwa be zo daukan su ba. Zama suka yi suna yan hirar su tare da kallon yaran dake fitowa daga makarantar har suka ji horn din motar da yasa su juya wa dukan su a tare dan ko a mafar ki suna iya banbance sound din wannan horn din daga na kowace mota. "Wallahi Dada ne, Dada na ne yeeeeehhh". Meemah ta fada tana kokarin rugawa da gudu zuwa wajen motar dake parke gaban su kadan "Kar ki fara yi mana gudu a nan, ki jira muje tare me rawar kan kawai". Meerah ta fada tana hararar ta, tsayawar ta yi bisa dole sedai bakin nan a tale kamar wadda zata yaga shi, jira take kawai su shiga mota ta haɗa Adda Meerah d Dada dan ta gaji da yadda take mata fada da abubuwa. Seat din gaba Haanah ta budewa Meerah ita kuma da Meemah suka shiga baya "How's the school babies". "Alhamdillah Dada". Suka fada a tare har Haanah da ta fara girma dan in a gaban Dadan ta ne jin ta take yi kamar wata yar baby. "Yauwa Dada, malamin mu yau ya fada mana ba kyau karya shiyasa zan fada maka abinda Adda Meerah tayi dazu". Da sauri Meerah ta zaro ido jin iya shegen da Meemah zata mata dan kawai ta hana ta gudu, "Kai Meemah kiji tsoron Allah ni kuwa me nayi da zaki fada in ba kalin sharri ba". Dariya Meemah tayi ganin yadda Addan tata ta firgita "Ki bari kawai na fadawa Dada da Adda Haanah kin sha ruwan sanyi immediately after you wake up". Rau rau da ido Meerah tayi tana kallon Haanah wadda itama ke kallon ta jin abinda tayi bayan likita ya hana ta kuma ta sani "Why, meyasa kike yin haka Ameerah?". Sharrr hawaye suka zubo mata dan suna bala'in tsoron baban su dan duk yadda yake wasa dasu yake son su baya hana ya hukunta mutum in yayi ba daidai ba "Am sorry Dada Allah ba zan kuma ba". Shiru yayi mata hakan yasa ta kara volume din kukan ta tana bashi hakuri "Will you pls keep shut, ko baki ga tuki yake ba?". Kamar an yi ruwa an dauke haka ta hadiye kukan ta bayan Haanah ta mata magana, ba wanda ya kuma magana se Meemah dake wasan ta ita kadai har suka kai gida, kowa ya dauki bag din sa suka yi falo. A tsakiyar falon ya tsaya ya zuba wa Meerah ido cikin hukuntata dasu wanda duk yayi musu irin haka suke gwammace wa yayi fada ko ma duka akan wannan silent punishment din. "Ciki na ne naji yana zafi Dada shine nasha amma ba zan kuma ba, am so sorry pls Dada". Kallon Haanah yayi se ta langwabar masa da kai alamun itama tana bashi hakuri, dauke kai yayi ya kalli me kawo gulmar Hajiya Meemah, wai dan gulma itama yarinyar nan se ta karyar da kai gefe wai itama hakurin take bashi, wannan dabi'a tasu na matukar burge shi tare da faranta masa rai. Gashi dai basu yi laifi ba Ameerah ce kadai tayi, amma yanzu da zai nemi hukuntata se duk hankalin su ya tashi ba kuma zasu koma daidai ba har se ya hakura kamar dai yanzu. Girgiza kai kawai yayi ya wuce bedroom din sa leaving them behind Wanda Haanah ta fahimci ya hakura ne dan haka ta ce "Se ki tashi ai babar marasa jin magana,ban da wulakanci so nawa kike so in nanata miki ki daina shan ruwan sanyi da safe after kin fi kowa samun you're not fine Amma shine bakya ji, to go ahead and kill yourself se mu zauna mu uku, kinga se mu dinga lissafin ke da Maamah bakwa tare da mu". Yadda muryar ta ta shiga rawa bayan ta kai karshen zancen ze tabbatar maka tana cike da kewa da alhinin wadda ta kira ga Maamah a ran ta, fashewa da kuka Meemah tayi tana kiran Maamah, ita wallahi Maamahn ta yasa hankalin su tashi. Shaf Haanah ta manta da cewa tan wajen ya sa ta ambaci sunan Maamahn ashe rabon ta jawo musu jidali ne . Fitowar Dada da sauri daga dakin yazo ya dauki Meemah tare da ɗorawa a kafada ya shiga aikin lallashin ta, wannan yanayin ya karyawa Haanah zuciya ta shiga hawaye da shessheka abinda yasa itama Meerah fashewa da kuka. Gaba daya se ya rude ya rasa ya ze yi, waye ze lallasa ma ya rasa se kawai ya juya ya zuba musu idanun sa da suka kada sukai jajir, hada idon da suka yi da Haanah da yadda taga jan da idon sa yayi yasa ta san lallai sun tayar masa da hankali, hakan yasa tayi saurin dakatar da kukan ta ta shiga lallashin Meerah har tayi shiru, jakunkunan su ta dauka ta kai bedroom ta dawo taja hannun Meerahn zuwa bathroom din da ta haɗa mata ruwan wanka, se da ta shiga wankan ita kuma ta fito mata da kayan sawa sannan ta fita. Kan kujera ta tadda shi zaune ya dafe kan sa ga Meemah a kan shi tana birgima da kuka, da gudu ta karasa tana kokarin daukar ta wanda se lokacin ya bude ido ya girgiza mata kai a hankali sannan ya dago Meemah daga jikin sa "Shhhhhh, is okay pretty". A hankali ta fara reducing volume din kukan ta har ta daina gaba daya se ajiyar zuciya da take yi a kai a kai "What's the problem pretty nah?". "Dada Maamah". Ta fada a shagwabe da muryan kuka, seda ya hade abin da ya tsaya masa a makoshi sannan ya iya daurewa ya kakaro wani busasshen murmushi yayi mata yana riko yan mitsi mitsin fingers din ta "Maamah tayi tafiya na fada Miki sweery". "Yaushe zata dawo?, Ni dai akai ni wajen ta". Ta fada tana neman fashewa da wani kukan sedai be bari ba yayi saurin tallafo habar ta "Look ta kusa dawowa, taje can aljanna ne fa, kin san aljanna akwai dad'i ko shiyasa Maamah bata dawo ba amma zata dawo". "Da gaske tana paradise Dada?". "Eh mana princess". "Yanzu tana can tana cin fruits din aljanna? Su Apple, banana, orange, pineapple, mango, strawberry and...se me ma Adda Haanah?". Ta fada directing the Question to Haanah, murmushi ta mata trying to karasa calming nata tare da dauke mata hankali "Eh mana dear, har dasu pawpaw fa, ga kuma su plantain and more". "Allah yasa zamu shiga aljanna irin na Maamah mu ma muje mu yi ta cin dadin mu". "Ameen pretty jeki Adda tayi Miki wanka a canja uniform ko". Tura baki tayi tare da girgiza kai "No Dada, yau kai zaka yi min, ka manta ka ce min zaka min wankan so biyar in naje school ban yi kuka ba, and kuma ban yin ba ko". Gyada mata kai yayi yana yake ya mike da ita dauke a jikin sa ya wuce dakin su Haanah na bin su a baya, ita ta haɗa ruwan wankan shi kuma yayi mata, ana yi tana wasan ta tare da bashi labarai kai baka ce yar shekara uku da rabi bace, seda ya shirya ta cikin jeans da riga sannan ya nufi fita se kuwa ta daga murya tana magana irin wai ita tayi masa yadda ze ji ne tun da yayi nisa "Kar kace wa Maamah ta dawo da Dada, ka bar ta a paradise din ta tayi ta cin dadin ta amma ka fada mata kar ta cinye duka ta rage min". Wannan karon kam ba yake bane sahihiyar dariya yayi jin wani shirme amma se shima ya dan daga muryar sa kadan ya amsa mata da "Okay princess bari in je in fada mata". Da "toh Dada" ta amsa masa tana kwanciya kan dan Karamin gadon ta me kyau shi kuma ya fita, "Je ki sa a shirya mana table Meerah, lemme take a shower nima". "Okay Adda ". Ameerah ta fada itama tana ficewa saura Haanah da Meemah "Kar ki je ko ina ko da kuwa falo ne har se na fito, and kar ki fara yi min barna if not". Ta fada tana mata kallon gargadi sosai, cike fa biyayya ta gyada kan ta tana sa bmhannu cikin baki, shigewa bayin haanahytayi daure da towel yana saurin tayi tai wanka kafin Meemah ta bata matsala. _____ Yana shiga dakin sa ya fada ka bed hannun sa biyu dafe da kan sa da yake jin kamar ze rabe masa biyu, wani irin ciwo kan ke masa na tsananin damuwa da rashin bacci ga kuma yawan tunani dake addabar sa. Da kyar ya iya mika hannu ya bude drower ya debo maganin da be tsaya duba na mene bane ya afa a baki batare da ruwa ko wani abu ba ya shiga taunewa, dacin da ke ratsa bakin sa be kai wanda zuciyar sa ke masa ba, jiki ba kwari yasa hannun ya sake dafe kan yana rurruntse idanu "Me yasa Maryam, me ye laifi na, me muka yi miki da zafi da kika zabi yin nesa da mu bayan kin san muna tsananin bukatar ki?, Me yasa kika zabi barin yayan ki da mijin ki cikin wani hali?". Dan juyi yayi kadan a gadon se kuma ya cigaba "Na sani laifi na ne ko, shikenan am sorry Maryam, am really sorry but pls do believe that I so much love you Maryam, Ina matukar son ki mairo na, dan Allah ki dawo gare mu ko dan ya'yan mu, kin ga kullum se pretty tayi kukan ki, pls Maryam ". Kamar kuma wanda ya farka daga bacci se ya bude idanun sa wal wanda suka yi jajir kamar wanda jini ya kwanta "Astagfirillah, forgive me ya Allah, astagfirillah ". Se kuma ya sake dafe kai "Ya hayyu ya qayyum bi rahmatika astagees"....... Ouummey 📚✍️. Ouummey 12 {5/11/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey                      Ouummey 12 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________                _Free Chapter Twelve_ Haka ya wanzu dafe da kan sa da ke masa matsanancin ciwo cikin wani hali, kirjin sa wani irin bugu yake masa kamr ze faso waje, irin yadda kan sa ke sarawa ji yake kamr ya cire ya yar. Wuni guda haka ya wuni cikin wannan har zuwa karfe biyar da ya iya tashi yana dafe bango saboda jirin dake dibar sa, yana ji ana kiran sallar Asr amma ya kasa tashi har aka idar duk akan kunnen sa. Anan bedroom din yayi alwala ya gabatar d sallah a zaune saboda jiwar da yake gani, addu'ar da yake so yayi ma kasawa yayi dole ya silale ya kwanta kan praymat din yana runtse ido.       Oat din ta damawa Miemie kamar yadda suka fi kiran Meemah saboda sunan Maamahn su da taci sannan ta fita zuwa dining dauke da ita a hannun ta ta zaunar da ita kan seat daya itama ta zauna a daya, Ameerah ta zubawa abinci a plate ta tura mata gaban ta hakan yasa ta kalle ta cikin rashin fahimta dan mostly tare suke ci "Eat your food Ameerah and pls do take care of Miemie bari na gano Dada". Gyada mata kai Meerah tayi iya kuma ta shiga zuba abinci cikin plate daban, faten dankalin turawa me ruwa ruwa ta zuba masa da ya sha kayan lambu da kuma hanta sosai, cikin nutsuwa ta dora kan madaidaicin tray tare da dora goran ruwa me madaidaicin sanyi se kuma lemon kwali ta dauka ta nufi falon sa. Kan Centre table din sa ta aje abin kana ta karasa kofar bedroom din sa ta shiga knocking ganin bata gan shi a falon ba, a hankali take knocking din dan har ta takura masa sanin da tayi baya san hayaniya, jin shiru yasa cike da fargaba ta fara tura kofan a hankali har ya bude sosai kana ta shiga bakin ta dauke da sallama. A gigice ta karasa wajen da yake kwance ta shiga girgiza shi tana kiran sunan sa sedai ya kasa amsa wa, wannan ya kara gigita Haanah ta nemi fita a guje dan neman wanda ze taimaka mata a kai shi asibiti amma dole ta tsaya jin yadda ya riko hannun ta. "Yanzu zan zo, am coming Dada, zan kira maigadi ya taimaka min mu kai ka asibiti ne, sannu Dada yanzu zan zo". Da kyar ya motsa bakin sa yayi magana cikin muryar sa dake fita da kyar "Dauko min drugs dina a drawer Haanah". A rude ta shiga amsa masa tana mikewa "Toh Dada, sannu bari na dauko, sannu Dada". Da tarin magungunan ta dawo gaban sa ta zauna kana ta dauko wanda ze sha kasancewar ta san prescriptions din sa, bottle water din ta bude ta aje kana ta fara kokarin taimaka masa ya tashi zaune, duk da yanayin da yake ciki seda murmushi yayi escaping daga lips din sa, yo Allah ya tuba Haanah ko motsa shi zata iya yine balle ta daga shi. "Sannu Dada, sannu, open your mouth ka karbi maganin kaji". A hankali ya bude bakin ta sa masa kwayoyin kana ta sa masa bakin robar ya shiga shan ruwan, seda ya hadiye maganin gaba daya sannan ya janye bakin sa yana sakin numfashi kasa kasa, komawa yayi ze kwanta tayi sautin rike hannun sa tana girgiza masa kai "A'a Dada, kar ka kwanta maganin ze dame ka, ka dan zauna kadan ya fada maka, lemme bring your food tukuna". Jingina yayi kamar yadda ta bukata ita kuma tayi saurin fita zuwa inda ta aje abincin sa ta dauko masa, cokali tasa ta debo tare da kai masa baki taba fadin "Dada haaaaa". A tausashe, girgiza mata kai yayi alamun a'a se kuwa ta kwabe fuska tana neman yin kuka "Pls Dada ka daure kaci ko ka sami karfi kuma ciwon ya tafi, You know bamu da kowa a duniyan nan da ya kai ka Dada, we loose our Maamah ba zamu so muyi loosing din ka ba, you're all we have, our only strength and source of happiness, pls eat for our sake Dada, for your little ones kaiiii". A sannu ya bude bakin kamar baya so ko da yake ba kama bane baya so din, ze ci ne dan su kamar yadda ta fada dan mafi girman tashin hankalin sa shine ganin damuwa kan fuskokin ya'yan sa, har can go to any limit dan ya sa su farin ciki ko da kuwa shi baya ciki, a hankali a hankali ya dinga karbar abincin har ya koshi, she's glad ganin yaci da yawa dan farin cikin ta sosai ya bayyana kan pretty face din ta taba ta sakin cute smile "Ka gani Dada, dama kana jin yunwa, kalli fa ka kusan cinye wa na ji dadi, yanzu zuwa anjima zaka iya kwanciya amma da zaka hakura har kayi isha tun da kaji ana sallan magrib yanzu". "Allah yayi Miki albarka Rayhanah, Allah ya hada kan ku da yan uwan ki ya albarkace ku da mazaje nagari". "Ameen Dada, Ameen, in kama ka kaje kayi alwalan?". Dariyar sa me kyau yayi "Haba dai, Dadan ki is not as weak as you're thinking, zan je da kaina, kema je ki kuyi sallah da yan uwan ki and stay with them nima yanzu zan fito". Pecking goshin sa tayi tana wide smile "Okay Father, a fito lafiya". Ta fice rike da tray din kayan abincin sa, a falo ta tadda su Miemie da Ameerah zaune suna kallon cartoon, kallon ta Meerah tayi tare da daga mata gira alaman yaya yake and she answered cikin yi mata alama da hannu alamun he's fine. Duk suna yin body language ne saboda Miemie dan tana jin ance Dada sun san zata addabe shi ne ta hana shi sukuni da kiran Maamah da a rana se ta kira yafi cikin calbi. Rayhanah bata mamakin hakan dan a bayyane yake Miemie Maamah's girl ce akasin su da suke Dada's babies, a rayuwan su basu taba sanin wani abu wai shi kulawar uwa ba hakan yasa tsakanin su da ita kallo ne da gaisuwa, daga nan kuma se su takure waje daya, walwalar su kuwa har se idan Dada na gida. Zama tayi kan dining ta dan ci abinci a gurguje kana ta tashi zuwa bedroom tana musu magana "Oya girls, time for magrib prayer". Tashi duk suka yi zuwa dakin inda one after the other suka yi alwala Ameerah tayi wa Miemie sannan suka saka hijabs din su da Rayhanah ta dauko musu kana suka jeru kan praymat daidai lokacin da Dadan ya leko, ganin su a haka ya juya ya fita zuwa Masallaci suma suka tada nasu sallan. Suna idarwa suka yi azkhars din su again Rayhanah ta tashi ta dauko musu kur'anan su dake bedside drawer ita da Meerah suka fara karatu inda Meerahn ke biya mata karin da aka yi musu juya zuwa na yau, seda suka gama sannan ta kara mata verses biyar inda ita kuma ta cigaba da maimaita wa Haanah kuma ta koma ga Miemie. Cikin wayo da dabarar da Allah ya mata ta yi sa Haanah ta biya mata aya dayan da ta kara musu yau a school, tar yarinyar ta kawo karatun ba ko tuntube hakan yasa ta kara mata aya biyu marasa tsayi, shima se da ta ga ta iya sannan ta bar ta. Hijab ta cire ta karbi nasu ma da suka cire ta ninke tare da maidawa cikin wardrobe kana ta juyo se kuwa idanun ta suka fada cikin na Dadan ta da ke tsaye yana bin ta da kallo cike da soyayya da kauna me tsanani, a ko da yaushe ya kai kan sa kasa da sunan sujjada baya dagowa face yayi godiya ga Allah da ya albarkace shi da samun ya daya tamkar da dubu, yar dake matukar so da kaunar sa hadi da tsananin tausayin sa, yar da ba dan ita ba be san yaya rayuwa zata kasance masa da yaran sa ba alhalin yanzu da ba mahaifiyar su ta gushe. Rayhanah yarinya daya ce amma a wajen sa tafi yaya dari domin kuwa ta share masa hawaye tun kan ta san kan ta, tun tana karama take da basira da wayo hadi da nutsuwat fahimtar abubuwan da suka girmi hankalin ta, a maimakon abin ya dame ta yasa ta cikin wani hali se ya koya mata tausayin mahaifin ta da halin da yake ciki, wanda ta taso ta girma dashi ya ke kuma karuwa a kowace kwana da wuni, kaunar ta gare shi bata buya a ko ina a kuma ko wane irin yanayi, ita ce rai daya dake gane kowane irin hali yake ciki tun kafin bakin sa ya furta, ta san shi ciki da waje sedai kawai yayi mata ta babba da yaro ya layance mata wasu abubuwan amma ba wai dan bata fahimta ko gane ba. Tana fifita cin sa kan nata, walwalarsa kan nata, farin cikin sa kan nata haka kuma tana damuwa da damuwar sa tayi dariya da dariyar sa, shiyasa ita din daban ce cikin yaya ukun da Allah ya azurta shi dasu, ita ce kuma *RIBAR AUREN* Maryam da kullum ya kalla baya dana sani balle nadama yake kuma alfahari da kasancewar ta ikon sa mallakin sa. "Barka da dare Dada na". "Barka kadai yaran Dada, hope you all fine?". "Yes Dada". Suka amsa masa gaba daya ban da Haanah dake ta murmushi tana kallon su, seda ya gama gaisawa da su gaba daya sannan ta durkusa har kasa ta gaida shi, be amsa mata ba seda ya shiga har dakin yasa hannu ya dafa kan ta sannan ya amsa cike da walwala "Jikin naka yayi sauki ko Dada?". "Eh babyn Dada, Father baze mutu ya bar babies din sa ba har se ya aurar dasu gaba ki daya insha Allah". Dariya suka yi su duka ita da Ameerah suna rufe ido at the same time wai kunya, shima dariyan yayi kana ya dauki Miemie a jikin sa ya fita falo suma suka biyo bayan sa, a kan three sitter ya zauna tare da zaunar da Miemie kan laps din sa su kuma suka zauna each by his side. Cartoon me kau and educational ya kunna musu suka shiga kalla Ameerah da Miemie se hira suke akai, ganin hankalin su ya dauku yasa Rayhanah juyawa a hankali ta fuskanci Dada "Dadaaaaah". Ta kira shi cikin low tone dan kar tayi calling attention din su Meerah, ganin yadda ya zuba mata ido yana bata full attention din sa yasa ta karyar da kai gaban ta ba faduwa haka tana ta addu'a a ranta kan Allah yasa ya yarda da abinda zata fada "Pls Dada kayi aure". Ta fada tana sunkuyar da kai haka tan jin effect din piercing eyes din sa akan ta, kirjin ta na duka jin yayi shiru ta cigaba da magana da rawar murya "You're suffering Dada, kullum baka samun bacci, You're always having sleepless nights saboda mu, abubuwan sun maka yawa Dada, kai din namiji ne, ga matsalan office, ga na jama'a ga na namu ga kuma nasu Yaaya, Dada na damu da yawa, tun tasowa na nake ganin ka cikin kunci da damuwa, i want you to live a happy life Dada, fatana da buri na be wuce in dinga hango kwanciyar hankali, jin dadi da farin ciki a idanu da fuskan ka ba, pls dan Allah do me a favor in ga Dada na cikin yanayin da nake fata kafin Allah ya dauki raina kaji Dada". Tun da ta fara magana babu kalmar da ta doki ran sa kamar irin kafin Allah ya dauki ran ta, abu na zuciya kawai se ya dinga hango har gashi ance ta mutu, ga ta ance itama ta tafi kamar Maryam, se kawai ya shiga girgiza kai yayinda zuciyar sa ta dinga ayyana masa ze iya rasa yar sa mafi soyuwa a ran sa, ze birne rai mafi damuwa dashi "A'a, a'a, no Haanah, ba inda zaki je, a'a ba zaki mutu ba". Ganin yadda Dadan ya rikice yasa ta riko hannun sa tare da matsewa cikin nasa "Calm down Dada, nima ba zan so in mutu in barka ba, I'll not leave you Dada, not now not after, ka kwantar da hankalin ka kaji". Ajiyar zuciya ya sauke tare da rufe ido ya kwantar da kai kan makarin kujera se kuma ya bude ya zuba kan fuskar Haanah da ta cigaba da magana "Zaka yi aure Dada?, Zaka cika min buri na?". Da sauri ya hade rai "Kar na kuma jin maganar nan a bakin ki Rayhanah, ko ba yanzu ba, okay?". A sanyaye idanu cike da kwalla ta gyada masa kai zuciyar ta na karyewa dan ta san ba dan kowa Dadan yaki aure ba se dan su, yana tsoron ya auri wadda zata gallaza musu ko ta nemi raba shi da su "Insha Allah ba zan Kuma magana ba Dada, a koyaushe ni me bin umarnin ka ne, komai zan yi kai nake fara tunani kuma wannan ne dalilin da yasa na kawo batun aure dan nasan insha Allah in kayi dace da mace nagari zaka yi farin ciki a rayuwa, zaka sami nutsuwar da ka rasa tun zamanin kuruciya hak kuma zaka sami kwanciyar hankalin da baka taba tunani ba. Na sani saboda mune kake dodging maganar aure Dada saboda kana tunanin makomar mu in ba'a yi dace da tagari ba, sedai ya kamata akan komai mu zama positive, what if muka yi dace da tagari, kai ma da muma duk zamu sami jin dadi da walwala, and above all hankalin Yaaya ze kwanta, kayi tunani akan Yaaya, itama mahaifiya ce kamar yadda kake mahaifi, yadda kake kaunar mu haka Yaaya ke kaunan ka, yadda kake son ganin mu cikin farin ciki da walwala haka itama Yaaya ke son ganin ka, na sani ka san yanayin da take ji tun da kaima kana jin makamancin sa, shiyasa na kawo maganar da na san zata faranta maka da ita amma ba zan kuma ba insha Allah tun d baka so, am sorry for upsetting you Dada, am sorry pls forgive me". Gaba daya se yaji Haanah ta daure shi da jijiyoyin jikin sa, se yake ji kamar ta sa wata igiya me karfi ta zazzarge shi dasu, kawo batun Yaaya ya sanyaya gabban jikin sa gaba daya, eh ba karya tayi ba domin duk wanda ya kwana ya tashi a gaban Yaaya yasan babu abinda take fata da burin gani irin yayi aure a yanzu, ta sha zaunar dashi tayi masa nasiha, ko kuma tayi ta bashi labari mai cike da hannun ka mai sanda amma duk se ya nuna baigane ba, yanzu kuwa da ta alakanta abinda mahaifiyar sa take ji da wanda yake ji se ya gane radadin me girma ne, haka kuma akwai ciwo a zuciyar mahaifiyar sa dangane dashi "Na amince Haanah, amma not now, ban kuma ce a zaba min ba, a bar ni har zuwa lokacin da zan ga wadda ta kwanta min da kaina". A zabure ta ke kallon Dadan nata ido waje, "Da gaske Dada?, Da gaske ka yarda zaka yi aure?". Gyada mata kai tayi babu digon fara'a a fuskar sa, sedai ga mamakin sa hakan be sanyaya jikin Haanah ba balle har ya hana ta fara'a se ma wani karsashi da ya ga ta samu lokaci daya, karo na farko kenan da Rayhanah tayi farin ciki lokacin da shi yake cikin damuwa................ _*3 PAGES TO GO, FREE CHAPTERS A YET TO END*_. _*KAR KU MANTA LITTAFIN NAN NA KUDI NE KAMAR YADDA TUN FARKO NA FADA HAKA KUMA NAKE ADDING PREFIX DIN _FREE_ A HEADINGS DIN KOWANE PAGE, SO GA MASU BUƘATA SHOULD HURRY UP AND START MAKING THEIR PAYMENTS DAN 15 PAGES NE FREE*_. ME BUKATA ZE IYA DM TA WNN NUMBER👇 *09013101854* Ouummey 📚✍️. Ouummey 13 {5/13/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey                       Ouummey 13 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________             _Free Chapter Thirteen _ Yana lura da yarda Haanah ke walwala da farin ciki har zuwa lokacin da suka yi masa sallama suka tafi daki dan yin bacci, da ido ya raka su har suka shige daki yayinda ya sake gyara zaman sa kan cushion din da yake yana kwantar da kan sa kwakwalwar sa na yin nisa cikin tunani. Seda ta tabbatar ta Miemie tayi bacci kafin ta sauko daga gadon ta dauki wayar ta da sauri, curiously ta shiga kiran layin kakar ta without minding dare ya fara nisa dan ita after ten lokacin, seda wayar ya kusa karewa kafin aka daga tare da sallama, a dokan ce Haanah ta amsa wa kakar ta and without sauke numfashi ta ɗora da dalilin kiran "Albishirin kin Yaaya". Daga can bangaren dattijuwa ce zaune ina gadon ta me kyau kamar na yaran amare yan gata, ba wani shekaru ne da ita da yawa can ba sedai zata kai sittin da wani abu zuwa close to saba'in, cike da son jikar tata ta amsa mata da "Goro fari kakal Rayha". Ta bangaren Rayhanah duk da bata san yadda Yaaya ke bata mata suna amma farin cikin da take ciki yau ya hana ta complaining "Dada ya yarda ze yi aure Yaaya" ta fada excitedly tana washe baki kamar gonar auduga, unbelievably Yaaya ta zaro ido tana sake manne wayar da kunnen ta "Kai haba dai, wa ya fada miki wannan tatsuniya?". Seda ta tura baki gaba jin yadda Yaaya ke neman karyata ta bayan ta san karya bay acikin habits din ta sannan ta bata amsa "To wallahi da gaske nake kuma ba tatsuniya aka bani ba shi da bakin sa muka yi magana dashi kuma ya yarda yace ya amince ze yi aure". Wani irin kwallan farin ciki ne ya taru a idanun Yaaya da yasa muryan ta ya raunana "Allah yayi miki albarka Rayhanatu, Allah ya jikan mahaifiyar ku ya sa ta huta, ke kuma Allah baki miji na gari da yaya masu albarka da zasu ji kan ki kamar yadda kike jin kan mahaifin ki". Da Ameen Ameen Haanah take ta amsa Yaaya har ta gama addu'ar ta ta shiga share hawaye "Dama na fada miki ki daina raina karfin talakar gani, kina ta wani fada min ba zan iya ba b azan iya ba se gashi ba baki mamaki, kuma ina nan ina jiran alkawarin mu dan ban manta ba kince zaki bar min murjanin ki in dai na sa ya yarda, bye dare yayi se anjima". Rayhanah ta karashe tana dariya jin muryar Yaaya itama tana darawa, aje wayar tayi tare da kallon bed din Meerah se ta ga tuni ta yi bacci so se itama kawai ta kashe wuta ta kwanta kan gadon ta wanda kowa da nashi a dakin. Ta can wajen Hajiya Yaaya kuwa tana jin Haanah ta kashe waya itama ta aje taya tare da daga hannu ta shiga godewa Allah idanun ta na zubar da hawayen farin ciki, a cikin kaf rayuwar ta a yanzu dai bata da wani rai da take kauna kamar dan ta mahaifin su Rayhanah, tsananin soyayyar da take masa ne ya jagorance ta wajen aikata son zuciya ko kuskure zata kira abin wanda ya zama Mabudin duk kan wani kunci, damuwa, tashin hankali da rashin walwalar dan nata haka kuma suka zama makullin farin ciki da jin dadin sa, bata fahimci tayi kuskure ba seda lokaci ya riga ya kure ta yadda bata da wani abin yi musamman ma da duk lokacin da ta nemi yin wani hobbasa dan nata ke dakile t ta hanyar nuna mata ai komene tun da ya kasance zabin ta to he can endure it even if it'll cost his whole life ne. Bata yi kasa a gwiwa ba t shiga toilet ta dauro alwala tare da tada kabbara dan mika godiya ga Allah tare da fatan ya sallada abin a ran dan nata ba se nan gaba ya tubure yace be san zancen ba wanda a yanzu wannan opportunity din kadai take kallo as hanyar gyara kuskuren ta dan haka zata yi iya kokarin ta wajen ganin ta bawa mafi soyuwar dan ta farin ciki. ________ Rayuwa na ta tafiya abubuwa na faruwa masu dadi da akasin ta, a kalla yanzu kusan wata hudu kenan da muke zaune lafiya a gidan mu se yan abinda ba'a rasa ba, duk da zan iya cewa a kwanakin nan yanayin namu ze fi kyau da a kira shi kadaran kadahan dan kuwa dai ba wai muna cikin farin ciki bane, haka kuma ba wai ana tsananin tashin hankali ko rigima bane. Fushi ne dai yake yi kan wani incident da ya faru shekaran jiya, abin ba wani me zafi bane amma dake a wajen Salees ko me ya shafi ya'yan sa me zafi ne ba ya daukan shi da wasa se kuwa ya daukaka abin har fiye da misali. A shekaran jiyan ni ke da girki, hakan yasa na shiga kitchen kamar kowane lokaci na shirya launch kasancewar Sunday kowa yana gida, before in fara girkin da se da nabi ka'idar da ya tsara na cewa duk wadda ke da girki zata fara tuntubar yaran sa abinda suke so, in bakin su ya zo daya su biyun shikenan se a yi wanda suke so din gaba daya ko kuma ayi musu su biyu sannan me girki ya dafa abinda yayi niyya daga baya, in kuwa bakin su be yi daya ba to kowa a dafa masu wanda yake so individually, tun lokacin da yasa dokar na fada masa hakan wani karin aiki ne na daban gare mu amma se yace shi haka ya tsara dan in yaran sa ba su ji dadi sun yi walwala a gidan su ba a ina zasu yi?, Dole haka na yarda a wancan lokacin dan maganar shekara hudu baya nake yi wannan. Abinda ya faru shekaran jiya kuwa shine na tambayi Sahal abinda yake so kafin na shiga kitchen se yaron yace me zan dafa, take nace masa jallof couscous se watermelon juice, da farin ciki da komai Sahal yace min shi zai ci meaning base na masa different girki ba, ita kuwa Ilham da na tambaye ta se tace rice and stew zata ci, daga haka na shiga kitchen na hau ayyukana, nan da nan na hada abubuwan da zan yi na jera kan dining sannan na wuce daki na yi wanka tare da canja kaya kana na kwanta na huta ina jiran dawowar mijina daga masallaci Karfe biyu ya shigo wanda tun da na hango shi ta window na fito falon yana shigowa na masa sannu da zuwa tare da masa jagoranci zuwa dining din Mariya da yara suka biyo bayan mu, seda kowa ya zauna sannan na shiga serving din su daya bayan daya har n gama kafin na zubawa kaina na zauna dan fara ci sedai abin kamar almara se kuwa Sahal ya ture plate din gaban sa a shagwabe yana tura baki nan da nan kuma idanun sa ya tara hawaye, irin yadda baban ya rude yana tambayar sa lafiya se kawai na zuba masa ido ina jiran jin me ze ce, zuciya ta kuwa har da ayyana min may be shi da mahaifiyar sa ne "Bana son abincin nan Daddy". Da sauri na zaro ido jin abinda yace fuskar sa a kwabe kamar ba shi ne har da tsalle dan nace jallof din couscous din zan yi ba "Why didn't you tell your Aunty da zata yi girki?, She would have cooked your heart desire for you". Salees ya fada trying to rarrashi dan sa yaci abincin "Daddy I've told her ni pounded yam nake so while Ilham tace rice and stew, but see what she serverd me after serving Ilham her favorite". Strictly Salees ya dago yana dubana with plain expression a fuskan sa "Shi meyasa ba'a dafa masa abinda yake so ba after kuma yayi mentioning?". Seda na hadiye wani yawu ganin yadda yake interrogating dina kamar wata yarinya gaban ya'yan sa da matar sa sannan na iya na bada amsa "I've asked him me zeci and shima se ya dawo min da tambayan me zan dafa so i replies with jallof couscous, har da tsallen sa yana cewa yana so kafin na tambayi Ilham ta fadi nata, and here's the same boy narrating different story dan ban San yaushe yace pounded yam yake so ba". Daga yadda yake kallo na na fahimci ba wai zance na ya gamsar dashi bane sedai be yi hukunci directly yadda ya saba ba se ya dubi Ilham "Wane amsa yayan ki ya bawa auntyn ku da tambaye shi kan abinci?". Wlh a lokacin I was speechless, kenan salees na nufin be yarda da abinda na fada ba?, Mu sa ma be yarda ba, mu sa a ransa kawai yana ganin karya nayi, in ma hakan ne kenan baze iya rufa min asiri gaban yara ba se ya zubar min da kima, ko so daya shin Salees be kamata yayi tunanin tarbiyyan ya'yan sa ba, gaba daya se naji komai ya fita a raina, shikan sa Salees din naji ya zube min a ido na "Daddy naji fa sanda yake cewa couscous ze ci fa, Allah be fada mata sakwara yake so ba". Irin yadda Mariya ke bin Ilham da wani mugun kallo ka dauka kisan kai yar nan tayi bayan gaskiya ne kawai ta fada, shi kuwa Sahal yana jin me Ilham ta fada se kuwa ya ture plate din a matukar fusace da har yasa abincin kai ta zube kana ya tashi yana jan tsaki ya nufi barin dining din, zuba ido nayi kawai in ga hukuncin da salees ze yi ko da dai ba wani sabon abu bane cewa zeyi yaro ne. To ny utmost surprise se kuwa Salees ya mike a hanzarce har yana neman ture table din ya maza ya riko hannun Sahal dake huci kamar ze daki wani, cikin lallashi da kwantar da murya ya shiga lallaba shi kan yaje yaci abincin "Wallahi ba zan ci ba Daddy, kawai saboda ba'a sona ita Ilham se aka dafa mata abinda take so ni aka ki, shiyasa ma ni na tsane ta dan bata da kirki, mtsww". Ya sake jan tsaki, burin salees dan sa yaci abinci kar ya zauna da yunwa so se duk be yi overlooking wannan rashin kunyar da yayi a gaban sa ba, shi dai damuwar sa yaci abinci, ganin yadda uban ya damu se ita ma Mariya ta shiga maganar playing her own role Wanda ina gani na gane makirci ne "Haba Sahal wannan wane irin wulkanci ne, ka tashi kaci abincin nan ko se ranka ya ɓaci". Kawai se yaro ya fashe da kuka tare da shigewa jikin baban sa yana maganganu "Ka gani ko Daddy, itama Mommy bata sona, i won't eat this food ko zan mutu wallahi, Daddy pls ka maida ni wajen Granny". Aikuwa kamar wanda ake dannawa remote se salees ya ture Sahal daga jikin sa ya shiga zazzaga masifa "Wannan wane irin rashin mutunci ne da wulakanci, akan me zaku samin yaro a gaba da tsangwama har yana gwammace wa rayuwar wani wajen kan gidan uban sa, ba tun yau ba na sh fada muku ban hada son da nake ma ya'ya na da kowa ba dan a kan su wallahi zan saba ma kowaye, har kema ki bar ganin kece kika haife shi dan babu ruwa na ke mahaifiyar sa ce hukunta ki zan yi in kika nemi takura min yaro, gargadi na karshe kowaccen ku ta kiyayi taba min yara, ku kiyayi bata musu dan a maimakon yaro ya bar gida sedai ku kubar shi dan nan ne dolen sa gidan mahaifin sa akasin ku, ke khadeejah tashi ki dafa masa sakwarar". Tun da ya fara magana ban janye daga tagumin da nayi ina bin shi da kallo ba har seda naji last statement din shi "...ke Khadijah tashi ki dafa masa sakwarar"... Na sake maimaita kalaman a ƙwaƙwalwa ta dan in tabbatar da eh abinda salees ya fada kenan, bayan na tabbatar din se na dago na zuba masa ido wai dan in gane akan fuskar sa wasa yake yi ko da gaske sedai daga look din fuskan shi babu wani alamu dake nuna wasa, he look so serious ma'ana dai sakwarar yake so in yi wa dan gwal din dan sa "Is okay boy, kar in Kuma jin kace zaka je wani gidan, you've no home other than this house which is your father's house, and stop crying, your pounded yam is yet to be ready". Ya fada cikin lallashin dan sa da ya dauka ya dora kan cinya, murmushi sosai Sahal yayi yana kankame baban sa "Thank you Daddy, I love you so much". "Thanks so much boy, daddy loves his little ones so dearly". Se kuma suka saki dariya Salees na mikawa Ilham hannu itama tayi joining din su yamutsa fuskan da Sahal yayi yasa cike da kulawa ya shafa kan sa "Yunwa ne ko, dan yi hakuri yanzu zaka ci abinda kake so". Se kuma ya juyo inda nake "Why are you still seating, pls je ki masa abinda yake so yunwa na damun sa". Yanzu kam na tabbatar da gaske yake abinda ni kuma ba zan dauka ba kenan, haka kawai saboda san ran sa da na dan sa ya hana mu cin abinci cikin kwanciyar hankali dan ko spoon daya ban yi ba yaron nan ya tashi hankalin mu yanzu kuma ana batun in tashi in masa pounded yam "Am sorry bazan iya masa pounded yam ba yanzu its too late, gashi ko abinci ban ci ba and ka san dadewan sakwara in nayi sauri in gama in an hour ga kuma abincin dare na jirana". "So kina nufin ya zauna d yunwa kenan". Se da na nunfasa kana na dubi sashin da Sahal yake tsaye "Ba haka nake nufi ba, yau kam yayi hakuri yaci couscous din gobe se in masa sakwarar ko kuma in yi ta as dinner". Ko kafin salees yayi magana Sahal y riga shi "Allah ba zan ci couscous ba, akuya ne ni da zanci abu me kaman dusa, ni ba zan ci ba". "And I'll cook the pounded yam as dinner, now lemme cook indomie for you da sauri'. "Ni i won't eat sakwara for dinner, ai kin san bana cin abinci me nauyi da dare malamin mu yace mutum yanayin katon ciki". Confusedly na tsaya ina kallon yaron jin kome nace se ya kushe, ko ta ina na fito se yace ba haka ba, gyaran murya yayi yana kallona strictly yace "Kawai kiyi masa tun da ya nace, ina ce muna da pounder". "Ka fa san ya lalace tun kwanaki". Na fada kaman zan fashe da kuka, se shima yayi shiru na dan lokaci kafin pleadingly yace "Pls pound it a turmi tun da bashi da yawa, i can't put an eye yaki cin abinci". "Am sorry Salees, Mariya tayi masa ko kuwa kuje restaurant dan wallahi ba zan iya yin sakwara yanzu ba". And this my reply shine dalilin da yasa Salees ke ta min fuskan shanu yau kwana biyu kenan, dan kamar yadda na fada ba zan yi ba ban yin ba, ban san yaya suka yi ba, Mariyar ce tayi ko kuwa siya suka fita suka yi................... *TWO PAGES TO GO💃💃💃, SAURA PAGES BIYU FREE CHAPTERS SU KARE, KINDLY MAKE YOUR PAYMENT FOR IT'S PAID BOOK* *INTERESTED BUYERS SHOULD CONTACT* 👇 *09013101854* Ouummey 📚✍️. Ouummey 14 {5/14/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey                        Ouummey 14 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________             _Free Chapter Fourteen_ Daga aiki na taso a matukar gajiye, jiki na gaba daya ciwo yake min dan kwana biyu ina overworking kaina saboda gujewa tunanika ga kuma promotion din da ya matso sosai, yanzu haka gobe za'a sanar da sunayen wanda suka yi nasarar samun wannan cigaban, dukan mu ma'aikatan da muka san an yi nominating sunan mu cikin zulumi muke dan kuwa bama fatan list ya fito babu sunan mu, promotion abun farin ciki da so ne ga duk wani ma'aikaci, yanzu haka ji nake kamar in jawo gobe tayi tayi dan kawai in samu peace of mind. Mayafi na a hannu na shiga falon dan tun a kofar falo na cire shi saboda wani nauyi dana ji ya min, ba abinda nake bukata a lokacin kamar wanka da bacci ko naji daidai. Turus nayi ganin Hajiya Iya, kannen Salees Rukayya, Sadiya da kuma auta Hannatu se matar kanin sa Sani me suna Lubabatu, kanwar Mariya me suna Safiya, da yayar ta Safara'u se maman su Hajiya Ramatu. Ban san me yasa gaba na ya fadi ba ganin wannan taron sedai na daure na karasa falon ina kaiwa tsugunne na shiga gaida Hajiya Iya da bata amsa min ba se kare min kallo da ta shiga yi kafin ta karkata kai tana kankance ido "Wato yawon tambadewar da kike kenan kika fake da aiki, yanzu mayafin ma a hannu kike yawo dashi". "A'a a kofar falon nan na cire saboda gajiya". Na bata amsa kai a sunkuye "Uhmmm kowa dai yayi me kyau kan sa". Jin tayi shiru bata kuka cewa komai ba yasa na juya ga mahaifiyar Mariya itama na shiga gaida ta amma itama bata amsa min ba dan gara ma Hajiya Iya dan ita ko kallona bata yi ba se kau da kai da tayi tana jan tsaki. Lamarin ya daure min kai dan kuwa ba haka ta saba min ba, ko da ba haduwa muke yi masu wani frequently ba amma in dai na gaishe ta tana amsa wa ko da dai ba wani da tsayi bane dan iyaka ta da ita 'Lafiya' shine amsar gaisuwa ta d ita koyaushe. Cikin sanyin gwiwa na dan mike sannan na gaida yayar ta Safara'u, ban tsaya jin zata amsa ko kuwa ba na yiwa sauran magana wanda kannen Salees ne da matar kanin sa se kuma kanwar Mariya "Sannun ku da gida". Da sauri nayi gaba dan jiki na ba bani wannan taron bana lafiya bane, ga kuma kallon banzan da na lura duk suna bina dashi, wankan da nake dokin yi duk se naji ba zan iya ba, kawai so nake in San meke faruwa a gidan namu inda na shiga addu'ar Allah yasa ba shida alaka dani dan to be sincere tuni na gama gajiya da wannan tashe tashen hankulan, kwanciyar hankali nake bukata a yanzu. Kamar wanda aka karanta min se kalaman da kunne na suka jiyo min lokacin da nake bude kofar daki na suka dawo min cikin ƙwaƙwalwa "Hmmm, lallai mugu bashi da kama, kalli matar nan kamar wata saliha alhalin kungurmar munafuka kuma azzaluma ce, yanzu ban da mun san hali ai da se mu karya ta abinda muka ji da kunnen mu". Rukayya kanwar Salees me bi masa ta fada in da Safara'u ta cafe "Ke ni fa a wannan zamanin bana tantama kan duk abinda aka ce mutum yayi dan wallahi wani mutumin in zaki shekara goma dashi ba zaki taba sanin wasu bakin halin nasa ba se Allah ya ciyar dake, to balle kuma wannan matar da tun a baya bakin halin ta ya fito fil, kina zaton zata bar Mariya ne cikin kwanciyar hankali bayan Allah ya bata haihuwar da ita ta rasa?". "To wa ya hana ta haihun ita, aikin banza, Allah ne fa ya san nufin jaki da be bashi kaho ba, wannan da ta haihu ba musan me zata yi ba, a haka ma muna fama da ita, ai ni na godewa Allah da be Kaddara min hada jini da wannan bakar jarabar ba". Hajiya Iya ta fada tana wani tsuke baki, sauke numfashi nayi bayan na gama tunani na, lallai akwai wani abu, tabbas akwai sharrin da aka kulla min da har yaja min wannan bakaken maganganun sedai ina fata Allah yasa komai ya zo min da sauki ya kuma bani juriya da hakurin dauka. Da kyar na iya nayi wanka na canja kaya, yunwar da na shigo da ita kuwa tuni ta fece haka ma baccin da nake kuzun nayi shima duk ya yi nasa wajen, jira nake kawai in ji an doko min kira an fara tuhuma ta, dalilin tuhumar ne dai ban sani ba. Kwankwasa kofar da aka yi yasa na dan zabura kadan kafin na kurawa kofar ido, da kyar na iya mikewa naje na bude, kallo daya za'a min a san a firgice nake. "In kin ga dama ki fito Hajiya na magana". Hannatu ta fada min tana wani yatsuna fuska haka at the same time tana harara ta kasa kasa, tsabar kidima ko dankwali na da ya fadi ban tsaya dauka ba na bi bayan ta ina kiran Allah a zuciya ta. Wannan karon gaba dayan su ne a falon har da Mariya da Salees da kuma wasu mata biyu manya da nake kyautata zaton yan uwan ta ne dan ban san su ba cikin familyn Salees, kowanne ka kala fuskar sa a hade take babu alamun wani abu wai shi fara'a yayinda idanun su ke kara kaina a jiki na kamar zasu dauke ni da ido. Daga fuskar su zaka hango tsantsan hasssada da kishi ganin irin kirar da Allah ya zuba min, riga da skirt din jikina ya kama ni dam kamar yadda kayana suke dan faranta wa miji na, ban lura a haka na fito ba dankwali ba balle mayafi se da Hajiya Iya dai ta yi magana "Sannu isasshiya, hamshakiya mandiya, shima dankwalin kina jira yaron naki ya je ya dauko miki ne?". Gaba dayan su suka kuma watso min na mujiya lamarin da yasa naji na takura matuka, na mike da sauri dan daukowa se ta kuma dakatar dani "A'a koma ki zauna dan na tabbatar da kina sane kika fito, koma me kike so mu gani mun gani sedai Allah wadaran irin wannan kyan na dan maciji". Komawa nayi na zauna jiki na kamar an min duka, wai shi dai wanda baya sanka kome kayi se ya kushe, kome kayi baka iya ba, kuskure a wajen sa ganganci ne, Allah ka rabu mu da wahala Ameen. "Dago ki kalle ni nan Khadijah, ba na tsoran ki bana tsoran fada miki magana dan ba zan zuba ido ki cigaba da cutar min da da matar sa tagari ba uwar ya'yan sa bayan ke ko kara baki aje ba.     Na dade da sanin ke din ba karamar muguwa bace munafuka kuma azzaluma tun lokacin da kika nemi raba ni da dana sedai Allah ya fiki ya tankwabar da mummunan nufin ki, sedai ban san rashin imanin ki har ya kai ace ki karbi maita dan cutar da matar Salisu ko yayan sa ba, kin yi asara, wallahi kin yi asara Khadijah dan kin dade da kwashe kayan ki daga gaban Annabi". Wani irin dam kunne na yayi, ƙwaƙwalwa ta ta dakata daga aiki, kwata kwata kaina ya toshe, gaba daya na daina ganewa d fahimtar komai da suka cigaba da fada se aikin kallon bakin su d ana cigaba da yi dan tun da Hajiya Iya ta ambaci maita na dago kaina daga sunkuyar dashi da nayi. Fiye da mintina biyar kafin ƙwaƙwalwa ta gama accessing all she've said, maita, na karbi maita, meaning suna nufin ni din mayya ce, mayya fa, innalillahi wa inna ilaihi rajiun. A lokacin wani irin Hajijiya nake ji cikin kaina, kaina ya shiga juyawa kamar wanda ake wujijjigawa, dakin ya shiga juyawa dani kamar zan kife yayinda kalman maita ya shiga yawo a kunne na, lamarin da ya tilasta min saka hannaye na toshe kunnuwa na tare da runtse ido na da sauri haka kuma at the same time Ina girgiza kan tare da furta kalman a'a, a'a da karfi cikin wani irin yanayi me ban tausayi ga masu zuciyar imani. A lokacin da na budi ido se gani na nayi kwance kan gado na Salees tsaye a kaina ya jingina da bango, nauyin da naji kaina yayi ya tilasta min mai da ido na rufe kafin kuma in a blink of an eye na sake budewa lokacin da tiryan tiryan abin da ya faru a falo ya dawo min kaina, a gigice na fara kokarin mikewa wanda hakan ne ya ankarar da Salees cewa na farka, da saurin sa ya matso ze rike ni na goce na nufi kofar da ke rufe wadda ake kan bugawa tare da kiran sunan sa, da sauri ya riko ni na shiga kokarin kwace wa "Ina zaki je haka a gigice, ki tsaya kar ki je ki fadi". "No, sake ni, ka sake ni in je in fada musu ni ba mayya bace, ka sake ni in ji me na musu da zafi da zasu hada ni da kalmar maita, dan Allah ka bar ni naje na musu bayani ko zasu fahimta suyi withdrawing wannan mummunar kalmar daga gare ni". "Naji zan sake ki, but first ki tsaya ki nutsu kar ki jiwa kan ki ciwo". Duk yadda Salees yaso dakatar dani naki, so nake kawai na fita na fada musu ni ba mayya bace, so nake in ji sun ce Khadijah wasa nake muke miki ke ba mayya bace. Kubcewa nayi na nufi kofar tare da murza key din da ya sawa kofar na fita, Rukayya, Sadiya da Hannatu duk na tsaye bakin kofar, ashe suke bugu tare da kiran sunan sa suna fada masa Hajiya Iya tace ya fito daga daki na kafin ran shi ya baci. "Rukayya Sadiya ai kun san ni kun san ni ba mayya bace ko, kema Hannatu kin sani ko?". Wani matsiyacin tsaki Sadiya taja tare da juyawa ta nufi falon ragowar suka rufa mata baya suma bayan sun yi nasu tsakin Hannatu na kunkuni kasa kasa, a haukace na rufa musu baya ina kuma yi musu magana, ni dai buri na kawai su yarda ni ba mayya bace. Fisgo ni Salees yayi jikin sa ya rungume, duk yadda nake ture shi ya sake ni ya kiya har seda ba hakura na lafe jikin sa na shiga maida numfashi da karfi da karfi kafin kuma wani maraitaccen kuka yi kwace min, kuka nake yi me suna kuka wanda tun d nake shiga tension a gidan Salees ba na tunanin na taba makamancin sa, Muryar Hajiya Iya ce ta sa Salees janye wa da sauri yana sosa kai "Sake ta sallamamme, sake ta nace karamin mara mutunci, mara zuciya kawai, kai in da kasan kan ka har ka kuma kallon wannan abar bayan abinda tayi, wuce muje, kema munafuka muje dan yau ko mutuwa zaki yi karewar mutuwa se an yi maganar nan yau". Hak ta tasa mu gaba har ciki falon, na sake neman waje na zauna haka ma Salees itama ta koma wajen ta ta zauna "Abinda y faru jiya d dare zuwa yau ya zama na farko na karshe, wallahi tallahi rantsuwar dan musulmi kika Kuma taba min suruka ko jikoki se ran ki ya baci, in zaki yi maitar ki kiyi ta can a waje amma ban da nan dan b zaki ci riba ba". Seda na saki sheshshekar da ta taso tun daga kasan zuciya ta sannan na dago "Na rantse da girman ubangijin da ya halicci sammai da kassai Ni ba mayya bace Hajiya, a cikin trend din dangin mu wallahi babu maye balle in gada". "Yo Allah na tuba maitar da ake siyarwa yanzu kamar alawa a kasuwa, ai ba abin mamaki bane dan babu a dangin ki kuma an same ki da ita, ni dai na fada miki wallahi ba zan lamunta ba dan gwara ki cinye kan ki da ki taba min zuri'a". "Me nayi muku da zafi hak da zaku jefeni da kalmar maita, me na tare muku da zaku min wannan accusation din, auren Salees gare ni ne laifin da har yaja min wannan zargin ko kuwa tsabar tsana ce?". Na tambaya hawaye na kafewa a fuska ta yayinda ya koma zuba ta cikin zuciya ta "Yi man shiru munafuka mara tsoron Allah, wa zaki yaudara da kalaman ki ko da wani fuskar tausayi bayan ke baki tausaya wa kan ki ba, daga yin mafarkin ki kin biyo ta a guje kin daki cikin ta yarinya ta tashi da ciwon ciki da zubar jini, hankali be kwanta ba har seda cikin jikin ta ya zube, cikin yan uku annamimiya kin yi mana asarar rai har uku, wallahi Allah ya isa tsakanin mu dake dan ba zamu taba yafewa ba". Hajiya Ramatu mahaifiyar Mariya ta fada tana fashewa da kuka yayinda Hajiya Iya ta shiga sharar ido itama su kuma ya'yan su suka rufe su suna basu hakuri da fadin Allah ze saka musu, ni dai tun jin wai Mariya tayi mafarki na se na juya gare ta na zuba mata jajayen ido na ina kallo na tsayin lokaci kafin cikin wata irin murya na tambaye ta "Na zubar Miki da ciki ta hanyar maita ko Mariya?, Kin yi mafarki na na daki cikin ki gashi kuma ya zube ko?". Kallo na Mariya take yi kawai bata ce komai ba hakan ya sa na saki wani busasshen murmushi mara kyau balle fasali haka mara ma'ana "In har na zubar Miki da ciki, in har na taba yin wani abu dan cutar da ke ko ya'yan ki Allah ya saka Miki da gaggawa Mariya". Na fada da karfi ta yadda kowa ze jini kana na maida duba na kan Hajiya Iya da Hajiya Ramatu "Kuyi hakuri Hajiya, kuyi hakurin cinye muku cikin Mariya da nayi kuma ku kwantar d hankalin ku domin ba zan kuma saukar da kwadayi na kan ya'yan ku ba". "Kuma kuyi hakuri". Na fada directing to su Safara'u da ragowar matan da kuma su Rukayya kana kuma na tashi da sauri nayi daki na tare da kullewa da key, irin ciwon da zuciya ta ke yi a lokacin ba me sauki bane, hawaye ya kafe a idanu na, ƙwaƙwalwa ta ta tushe na rasa tunanin da zan yi, daga karshe se na samu kaina da nufar toilet na dauro alwalar da ban san daidai nayi ta ba ko akasin haka, Kur'ani na dauka na shiga karatu a zuci kafin a hankali murya ta ta fara fitowa kadan kadan har ta fito sosai kana kukan ya biyo baya. Ina jin bugun kofa tare da muryar Salees amma ban ji a raina zan bude kofar ba, ina kuka haka ina karatu ban fasa ba har se da naji mafi girman kason nauyin zuciya ta ya ragu, wani irin bacci ya dinga sanda ta sannan na aje Kur'ani na bingire a wajen. Ban farka ba se bayan magrib, a lokacin kam alhamdillah bana jin wani bacin rai me girma sedai kalmar maita ta samu wajen zama na musamman a ƙwaƙwalwa ta, seda nayi wanka na canja kaya na ci snacks dina sannan na bude kofar na fito, babu kowa a falon haka kuma gidan yayi shiru alamun duk sun tafi, fridge na bude na dau ruwan da ya fito dani sannan na nufi komawa daki se Salees da ban lura dashi zaune kan kujera ba ya dakatar dani "Khadeejah". Juyowa nayi na kalle shi tare da sake masa murmushi ganin yadda duk yayi wani iri, tasowa yayi gare ni tare da riko hannaye na "Are You fine, ba abinda ke damun ki, ba inda ke Miki ciwo?". Wani murmushin na sauke jin tambayoyin da yake min wanda shima ya san in nace bana jin kome ya fada karya ne sedai dan na kwantar masa da hankali se na amsa masa "Ka kwantar da hankalin ka, am perfectly fine and okay". "Abinda hajiya iya su.....". Rufe masa baki nayi da hannu na har lokacin murmushi na be bace ba "Hajiya Iya kamar Ummi na ce, so karka damu da abinda ya faru". Daga haka nayi gaba leaving him speechless. Kwanciya nayi kan bed tare da janyo waya ta, ina bukatar shawara a wannan lokacin dan ina jin bazan bar wannan maganar ta tafi haka ba, dole zan dau matakin wannan bata sunan da ake kokarin yi min, kotu zan kai kara, shigar da kara zan yi abin min hakki na, amma kafin nan ina bukatar tattaunawa da wani, ina bukatar wani da ze yi supporting dina ya fada min Yes kin yi daidai Khadijah sedai waye wannan?. Ba ze yiwu in fadawa Ummi ba balle har hankalin ta ya tashi, yaya Salima kuwa na san in na fada mata kamar na fadawa Ummi ne dan se ta sanar da ita, Abba kuma is not a solution dan hanani ze yi yace in yi hakuri, yayyu na kuwa ba ma zan iya maganar dasu ba dan suma maza ne ba fahimta zasu yi ba. Na dade rike da waya a hannu kafin na shiga facebook, group din mu na NATIONAL ASSOCIATION OF INFERTILE WOMENS na shiga nayi posting anonymous message, in brief na fadi matsala na tare da neman shawara bayan na canja abubuwa da yawa daga abinda ya faru dan gudun halin mutane na daukan matsalan mutum suyi ta yadawa. Kafin kace me members suka shiga reacting tare da comments, ban duba ba seda na tara da dan yawa sannan na shiga bi one after the other, sannu a hankali nake karantawa ina analysing bangaren shawarar da tafi yawa, in yi ko kar inyi da dalilin haka, sedai mostly duk suna cewa kar in Kai karar ne saboda ba kowa yayi accusing din ba face uwar miji na, duk kuma so d kaunar da mijina ke min base goyi bayan kai mahaifiyar sa kotu ba hakan kuma ze iya kawo karshen aure na, in bar su da Allah kawai in cigaba da fada masa ze min sakayya da gaggawa. Wannan itace shawarar da na dauka, se da na gamsu da ita sannan na kashe datan na koma na kwanta ina cigaba da tunani. Washegari haka na shirya na taci aiki na sedai kukan da nayi juya yasa fuskana duk ya tasa duk da kuwa na dan shafa powder da kohl dan ya boye yanayi na, karfe goma na safe muka shiga meeting din da anan ne za'a fadi list din sunan mutanen da suka yi dace da samun promotion da kuma gurin da aka canja musu na aiki in an canja din. Suna na ne na biyar a list din, wani irin sassanyan farin ciki da ya sauka a raina a lokacin ba zan iya fada ba sedai be yi nisa ba ya gushe jin an canja min garin aiki an maida ni garin Bakwarni maimakon garin Darma da nake, sanyi jiki na yayi dan a bayyane yake dole haka zan hakura da promotion din in cigaba da zama a nan dan baze yiwu in tafi wani garin aiki ba bayan aure na da mijina na garin Darma ne. Sunan Salees shine na goma sha biyu dan daga kasa aka fara zuwa sama, shima ya samu promotion me girma haka kuma shima an canja masa gari zuwa Bakwarni lamarin da ya faranta min fiye fa komai dan bana tantama yanzu kam zan je tun da shima dole ya koma can. Da wannan farin cikin na dawo gida ina tsara yadda zan je in yi wa family na sallama dan sati kadai aka bamu muyi reporting sabon wajen aikin mu, ranar kam a gidan Ummi na na wuni dan saboda guilty din abinda su Hajiya Iya suka yi min Salees ya bar ni na wuni can. Shawarwari masu yawa Ummi ta bani wanda naji dadin su n al'umma kudire niyyar aikata wa insha Allah, na ziyarci yan uwa da yawa a satin har ranar tafiyar mu yayi. Ranar asabar da yamma muka yi sallama d jama'a muka dauki hanyar garin Bakwarni ni da Salees da driver, tafiyar awanni goma sha biyu da mintina ya kai mu cikin garin Bakwarni, gidan da Salees ya siya muka sauka dan shi ya zo so daya ya duba yanayin garin tare da siyan gidan da zamu zauna. Tsananin gajiya be bar ni na yi komai ba a ranar se washegari na gyara ko ina na shirya mana kayan mu, gidan yayi min matuka dan bedroom uku ne se kitchen da toilet a falon, haka kuma each bedroom na da nashi toilet din. Washegari monday muka yi reporting wajen aikin mu in da Salees ke da matsayi na uku a ma'aikatar ni kuma matsayi na biyar, aiki sosai muka yi dan daidaita alamura ta yadda aiki ze mana sauki, a ka'ida a ranar zamu yi meeting da general head na ma'aikatar gaba daya sedai ya bada uzirin baze samu zuwa ba so a ka daga meeting din zuwa ranar da ya dawo daga tafiyar da yayi................. *GEN GEN GEN, END OF FREE PAGES YA ZO, DAGA GOBE ZA'A GAMA FREE CHAPTERS AND D SAGA IS YET TO BEGINS. KINDLY HURRY UP AND MAKE YOUR PAYMENT BASE MUN FARA A ZO ANA KOMAWA BAYA BA, OUUMMEY IS VERY AND VERY READY TO ENTERTAIN, EDUCATE AND MOTIVATE YOU WITH HER NOVEL RASHIN HAIHUWA, KAR KU BARI A YI TAFIYAR NAN BABU KU DAN WALLAHI YOU'LL MISSED. INTERESTED BUYERS SHOULD CONTACT 👇 09013101854 Ouummey 📚✍️. Ouummey 15 {5/15/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey                        Ouummey 15 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________               _Free Chapter Fifteen _ ____________ ____________ Zuba mata ido kawai Falmata tayi tana kallo ta rasa me za tace, she's totally speechless da wannan aikin na Farida, ta sani su din sun dade da zamar wa juna yan uwa, sun fi karfin a kira su aminai balle kuma kawaye, matakin alakar su ya koma tamkar blood relatives sedai bata san har haka Farida ke matukar kaunar ta ba se yau. A hankali ta kuma juya katin hannun ta wanda ba komai bane face passport, kana ta Kuma maida duban ta kan Farida da ita ma take bin falmatan da ido "Dan Allah maimaita min me kika ce Farida". "Wani abu na fada na daban ne?, Nace ga shi nan dan ki ya gama yi miki komai da ya kamata na tafiyar ki India, kuma insha Allah jibi jirgin ku ze tashi ke da harira saboda ta kula dake ni kin ga baze yiwu in bar su Hassana su kadai ba ga kuma Business din mu, amma tare zaku je da dan naki ya daidaita komai sannan ya dawo, nima kuma kafin ku dawo din zan zo dan jira nake ayi hutu su tafi gidan yayan nasu, a cikin wannan maganar me ne baki fahimta ba?". Fashewa Falmata tayi da kuka, kukan farin ciki da kuma takaici at the same time, cikin muryan kukan take magana ma Farida "Tun da muka taso da ke ban taba jin wai bani da dan uwa ko yar uwa ba a duniya saboda kin cike ko wane gurbi Farida, duk abinda kika san ina so yi kike kafin in furta, kome zan bukata aje wa kike kafin na ambata, ban san dame zan saka Miki ba Farida, ban san me zan Miki ba in biya ki, a kullum roko na Allah ya kara miki budi da daukaka, Allah ya jikan iyayen mu in basa raye, Allah y raya Miki zuri'a yasa masu amfani ne, Allah kuma ya bar ni dake har karshen nunfashi na.        Yanzu dai dubi Alhaji da nake karkashin sa, hakkin neman lafiya ta ke rataye a wuyan sa amma ya nuna lafiyar tawa bata gaban sa, ya tattara ya zuba min ido yaki yin wani hobbasa kan neman lafiya ta bayan babu rashi balle kuntata a tare dashi face zallar son zuciya da rashin adalci, b azan yi masa mummunan fata ba Farida amma tabbas da sannu se hakki na ya kama Alhaji in har ya zalunce ni". Kwalla Hajiya Farida ta shiga gogewa tana duban Falmata emotionally, "Ni ya kamata in Miki wannan addu'ar Falmata, ke din macece me kyakkyawar zuciya, ba ni na fara miki alkhairi ba halaccin saka alkhairi da alkhairi kawai nayi, kome Hammad ya zama a yau kin san dalilin ki ne?, Ko wace daukaka Hammad ze samu a rayuwar sa kin san kece jigo, ban da kuma tarin alkhairan ki gare mu tun Alhaji na da rai, Falmata kin so ni tun ina abin ki da gudu wajen jama'a, kin kusance ni yayinda kowa ke gudu na, kin tallafe ni lokacin da na rasa wani mataimaki, shin in ban Saka alkhairi ba me kike so a kira ni, balle kuma ni ina miki kallon yar uwa ce da muka fito daga cikin mahaifa daya, ko kin manta kece.........". Da sauri Falmata ta sa hannu kan bakin Farida tana girgiza mata kai hakan yasa Farida ta cire hannun daga bakin ta "In har ba kya san in tuna Miki to ki bar maganar dan in ance za'a ayi tone tone to kuwa kece kika yi sadaukarwar, ni kwatanta wa kawai nake, shi kuma Alhaji kamar yadda kika fada Allah ze Miki sakayya tabbas hakane, a da nayi niyyar in kin tafi can India nikuwa in shiga in fita har se na rama miki abin da aka miki sedai yanzu tsakani na ga Allah na fasa na bar shi da Allahn kamar yadda kika fada, ina kuma fatan ace an yi aikin nan cikin nasara". "Allah yasa Farida, in har kuwa akayi Nasara ki rubuta ki aje se na rabu da auren Usman domin kuwa bashi da wani amfani gare ni ta kowace fuska". "Allah ya kai mu, nidai fatana a dace in ga kin dawo gare ni lafiya lau, wannan shi ze samar min da kwanciyar hankali da nutsuwa". "Allah ya yarda, in Kuma bani da rabo...". Wani irin ƙatuwar harara da Farida ta balla mata yasa bata karasa a binda zata fada ba ta kyalkyale da dariya tana dagewa Faridan gira cikin tsokana lamarin da yasa suka tuna baya su ka kuma sake darawa sosai... ____________ "Yaaya na fadawa Haanah ai kar ace za'a sama min mata a bar ni in zaba da kaina". Cikin son kwantar masa da hankali ta yadda ze amince wa kudirin ta ta shiga yi masa bayani "Kar ka damu kan ka Ibrahim, duk abin da za'a bukata a wajen mace Saratu na dashi, halin ta kuwa base na ce maka komai b adan kasan daga gidan d take, fatana kawai amincewar ka dan ba zan maka dole ba". "Amma yaya bakya tsoron a maimaita yar gidan jiya?". Da sauri ta shiga girgiza kai "Insha Allah ba abinda ze faru, bana fatan in maimaita kuskuren da nayi a baya shiyasa ma ban yi maka magana ba se da naji t bakin ita Rahinatun kuma alhamdillah tayi na'am dan yadda take walwala ya shaida min tana farin ciki da lamarin". Shiru Dada yayi dan daga jin yadda Hajiya Yaaya ta ambaci sunan sa Ibrahim kai tsaye yasan ta kai makura wajen son hadin nan ta yadda komai daze fada ba zata gane ba duk kuwa da tace wai amincewar sa take nema dan haka se ya shafawa kan sa lafiya kawai "Shikenan Yaaya, Allah ya sa hakan yafi alkhairi". "Ameen, ko kai fa, insha Allah wannan karon se mun ce gwara da akayi". Shidai be Kuma cewa komai ba har ta gama maganganun ta ya mata sallama ya fice, sedai fa a fili yake ya amsa mata ne kawai dan ba yadda ze yi dan ya kasa boye hakan a ransa, sanadin bacin da ran sa yayi ranar a gidan ya bar su Haanah suka kwana abinda ba ya iyawa se an kai ruwa rana dashi, jikin Hajiya Yaaya yayi sanyi ganin hakan se dai kuma wani bangaren zuciyar ta na fada mata ta share shi da sannu da kan sa ze dawo yana gode mata. To abu kamar wasa karamar magana na neman zama babba dan kuwa sati biyu kenan babu Dada babu labarin shi, shi be zo gaishe da Yaaya ba kuma be zo dibar su Meerah ba, a kuma tsukin lokacin har an yi maganar sa da Rahinatu an karbi komai na aure in da saura kwana biyar a daura kasancewar ta bazawara. Ba wanda ya kuma ganin Dada se ranar daurin aure wanda shima ya je ne dan kar ya kunya ta mahaifiyar sa cikin jama'a, haka yabi dangin amarya Rahinatu da ke ta masa barka da zuwa dan cewa Yaaya tayi wai yayi tafiya. A ranar amarya ta tare inda Yaaya ta rike su Haanah wai zasu yi mata sati in da a fakaice ta bawa Dada da amaryar sa damar sakewa ne, dan a ganin ta yaran zasu takura su sedai bata san tayi wa amarya bukulu bane dan kuwa Dada tun da aka kai amaryar be kuma komawa gidan ba se bayan sati shima se da Haanah ta kira shi a waya cewar sun koma gida. ___________ Wata daya kenan da kwana biyu da fara aikin mu yau, shirin da muka yi yau na musamman ne dan tsawon lokacin da muke ma'aikatan yau din ne zamu fara ganawa da shugaban mu gaba daya don haka kowa ka gani cikin shiri yake tun bare da muka sami labarin he's a non nonsense Man, he's very strict and concentrated kan aikin sa. Moroccon gown ce a jikina light purple in color se dark purple veil da nayi using, jaka na da takalmi duk dark purple, a rayuwa ta ina son purple dan lokacin da ina secondary school da miss purple ake nicknaming dina. Gaban mota na hakim ce Salees ya shiga owner's corner ya tuka mu muka bar gidan zuwa ma'aikata, ko ina was very very neat though kullum gurin is neat but na yau is extra + special neat, hatta flowers an yi trimming din su t a good level ta yadda suke bad sha'awa and the silence of the environment is just so wow. Muna fita daga mota muka rabu kowa yayi bangaren sa dan office din Salees na admin block ne ni kuma nawa na bangaren normal offices ne, se da na gama arranging table dina tare da kara extra scents sannan na zauna na fara aiki cikin nutsuwa. Karfe tara daidai aka hau knocking kofa ta, still working na amsa tare da bada izinin shigowa idanu na kafe kan screen din system, sassanyan kamshi me shiga cikin gabban jiki suna kassara su ne ya fara kaiwa hanci na ziyara kafin kuma in ji gaba ki daya iskan da nake shaka ya zama shi, a hankali na dago kai na na sauke kan being din da na tabbatar shi ya kwankwasa kofa ya kuma shigo. Kan kyakkyawar fuskar sa ma'abociyar haiba, tarin kamala da matukar kwarjini na sauke idanuna, fatar sa wata irin kala ce me daukar hankali, ita ba fara ba haka kuma ba za'a ce baka ba, manyan idanu ke gare sa da ya ya rage musu girma ta hanyar lumshe su,  hancin sa dogo ne zit yayinda bakin sa yake nan madaidaici da ya dace da doguwar fuskar sa, a gaggauce na sauke idanu na daga kan fuskar sa saboda kwarjininsa da ya dake ni hakan kuma ya bani damar ganin gangar jikin sa. Dogo ne shi irin na sosai din nan, ba siriri bane dan a murje yake hakan yasa tsayin nasa zanowa me fasali haka kuma abin sha'awa, sedai duk tsawon sa a tsaye yake kyam alamun cikakken namiji haka kuma dukkan wata kirar maza ta bayyana a tattare dashi. Gaba daya wannan kallon a cikin sakanni nayi masa su ina mikewa da sauri dan girmamawa, ban san waye shi ba haka kuma nayi mamakin zuwan sa wajena dan in ma guest ne to bani ya kamata ya gani ba sedai na bar shi as ko an masa kwatance ya kuskure ne hakan yasa na mike dan girmama shi "Pls have a seat Sir". Na Yi amfani da kalman sir ne dan ban san sunan a ba a ganina kuma is not polite to call him Mr. Cikin wnai irin taku ya shiga heading to kujerar da na nuna masa lamarin da ya tilasta min sake kallon fuskar sa sedai wannan karon maimakon cikin idanun sa se na sauke duba na kan kyakkyawan sajen sa da yasha gyara yake kyalli da daukan ido shedar yana samun gyara matuka, wani irin urge nake ji na son kallon kan sa dan ganin gashin kan sa yaya yake sedai na danne da sauri ina ambata auzubillahi minash shaidanir rajim a raina. Wani irin zama yayi na ban mamaki amma se n share nayi kamar ban gani ba na koma na zauna nima kafin in a polite manner na tambaye shi "How may I help you sir". Shiru yayi min har seda na sake maimaita tambaya ta kan cikin wani tone me cike da  kamewa hadi da tsare gida ya yi min wata bahaguwar tambaya "Your name?". Kamar in ki amsa masa se kuma na dan saki murmushi bayan nayi tunanin ko so yake yaji in ni yake nema "Khadeejah Ma'aruf Nasidi". Nan ma se da yayi shiru kafin kuma ya mike ya fita in da ni kuma kamar shashasha nabi bayan shi da kallo baki sake ina tunanin wane irin mutum Allah ya hada ni dashi yau ni kuwa?. Kusan minti uku ina zaune baki sake ina bin kofar da ya fita da kallo kafin na iya rufe baki na na maida hankali na kan system din sedai sa'i da lokaci na kan kalli kofar da tun da ya fita ya rufe min ita take a kulle. Karfe sha daya da rabi muka nufi hall gaba dayan mu inda a nan za'a yi meeting da general head da se yau ya sami zama da mu, baki na dauke da boyayyar sallama na shiga hall din, kujerun wajen adadin ma'aikatan dake ma'aikatar ne excluding irin masu share share da goge goge and the rest, kujera na samu na zauna ina aje yar ipad dina kan table din gabana. Se da aka zzzauna kafin muka ji gyaran murya with a matured tune hakan yasa duk muka sake shiga nutsuwar mu, for the second time wannna sassanyan kamshin ya sake kai wa hanci na ziyara, wannan karon lumshe ido nayi ina shaka dan yadda turaren yayi min dadi na dade ban ji bakon kamshi me dadin sa ba. Tattausan Muryar sa yet cike da bossing ya fara magana cikin welcoming din mu kana ya fara addressing din mu, shiru kowa yayi muna sauraren sa cike da nutsuwa, irin yadda turancin sa ke fita fluently with Fulani ancient dole ya burge kowa, awa daya meeting din ya dauka ya sallame su bayan ya bada damar kowa yayi introducing kan sa hakan kuwa muka yi tare da fadar post din da yake kai. Ko da na koma office na dade ina mamakin me ya kawo general head office dina, hankali na be kwanta ba se da naji ashe ba office dina kadai ba ya shiga office din duk wani sabon zuwa. Ranakun da suka biyo baya aiki muke tukuru dan kuwa boss din mu ba shi da wasa kan aiki, in kuna jin workaholic to shine, ina zaka aiki, daga ina kake aiki, me kake yi aiki, me zaka yi aiki, komai aiki, ni har mamaki nake in yana da lokacin wani abu bayan aiki, Allah ya dasa min shakkar wannan bawa ta yadda har bana san abinda ze hada hanya ta da tashi dan kuwa kwarjinin sa ba karamin duka na yake ba. Yau ma dan ba yadda zan yi na hada files din da dole se na kai masa na fit heading to his office, kamar me tsoron duka haka nake sanda a corridorn har na kau gaban office din inda aka rubuta boldly "IBRAHIM ABDALLAH MAIDOKI". A fili na karantawa sunan na sake maimaita wa kafin na tabe baki kana na maza na gyara sannan na shiga knocking, kasa kasa na ji muryar sa na amsa min da "Yessss". Irin yadda ya fadi yessss din kamar wani wanda yayi aikin karfi ya gaji lilis, not minding hakan na tura kofar na shiga with my little sallama a baki na, ban jira jin ya amsa ko be amsa ba na karasa gaban table din sa na ajiye files din hannu na na koma gefe ina jiran ya gama phone call din da na same shi yana yi dan na masa bayani "Dada is sorryyy, no I'll be coming back today insha Allah". Ya fada can kasa, "I missed you more Haanah, where's my Meerah and pretty?". "Is okay, I'll be back today, I promise". "I love you more dearies, byee". Kaman dole haka na tsaya ina sauraren sa har se d ya gama wayar da yake yi wanda tsabar yadda yake magana yayi baya yi ba se da nayi kusan minti biyar a tsaye ynaa fadar iya wancan sentence din na sama. "Here's the list if files you asked for sir". Gyada min kai kawai yayi lamarin da yasa takaici ya cika min ciki, yanzu duk tsayuwar da nayi dama gyada kai ne kawai amsa ta, lallai mutumin nan karshe ne. Fita nayi ina tafe ina kunkuni abina har na kai office, daga nan kuma wani abu be kuma hada mu ba. __________ Watan mu hudu kenan da kama aiki a garin Bakwarni, matsaloli kamar sun tafi ashe wanda suka fisu na gaba, a zaman da muka yi a nan har na manta da damuwoyi na na saki jiki dan babu Mariya babu Hajiya Iya babu kuma su Amir an hada husuma. Sedai tashi daya wai se ga wani sabon zance, ba'a kawo maganar ba se da muka je Darma yin hutun sallah, cikin farin ciki nake bin ko ina da kallo da tunanin zan je in ga Ummi na in kuma zagaya dangi, aikuwa haka nayi din dan naji dadin sallar ba kadan ba, na gama zagaye na kana muka hau shirin komawa dan hutun mu ya kare se kuma ga wani sabon tsari daga Hajiya Iya. Wai ai ni a nan zan zauna Salees ya tafi da Mariya dan baze yiwu yaje ya tare da ni ba alhalin babu abinda na aje ban da in ci in kasayar so wannan karon ni zan zauna da yara su kuma su tafi, gaba daya am confused jin wata magana kuma, wai shikenan ni mutanen nan ba zasu bar ni in samu kwanciyar hankali ba. Duk yadda naso in fahimtar da matar nan taki dan rantsuwa tayi ba za'a bar Mariya ba a gida, nima kuma a wannan karon nayi rantsuwa ba zan zauna ba dan ba abinda ze sa na zauna nan alhalin aiki na yan can, wannan ma bame yiwuwa bane. Haka dole Salees ya tarkata mu muka tafi mu uku, ni dashi da Mariya se kuma Amir, Sahal da Ilham kuma aka bar su wajen Hajiya Iya saboda karatun su. Base nace muku komai ba kan zaman dan kuwa rayuwa da Mariya kun san se hakuri kawai, ana dai malejin rayuwa kawai, yau dadi gobe akasin haka har muka kuma shafe wasu watanni biyun, anan ne kuma Kaddarar mu ta tsaya. Tun zuwan su Mariya d sati Uku Amir ya fara rashin lafiya sama sama, da farko Mariya bata dauki abin da wani mahimmanci ba ta rin ga bashi magunguna batare da anje asibiti ba, wasa wasa ciwo ya fara karfi a jikin yaro hakan ne yasa ta sanar da baban sa nan suka tafi asibiti, bayan series of test likitoci suka ce basu ga komai ba amma suka ba su magani aka dawo aka cigaba da sha, maimakon sauki ya samu se ciwo ya cigaba da gaba, gashi kuma duk asibitin da suka je se ace ba'a ga komai ba lamarin da ya daga hankalin Mariya da Salees tun bare ganin yadda yaron ya kare ya tsiyaye, hakan yasa suka buga waya gida suka fada aka fara yawon neman na Hausa aka aiko kanwar Mariya ta kawo, ta bangaren Hajiya Iya itama Hannatu ta kawo sedai duk a banza. A lokacin ne suka fara rade radin ai nice na kama yaron tun da ban so dawowar uwar sa nan garin ba dama ni mayya ce, hakan yasa aka koma karbo maganin maita sedai kwana biyu da fara amfani dashi aka tashi ba yaro, YA MUTU!. Anan ne cikakken tashin hankali domin kuwa ba su Hajiya Iya da Hajiya Ramatu ba, wannan karon har da Salees a masu yarda ni na kashe masa da, a farkon maganar ban famuyba sanin shi wanda ya aje ni yasan wace ni sedai awanni kadan kafin Amir ya mutu Salees ya same ni a daki na dawo daga aiki dan duk abinda ake ban fasawa zuwa aiki na ba dan na sawa raina akan su ba zan yi asarar means of earning dina ba, so ranar na dawo na wuce su a falo, Mariya da Hannatu da Safiya suna ta kokarin ganin sun durawa Amir maganin dan baya iya sha da kan sa, daga sallama ban sake ce musu komai ba dan ko nayi magana basa amsa min, ina aje jaka ta kan gado se gashi ya shigo a fusace yana buga min kofa, dan turus nayi ganin yadda ya shigo a fusace yan huci kamar wanda ya hadiyi garwashi so se na dakata daga kokarin cire kayan da nake yi na zuba masa ido dan nasan akwai Magana a bakin sa. "Shin a zuciyar ki babu imanin da zaki ji tausayin wannan dan jaririn da be san komai ba a duniya, me ye hadin sa da fadan ku da mahaifiyar sa balle kice zaki huce a kan sa, shin Khadijah ko dan ni be kamata ki kyale yaron nan ba ya huta, eye". Gaba daya na daburce na kasa accessing inda maganganun sa suka nufa, to cut the drama short se na fada masa kawai "Ban fahimci zancen ka ba, nayi wani abu ne? Wane yaron kuma kake magana ?'. "Dan Allah ki daina wannan pretending din naki alhalin na san kin san kan me nake magana, a rayuwar ki ki rasa wa zaki cutar se jina na saboda duniya babu amana, is okay bari in fito Miki a mutum ki sakar min kurwar yaro da kika kama dan ina bukatar ganin sa a raye, in zaki yi kwadayin ki kar ki kuma sauke idanun ki kan yayana". Yanayin da na shiga alokacin baze bayyanu ba dan kasa magana nayi, baki na da zuciya ta suka yi min nauyi se idanu na da suke zubar hawaye Masu tsananin radadi da azaba. Ko a jikin Salees se ma wani uban tsaki da ya ja yana nuna ni da yatsa "Bar ganin ina cewa ina son ki a kan yayana na sha fada Miki zan iya komai, tun muna mu biyu ki saki yaron nan ya mike, na baki awa biyu zan je na dawo, wallahi in baki sake shi na se kin hadu da mafi munin tozarci dan se na tabbatar na sanar da duniya wace ce ke bakar muguwa, green snake under green grass, kina zaluntar mutane da wannan innocent fuskan da kike displaying alhalin bakar kumurci ce ke, banda kaddara me ze hada rayuwa ta da taki, wallahi i curse the day I met you". Da kyar na iya daga kai na kalli lokaci wanda ya nuna min na ci awa daya da mintuna cikin awanni biyun da Salees ya diba min, hannu na karkarwa na janyo waya ta daga jaka na shiga call logs dina, akan number Ummi na tsaida idanu na kafin na danna mata kira, bata dade tana ringing ba kuwa ta dauka da sallama cikin dattijuwar muryar ta kamar yadda ta saba "Ummi kizo zan mutu, zasu kashe ni Ummi dan Allah kizo, innalillahi wa inna ilaihi rajiun". Abinda na dinga maimaita wa kenan wanda ya tashi hankalin Ummi, ina ji tana kiran suna na amma na kasa amsa wa hakan yasa ta kashe wayar, kifa wa nayi kan bed din Ina sauke wani irin numfashi da duk wanda yaji yasan ba lafiya ba, kwakwalwa ta ta daina tunani ta tushe, kaina yayi wani dummm. Ina nan a haka Salees ya dawo, a lokacin kuwa tuni Amir ya bar duniya domin a yadda naji kururuwar Mariya da yan uwan ta ko awa da fitar Salees ba'a yi ba lokacin, irin yadda take fadar ta shiga uku ta lalace na kashe mata da shine ya shaida min ya rasu, tun lokacin da naji haka na tashi na kulle kofa ta na koma na zauna ina jiran tsammani, ganin hakan ba ze min ba ne yasa na kira Ummi na. Kamar sun manta dani ba wanda ya kuma bi ta kaina aka shiga kokarin mika Amir gidan sa na gaskiya, se bayan an kai shi an dawo sannan Salees yayi lokaci na, irin yadda yake dukan kofar yana kiran suna na tare da zagi da munanan kalamai yasa gidan ya rikice, wanda basu san abinda ke faruwa ba ma aka dinga tsegunta musu, ni kuwa hankalin tashe ta ciki na daga kai na dubi agogo se naga ko awa uku ma ba'a yi ba da kiran Ummi na, alhalin tafiyar awanni goma sha biyu ce daga garin Darma zuwa Bakwarni, so se na saddakar dan nasan kafin su zo maybe sedai gawata dan yadda Salees ke dukan kofar ya na tabbatar min se ya kashe ni abin ba magana, ga can kuma taron mata makwabta da suka shisshigo suma suna fadin a fito da ni se sun yi maganin na. A firgice na mike tsaye lokacin da Salees ya sami nasarar balle kofar dakin, yadda ya koma kamar wani mahaukacin zaki shine y sake rudar dani na fara girgiza masa kai ganin yana nufo ni "Na rantse da girman Allah Salees ni ba mayya bace ban kashe maka da ba, ka kawo Kur'ani ma dafa wallahi bani na kashe shi ba". Ina Salees da alama baya ma fahimtar me nake cewa dan wani irin shaka yayi min kamar me shirin raba ni da duniya, take na fara kakari idanu na na juye na shiga kokarin fisge kai na amma na kasa, a yadda nake shaƙe a hannun sa ya shiga kashe fuska ta da maruka yana zagi ta uwa ta uba, hanci da baki na suka fashe suka dinga jini amma bawan Allahn nan be yi imanin bari na ba, can sama sama nake jin wasu muryoyi na fadin ya sake ni kar ya kashe ni sedai ban tantance na waye ba na sume a hannun sa. _____________ Ko da ta suma be fasa dukan ya ba seda kyar aka samu aka kwace ta a hannun sa ana fadin ya bari kar ya daukar wa kan sa masifa, ruwa me sanyi Hajiya Iya da basu dade da zuwa ba dan ma jirgi suka biyo tasa aka watsawa Khadijah dake kwance helplessly sedai ko motsi bata yi ba, ruwa cikin bokiti ya sa aka watsa min wannan karon amma duk a banza, a nan ne hankalin ta ya tashi dan tunanin shikenan Salees ya kashe ni shima za'a kashe shi dan tafi kowa sanin dangin Khadijah ba zasu zuba ido ba, gashi in maganar kudi ake yi ko alfarma da hanya ne sa ba kusa ba su din ba sa'an danta bane. A daidai lokacin Ummi mahaifiyar khadeejah tare da yayyen ta maza biyu Hashim da Hashir da kuma autan su Hisham suka shigo, gaba daya hankalin Ummi a tashe yake ta yadda bata tsaya kallon kowa ba ta shiga nema na "Khadijah, Khadijah, ina Khadijahn take". Se kuma aka rasa wanda ze bata amsa inda tashin hankalin Hajiya Iya ya ninku haka ma Mariya, ga tashin hankalin rashin da ga kuma wani na miji yayi kisan kai, ja baya Ummi tayi jin kafar ta ta taka mutum ya kai duba se kuwa idanun ta suka sauka kan fuskar mafi soyuwar yar ta Khadijah, fuskar ta kumbura da shatin hannu haka kuma tayi kacal kaca da jini, wani irin juwa ce ta dibi Ummi yasa tayi taga taga zata fadi ya Hashim da shine babba kuma yafi kusa da ita ya maza ya tare ta, kwace wa tayi daga hannun sa ta kai tsugunne ta shiga tattaba fuskar Khadijah kana ta dube su cikin wani yanayi "Hashim, Hashir wannan khadeejah na ce ko, Deeje ce wannan ko?". Se lokacin suka lura dani suka kuma shiga rige rigen durkusawa waje na, cikin wani irin kururuwa Hashir ya mike yana bin jama'ar falon da kallo "Waye yayi mata haka, wane dan iskan me tsautsayin ne yayi laying filthy hands din sa kan kanwata, nace waye shi". Tsit falon aka rasa me magana kafin Salees cikin jin shima wani jan wuya ne ya furta maganganun da suka ja masa shiga wani hali "Ni ne nan na dake wannan asararriyar mayyar me fuska biyu, akwai abinda zaka iya....". Ko kafin ya karasa abinda yayi niyyar fada ya Hashir ya danke shi ya shiga sauke masa naushi a ko ina da hannun sa ya kai, idanun sa ya rufe kawai Khadijah yake gani a halin da take ciki da kuma zancen salees na cewa shi ya mata haka, se da ya Hashim da hisham suka rike shi da kyar dan Salees ya jigata ga kuma jin da mutanen falon ke yi, wani irin fincikewa ya Hashir ke yi yana fadin a bar shi ya koyawa Salees hankali be kuma tsaya ba seda Ummi ta daka masa tsawa "Kazo ka ɗauke ya mu wuce asibiti su duba min in ta rasu ne". Ta fada directing to ya Hashir aikuwa ya taho da sauri tare da ɗaukan ta gaba daya Hisham ya bi bayan shi ita kuma ta dubi ya Hashim "Kayi duk abinda ya dace kan shi dan ba zan bar digon jinin khadeejah ya zuba a kasa ba, ni da ku shege ka fasa wanda yace a zauna lafiya yaci uban shi, auren da ya haɗa ma Allah ya tsine masa albarka". Ta fada tana kallon su Hajiya Iya ya fusace kana ta nufi kofar falon kafin kuma ta tsaya ta juyo "I'm coming back to you, zaku san kun taba jinin Ma'aruf Nasidi". Ta sa kai ta fice, shi kuwa ya Hisham tuni ya kira yan sanda, babu dadewa da fitan Ummi suka karaso aikuwa ya nuna musu Salees "Ku tafi dashi, kowa ye yazo kar ku yadda ku ba da bail din shi se da izinina, for now bani da lokaci amma daga baya zan shigo". Kamewa suka yi tare da sara masa suna fadin "Yes sir". Kana suka tattara Salees da be san inda kan sa yake ba suka watsa a mota suka fice ignoring all the kururuwar da Hajiya Iya da jama'ar ta ke yi. ________________ "Amma dai Aunty kin san bake na dafawa abincin nan ba, kalli yadda Miemie ke jin yunwa kuma kin hana maids su dafa komai yanzu kuma na dafa mata kin dauke, this isn't fair kin sani". Haanah ta fada rai bace sedai tana kallon Rahinatu dake amsa sunan kanwar maman su haka kuma matar baban su a yanzu, tsaki tayi tana cigaba da cin abincin wanda indomie ne da yaji hadi matuka, kifi kaman yayi magana a ciki ga kuma veggies da aka sa wanda ya sa abincin ya zama gwanin sha'awa. "To ki hana ni ci mana karamar mara kunya, yara duk an bata ku da iskanci da sangarta, kamar ku tula tula a gida amma an zube wasu masu aiki, abinci har kusan kala uku ake dafawa dan samun guri, kowace munafuka ta bude ciki tana zurawa ko tausayin me kawo wa bakwa ji". "Amma dai kin san a gidan uban mu muke ko?". Ameerah ta fada cike da tsiwa "Kuma gidan miji na ba dan haka ba za'a sake dafa min abinci biyu ba, daya za'a yi shima wanda na zaba sannan dolen ku ku zaku dinga gyaran gida dan na sallami masu aikin tun da ni ina tausayin sa, itama wannan yar tatsutsuwar duk abinda aka dafa shi zata ci ba zancen wani a dama mata oat ko cerelac or something, and mind you ki koya wa kannen ki da'a kafin in darji bakin daya daga ciki, tarka tasu ku wuce bedroom dan ina bukatar hutawa a falo bana bukatar kowa ya dame ni". Cikin wani yanayi Haanah ke kallon ta idanun ta na cika da hawaye, bata taɓa sanin kanwar uwa kan iya behaving a'a matar uba wa ya'yan yar ta ba shiyasa har ta bada goyon bayan Dadan ta ya auri Aunty Rahinatu, da ta san things can turn out to be like this da ba zata fara ba. Gashi babu yadda zata yi ta fadawa Dada dan yayi tafiya zuwa Moscow and bata san me ya faru ba yau kwana biyu shiru be kira su ba sedai tafi tunanin yayi busy ne, tun bayan dawowar su daga gidan Yaaya after a month da auren Dadan komai ya canja masu na yadda suka saba rayuwa, kome suka yi ba su iya ba a wajen Aunty Rahinatu, komai suka ji laifi ne, kallo ta hana, zaman falo ya hana, kayan snacks da ake musu na zuwa school ta hana ta ce ai ana basu kudin break, tafi tafi tace su daina daukan juice in zasu tafi school, a nan islamiyya tace malam Lawan ya daina kai su ai ba nisa, kai duk wani abu na jin dadi ta hana yanzu kuma gashi har ta zo ka abinci, inaaaa ba zata bari ba dole ta taka mata birki, bari dai Dada ya dawo dole ayi wacce za'a yi. ______________ Rike suke da hannun juna kowacce hawaye a fuskan ta, "Ban sani ba ko akwai rabon mu cigaba da rayuwa Farida, ban sani ba ko kuwa iya wa'adi na Kenny, abinda nake so kawai shine dan Allah in na bata miki ki yafe min, ina matukar kaunar ki Farida dan bani da yar uwar da ta fiki, kin zame min, kawa, aminiya, yar uwa haka kuma mahaifiya a wasu lokutan, kina kan kashe ko nawa ne dan sama min farin ciki, ba zan taba mantawa dake ba Farida, ba zan iya biyan ki abinda kika min ba, Allah y saka miki ya biya ki da mafificin alkhairi". Hajiya Farida bata iya cewa komai ba saboda kukan da yaci karfin ta, a haka aka tura gadon da Falmata take zuwa dakin theatre din idanun ta a rufe cikin tunanin Alh Usman, yadda ta baro garin batare da sun yi sallama ba abin ya tsaya mata a zuci, ya fa san da maganar tafiyar amma ya sa kafa ya bar garin zuwa wai daurin auren dan abokin sa, tayi ta kiran wayar sa kuma baya dagawa dole ta hakura, a haka ta bar kasar baya nan har kuma yau da za'a shiga da ita dakin aiki be kira ba bayan ko a nan tayi kiran wayar sa be dauka ba................ *TOOOOOO ALLAH YA KAWO MU LOKACI YA KAWO MU YAU GASHI MUN KAWO KARSHEN FREE CHAPTERS".* *KAKAKARA KAKA, CAKWAKIYA KAN CAKWAKIYA, SALEES YA YI WA KHADIJA DUKAN MUTUWA AN TAFI DA ITA ASIBITI RAI A HANNUN ALLAH,* *GASHI SHIMA YAYA HASHIR YA FITAR DASHI HAYYACIN SA KUMA YANA HANNUN HUKUMA* *SHIN ME ZE FARU A GABA, KHADIJAH TA MUTU KO KUWA?, SHIN YA ZAMAN SALEES A HANNUN HUKUMA?* *KAI KU TSAYA, YAYA MAKOMAR AUREN SALEES DA KHADIJA?* *SHIN ME YASA SALEES YA AMINTA KHADIJA MAYYA CE BAYAN A DA YA KARYATA HAKAN?* *WAI SHIN WANE FAMILY NE NA MA'ARUF NASIDI DA UMMI TACE ZA'A SAN AN TABO SU?.* *MEYE MATSAYIN YA HASHIM DA YAKE BAWA YAN SANDA UMARNI HAKA?.* *YA YA TARIHIN SOYAYYA DA KUMA FARKON AUREN KHADEEJAH DA SALEES YAKE DAN MUN JI DA FARKO TACE AUREN NASU CIKE YAKE DA SO DA KAUNA?.* *MEYE SILAR TARWATSEWAR WANNAN SO DA KAUNAR IN HAR AKWAI TA.* *GA AUNTY RAHINATU GASU HAANAH GA KUMA DADA, KO WANE MATAKI DADA ZE DAUKA IN YAJI ABIN KE WAKANA A GIDAN SA NA TAKURA YAYAN SA DA RAHINATU KE YI?* *SHIKENAN SHI DADA BAZE YI DACE DA MACE TA GARI BA HAKA ZE RAYU DA YA'YAN CIKIN UKUBAR MATAR UBA KK KUWA RABUWA ZE YI DA ITA SU RAYU HAKA BATARE DA UWA BA?* *SHIN WAI WANE KUSKURE HAJIYA YAAYA TAYI WA RAYUWAR DADA DATA KE NADAMAR SA HAKA?* *HAJIYA FAKMATA ABAR TAUSAYI AN SHIGA DA ITA THEATRE, KO YAYA AIKIN ZAI KASANCE?, SHIN ZA'A YI NASARA KO KUWA?, SHIN ZA'A FITO DA ITA A RAYE KO KUWA WA'ADIN YAYI KAMAR YADDA TA FADA?* *Kai, tambayoyin da yawa da ba zasu lissafu ba haka kuma kowanne yana da amsar shi wadda ba wanda ya sani se ni kadai wato Ouummey, ku dai ku biyo ni domin warware duk wani kulli dake cikin wannan tafiyar, domin cigaba da samun damar karanta littafin RASHIN HAIHUWA KINDLY make your payment via*👇 9013101854, Rabiatu Abdullahi Aminu, opay Or 2391368231 Rabiatu Abdullahi Aminu, zenith bank. HURRY up Dan muyi my fara wannan tafiyar dan endpoint din akwai nisa, se kun zo💃💃💃💃 Ouummey 📚✍️.